Sashe 15
Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ma Allah cewa ya bani kai amatsayin miji na, gashi ya amsa. Ranar da aka kawo mintin bai kon mu da sa rana ban iya bacci ba don murna, gani nake daga bacci ya debe ni zan farka in ga cewa ba gaskiya bane. Zugun abubakar yayi yana kalon kasa, wannan al‘adar tana cikin al‘adun da ya tsana a mata. Ba wai haramun bane mace tace tana son namiji, amma a kalla kijira ya fara furtawa. Shi yasa yake son hafsa, don tana da kamun kai. Shi a nashi ra‘ayin in dai mace zata fito tace tana son namiji ba mijinta ba, ko kuma shine yazo da da‘awar son shi gurinta ta amsa mashi ba. To wannan bata cika mace ba a nashi ra‘ayin.........ta katse shi. Na san waccen yarinyar da kake nema ta kano din tafi ni kyau ne ko? Ya dago kai, please ki muyi maganar da ta shafeni da ke, bana so kina saka hafsat. Tayi dan diM, can tace shi kenan. Yanzu wane shiri zamuyi? Ya kamata bukinmu yazo da sababin salo na burgewa acikin zuri‘ar mu. Yace, ko? Tace, sosai kuwa. Yace, to ki rubuta duk abinda kikeson ayi, in yaso in nazo zan gani. Ya mike zan tafi gida, ga yar tsaraba nan. Ya nuna mata lader. Cikin doki tace, amma na gode. To yanzu har zaka tafi bamuyi wata fira ba sosai. Wani lokacin in nazo zan dade. Ta rako shi har bakin gate in da hashim yake tsaye da jamilu yayan fadi. Suka gaisa da jamilu, inda ya shiga jin jina masa da cewa ya gode da wanan jahadin da yayi a gurin lamido, inda ya samo musu yanci. Abubakar yace au! Kai ma kayi farin ciki ne? Jamilu yace, ba dole ba, don yarinyar da nagani zuciyata ta so ba yar zuri‘ar mu bace. Son yarinyar ya shige ni a kudu muka hadu da ita lokacin da muka je (N Y S C) Allah ya shi maka albarka bayan bukinka zanyi maganar tawa. Abubakar yace Allah ya taimaka, mu kam bari mu tafi. sati 2 tsakani da zuwan shi kano, lamido ya kirashi to kasan lokaci yana gabatowa, don ha sai kafadi inda iyayen yarinyar nan suke saboda aje a kammala da su suma. Zufa ce ta soma tsatsafo ma Abubakar, amma sai yace, am.....dama mahaifinta yayi tafiya ne shi yasa. Amma idan ya dawo sai in fada muku saboda ya riga ma ya san da maganar, kuma su a shirye suke. Lamodo yace, to cike da damuwa ya fito, dole ne ya koma kano gobe sai sai ya takurawa hafsa don yasan abinda take ikirari zai hana auren su. Ya kira phone din hashim yace, ka shirya gobe juma‘a zamu shiga kano, sai mujuyo ranar sunday. Hashim yace, to ******* Nikam tun ranar da abubakar ya tafi na shiga halin kunci da damuwa. Na rasa dan ragowar farin cikin da ke tare dani. Ina zuwa makaranta da gurin aiki, amma bana iya cin wani abu. Ban amince ina son abubakar ba sai yanzu. Har shadad yafini hakurin rashinsa, duk da cewa sun shaku matuka. In nayi kamar in kira lanbobin da ya bani sai in fasa. Nace, kai gara in koyi yanda zanyiwa kaina fada, in hori zuciyata ta saba da rashin sa kada in zurma da yawa in kamu da ciwon zuciya a banza. Don nasan babu mai hankali da zaya aureni. Kai akwai daran da na rabashi ina kuka. Ba zance irin kukan da na saba bane, wannan kukan son abubakar ne. Yau satin mu 2 rabon mu dashi. Ina zuwa ne cikin aji, duk da hankalina yana gurin malamin amma har yayi ya gama ba zance ga kalma 1 da yake fadi ba. Tunanin Abubakar sadeek kawai nake yi. Na san abaya na so munnir amma ban shiga irin wannan ma tsanancin halin ba. Wani irin abubuwa nake ji game dashi, waddanda ba zan iya fasrasu ba. Kenan da ba son mannir nayi ba. Kenan da shirme nakeyi. Ya rintace tasa nake ganin kamar son shi nake. Karshe ya cuceni, shima dama ba sona yake yi ba sha‘awa ce. Gashi dalilin abin da yayi min yasa na rasa abubakar sadeeek. har aka watse cikin aji ban sani ba. Da yake ni ba kawa ko aboki gareni a makaranta ba, babu wanda ya kulani. Kasancewar ko yaushe cikin daure fuska nake, masu son kulani ma tuni sun watsar dani, saboda rashin fuska. Ringing din wayata ne ya dawo dani daga tunanin da nayi zurfi acikin sa. Jikina lakwas na dauka. Nasan rahama ce, tunjiya take min nacin inje tana nemana, ba tare da na duba fuskar wayar ba na kaita kunnena. Muryar da tayi min sallama ce tasa naji na