Sashe 1
Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanadin Boko 2-1 Posted by ANaM Dorayi on 05:26 PM, 18-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Duk gidan da na shiga kalmar iri daya ce,wato baya shigowa. da hanxari na nufi gidan su maman rahma,ita bata nan ma sai matar wansu tace min shadad bai xo ba, na dawogida na sake duba ko'ina, rijiya a datse da kwado, don haka ban kawo xaton ya fada ba. na dubi takalman shi da takardun makarantarshi da yake hm work, sai naji kuka ya kufce min. nayi-nayi,sannan na mike na sake fitowa, wata daga cikin makotana ta same ni tsaye kofar gida ina ta leke-leke,tace "kin ko gan shi? nace,"a'a." cikin muryar kuka tace "ikon Allah, to ke ina ki ka tafi ki ka bar shi? nace,bakin kasuwa naje, kuma nakan bar fa. tace da kin sani nan gidanmu ki ke turo shi in xa ki fita.kila fakonki aka yi kina fita aka xo aka dauke shi, na tsura mata ido. su wanene xa su dauke shi? tace, oho.mugu yana nuna kanshi? aka dauki babba ma bare yaro, ke dai wannan rayuwa tamu ba sai dai addu'a ba. nace,to su wanene xa su fake ni?ban jira amsa ba na juya cikin gidan,tamkar mai shirin daukan wani mataki.tace,kije ofishi 'yan sanda ki kai rahoto,ban juyo ba kuma ban tanka ba, a tsakar daki na zauna gwaraf,idanuna suna ta kai kawo guraran yin 'yan tsalle-tsallen shi, naji na fashe da kuka. hakika wadanda suka daukar min yaron nan ba su min adalci ba, don bani da wanda ya fishi duk fadin kano, naci kukana ma ishi, bani da mai bani hakuri, na share hawaye. abu tamkar wasa, sai gashi har anyi kiran sallar azahar,jikina a mace nayi sallah,ina zaune ina addu'a hawaye na bin kumatuna, sai naji sallamar maman su rahma,na amsa ba tare da na share hawayan ba. ta shigo tana cewa, hafsa kin ko ga maigidan nawa? sabon kuka ya kufce min, cikin muryar mai kuka nace wallahi har yanxun mama, tace na dawo kawai sai suke fada min wai kun xo neman shadad,hankakinki tashe. na ko ro mata wajibin duk abubuwan da suka faru, zama tayi rike da baki tana salati, tace lai finki ne in gidan mu yayi nisa ki rike hannun abunki kije dashi mana, angaya maki yanzu kaza batafi dan adam ba ne? Wlh sai kaza ko rago yayi yawanshi han kali kwace amma bil adam yana tafe ana cinikinsa, na sake fashewa da kuka, nace mama tunfa bai kai haka ba ina barinshi a gida, tace to yanxu me zaki fadawa dangin uban shi da iyayenki? Na mai maita kalmar dangin ibanshi? A cikin raina. Sallamar shi ne cikin murna ta ka tseni, anty na yau mun sha yawo da uncle dina, ya fado jikina, munje gurin wasa na hau doki da duniyar sama, mun sha ice cream, harma muka dau hoto. Ban bari ya sake cewa wani abuba na dagoshi na watsa mai wani irin mahaukacin mari, ya yanke da wani ihu sai ganin uncle din nashi mukayi a sukwane ya fado cikin gidan. Na han kadar dashi ya fadi na bishi da duka maman rahama tana a a-a a, ban tsaya ba ina dukanshi ina kuka. Shi kuwa uncle din nashi yana tsaye. Mama cikin jin haushi ta wanka min mari, tace ke ma haukaciyar ina ce? Za ki rufe dan wanan yaro da duka? Na dubeta ina kuka, mama wanan yaron yana jefani cikin damuwa, uban wanene yace yafita ba nanan saboda ya raina ni? Uncle din shi ya sa hannu ya dauke shi, yasa a kafada yana lalashi, shi kuwa sai tsala kuka yake. Cikin daurewar fuska yace, nasan haka zata faru, shi yasa ma na daukeshi ki san cewa kina kasada, ina sone kiji halin da zaki shiga in wani yai gaba dashi saka makon kasadar ki. Ya dubi maman rahama yace, mama don Allah ba kasada bane tatafi ta bar yaro shi daya, mai zai sa ba zata tafi dashi ba? Mamar rahama tace sakarya, nima yanzu na gama yimata fada, gwara da ka gwada mata hakan. Ni ko cikin takaici da masifa nace, ina ruwanka da shi? Menene hadinku da zaka zo ka dauke shi, shi shigi da kalata. Bai tankani ba, kilama bai fahimci hausar tawa ba. Mama tace jacan sakara, na shige daki bansani ba haushin daukar yaron nake ji ko farin cikin dawowarshi? Mama ina ji tana cewa kayi shuru. Kyale ta, kai kuma dana ka kyauta da kayi mata wanan ba razanar. Shi kuwa cikin hausarsu ta filani yola yake cewa, amma mama nikam banji dadin dukan nan da tayi mashi ba fa, da ma ni ta buga zanfi jin dadin hakan don nine na buga ya bude na tafi dashi. Na motsa ranta ne dan ta gane hakan na iya faruwa, in nace zan fada mata da baki bazata saurareni ba. Mama tace haka ne, ai hafsat shu‘uma ce, bayan yayi shuru, da kyar ya mikawa mama shi. Gashi mama, don Allah ki bata hakuri, na