watsake. Bansan na mike tsaye ba, ina cewa. Wa‘alaikumus-salam. Yace, ina kike ne? Sai na samu kaina da wani jan aji, ina tambayar wanene? Da sauri yace, kina nufin baki ganeni ba ko? Nace, eh. Yace, good! Ki fada min inda kike sai inzo in sameki. Nace, ban gane kowanene ba ya za‘yi in fadi inda nake? Sai kurum ya kashe wayar shi. Take naji haushin kaina, mutumin da nake son gani ruwa a jallo amma yanzu na tsaya salo. Da sauri na fita na nufi gida, ko in biya in dauki shadad wai ina zaton yana kofar gidanmu. Ganin bashi na juya da sanyin jiki na nufi makarantar su shadad na daukoshi muka nufo gida. Hashim ya kali sagir yace, kaima kazo muje mu 3 don mu sami galabarta. Sagir yace, nifa shaknar hafsat nake ji, gashi tana bani girma kada taga zamu matsa mata. Rahama tace, ka daure kuje, kila ganin idonka ta sausauta. Abubakar yace, nifa hafsat nasani tana sona. Dalilin da take fadin cewa ba zai bari muyi aure ba shine nake son ji. Sagir yace, to ku tashi muje. Suka mike yana mitan cewa dan miskilanci irin na hafsa waima nine bata gane ba yau. Hashim yace, kai dai wannan abu yayi maka ciwo. Kasani ko kila bata gane kadin bane? Sagir yace, wannan yanuna kai kadai kake sonta, ita bata sonka kamar yanda kake zato. Abubakar yace tabbas tana sona, amma ku muje dai. Misalin karfe 8 na dare, Shadad ya yi barci, muna kan tabarma a tsakar gida, ni kuwa lokacin zuciyata ta kekashen idanuna sun bushe ina ta tunanin ina cewa, "Ya Allah, dama haka so yake?" Na tashi zaune, na mike tsaye, na jingina da bango duk banji dadi ba dai, zuciyata tana tuhumata da cewa nice na bar dama ta, me yasa na nuna ban gane shi ba? Sai kuma wata zuciyar tace ki daina saka kanki cikin matsala, ba zai aureki ba, keda kika yi cikin shege?!!! Na koma na kwanta, hawaye na sintiri a idona daga gefen idona zuwa kumatuna, so matsala ne, dama ban san Abubakar ba, dama ban zo Kano ba, dama ban je bikin Rahma ba. Bugun kofar ne ya sani na dawo cikin hayyacina, da sauri na mike cike da fatan shine, ba tare da na saka takalmi ba na nufi kofa, ban bukaci na san waye ba na bude kofa. Ganin shi tsaye ya sa na sauke wata nannauyar akiyar zuciya, sai kuma Miskilanci ya motsa na ce, "Daga ina? Ka canja ne ba kace ba zaka kara zuwa ba?" "Au korata kike? To shike nan bari na koma." Da sauri na ce, "Ni bance ba, ai ance bakonka Annabinka, ka iya shigowa." Ya ce, "Zaki ji da gulmarki. Hashim ku shigo." Na shimfida musu tabarma suka zauna, shi kuma ya zauna kan tabarma ta kusa da Shadad yana shafa masa kai, na kawo musu ruwa cikin jug, na nemi kujera 'yar tsuguno na zauna. Na gaishe su suka amsa, sai dai shi daya kafe ni da ido yana kallona, duk da ba wuta sai hasken farin wata, ya ce, "Ni ba zaki gaidani ba?" Na kalleshi irin hararar masoya, na maida kaina kasa. Ya ce, "Shine na kiraki dazu wai kike cewa baki gane ni ba." Shiru nai ban tanka ba Ya ce, "Ka gani ko Hashim ta gane ni." Sagir yayi dariya, "Kila bata gane ka din ba." Abubakar ya ce, "Bani aron hankalinki nan. Shi yasa na kwaso abokaina dan su zama shaida, da farko ina sonki, kuma ki ban amsa. Ta dago ta ce Abubakar bana sonka, ba aibu bane dan kince baki sona, in yaso sai sonki ya zama ajalina, amma daga yau idan har kinki amince min ba zaki kara ganina ba koda cikin mafarkine. Gabana ke faduwa, na ce, "To ai ban ce bana sonka ba." Hashim ya ce, "Pls Hafsa, magana daya zamu yi tunda kina da hankali tin taba aure bai kamata mu tsaya muna wasa da hankulan juna ba." Abubakar ya ce, "Magana daya ce Malama, kina sona?" Kalma daya ce da Hashim ya fada ta dagan hankali, wai na taba aure? Inama na taba auren ai da bazan damu ba, sam banji maganar da Abubakar yake min ba, su duk sun dauka aure nayi na haihu, to tun kan na samu matsala gwara na rabu da shi, sai dai sonsa ya zama ajalina, na ma rabu da iyayena ballantana shi? Tsawar da ya dakamin ita ta dawo dani daga tunanin da nake ya ce, "Kin maidani dan iska ne ina magana kin min shiru?" Hashim ya ce, "Ki yi magana mana Hafsa." Muryata ta soma rawa irinta masu kuka, "Lallai ina son ka har ba zan iya kwatanta son da nake maka ba. .....