san cewa na taba ranta, amma fa kada ta sake dukan shi. Mama tace kada ka damu, gulmace ta sata dukanshi bakaga yanda ta haukace tana neman shi tana kuka ba. Yace Allah sarki! Ban san ko nawa ya ciro ba, naji dai yace mama ga wanan ki sai goro, sanan na jiyo murmushi yana cewa hafsat sai anjuma ko? Ban tamka ba mama ta shugo tana cewa, kinga harda kudi ya bani don Allah kiyi mashi godiya. Ta kwonto shadad a jikina, na turo baki nifa ban sanshi ba daga bikin rahama ya liki men. Wlh na rasa yanda zan yakice shi. Ta ce keko yarnan sai kace wace mujinta ya mutu da kurwarki? Nifa na tambayi rahama da lilin kin jama‘ar ki ta ke shai da mun tun rasuwar baban wanan yaro ne gashi kunyi zaman mutunci, to banda abinki hafsa itafa rayuwar duniya haka take kuma Allah ya fimu sanin abinda ya dace gare mu, don haka ki kula. Tan tahakiliki kila ya maye maki gurbin miji naki. Nace to na fada ne ba dan na amince ba sai don kada mama taga naki zancenta sanan ina son abar maganar cikin tarkace kayan zakin da ya sayowa shadad ne na ga hoton da suka dauka kala 3 sunyi kyau har wata zuciyar tace na yaga su sai kuma wata ta gargadeni da cewa mutumin nan bai cancaci haka a bayan idon sa ba. In kinyi masa a gaban idonsa yanzu sai ki mutunta hotonsa ko dan danki don haka sai na hakura na ajiye masa. Anfi saty banji duriyar shi ba hakan yayi min dadi shadad ne kanyi min zancen sa in na bala mashi harara sai yayi shuru don tun da na dakeshi yake dari dari da zancen uncle din sa. Nan na fahimci wani abu ga yaro shi yaro dan ja a jiki ne zagi duka baya gyara yaro janshi a jiki nuna mashi soyaya cusa mashi tsoron Allah yi mashi nasiha tare da bashi lbr magabata. Suna tai makawa gurin tarbiyya bana dukan shadad na fi yi masa duk abubuwan da na lisafa amma yau daya da na dukeshi duk ya shiga tai tayin sa. Kenan in baka yawan dukan yaro yafi tsoron dukan sannan ya fi jin magana. Wanan tunanin da nayi shiyaja na sake janshi a jiki, da dadare ya gama cin abinci yayi home work, nace ya bani lbr duk abinda ya faru a makarantar su. Nan zan tajin wane ya iya karatu wane ko an tada ya kasa, mun yi masa shem, nace kai fa ka kasa ko? Yace, ina yi anty, har antyn mu tace wai nine nafi kowa zan sake cin na 1 yanzu, nace to ka kara kokari har a islamiyya ka dage, yace uncle yace in na sake cin na 1 zai mun kyauta da ya so ko, uncle din shi sai na watsar da zancen. Nayi shuru ina tunanin yanda zanyi ga adashan da na kwasa gidan su maman rahama dubu 20 a hannuna kudin da naci burin inyi rigista da su, kuma ga kudin makarantar shadad, in ban da da ba cikin satyn nan zasu koro shi, kuma ni an kusa rufe rijista wata zuciya tace, tunda baki taba lattin biya ba kije ki nemi alfarmar suyi maki uziri, nan gaba sai ki basu. Don haka washegari naje naje nayi rigista ta, har kwana 4 ba sukori shadad ba, muna home work na ce wanan karon makarantar ku sunyi dagi amma gobe zanje in basu hakuri kada su koreka. Yayi caraf yace, anty an bani rasit wai na biya, ya tashi da gudu ya nufi ja karshi yana cewa, anty yau anyi kora ma, cikin mamaki na amshi rasit din ina dubawa, na shekara daya aka biya nace shadad wa ya biya maka kudin makaranta? Ya juya hannu tare da cewa ban sani ba. Da mamaki na kwana, da safe kuwa makarantarsu muka nufa kai tsaye bayan ya shiga aji ofishin mai karbar kudin makarantar, muka gaisa ta ganeni, nace shadad yazo da rasit wai an biya mashi kudin makaranta, wanda nasan ban kawo ba tace uncle dinshi bai fada maki zai biya ba? Na kasa magana, tace to shine ya zo ya biya na shekara 1. Sai sabuwar shekara zaki soma biya kudi. Da kyar na ce to shi kenan, na fita na nufi makaranta rai na a bace. Shi wanan habubakar din ba za ya fita hanyata ba kenan? Shi ma yana son dole sai ya cika burinsa a kai na. Tabdijan! Duk ranar da yasake gigin hada ido danine zan rufe idona ne in zage shi tas, yanda zai bar rayuwata ta huta. Abubakar lamido kyakyawan saurayi bafulatanin jahar adamawa dan yola, tuki yake cikin na tsuwa har ya isa gidansu tamgameme da ke bayan PZ, ya ajiye motar a mazaunin ta, sannan ya fito cikin takun na tsuwa ya nufi cikin gidan. Yan mata ne 2 a wadatacen palon duk kansu 1, sai dai in ka kali fuskarsu zaka gane daya tayi tsawon kafa ne, ta taras da yar uwarta. Suka amsa sallamarsa, karamar ta taso da sauri tana cewa (cikin harshen fillanci) sannu da dawowa hamma. Ya rumgumota gefen shi cikin harshen turanci ya ce mata. Yaya makaranta? Ta amsa da