← Book details Sai Na Auri Marubuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 18

Sashe 5

Sai Na Auri Marubuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maryam ta kalleta cike da Mamaki, "Habibbty ke da bakya kallo me za ki yi da film kuma?"

Harararta Nafeesa ta yi, "To na fara kallon daga yau,ni muje shagon cen mu siya."

Binta kawai Maryam ta yi domin bata da tacewa.

Da sallamarsu suka shiga shagon cikin fara'a kuwa mai shagon ya amsa.

Nafeesa ta ce, "Films muke so Amman Wanda marubuci Nafseen ya rubuta."

Murmushi mai shagon ya yi, "Ah madam an gama daman ko duk wa'inda ya rubutane Sabin fitowa Dan dazu da safe ma na karbo biyun nan,SIRRIN DA KE RAINA, NIDA KE MUN DACE, Da sauri Nafeesa ta karba tana mai yi masa godiya tare da mika masa kudin.

Suna komawa Mota Maryam ta ce, " Yawwa Habibbty kin ce min kin zama marubuciya tayaya?"

Dariya Nafeesa tai, "Ta inda kowa ke zama mana duk abin da zai hadani da Nafseen dina kusa gareni koma miye zan Iya ina tabbatar miki da hakan,na fara rubutu na zama marubuciya domin kasancewata da shi kawai."

Maryam ta gyara zama , "Kice min kun hadu ma."

"Umm haba dai ba ajima da sani ba,kuma kaf na duba cikin group din ba mai irin sunansa Abu daya na rike akullum jikina na bani cewa yana group din,ko da wannan aka barni ina jin dadi araina."

Murmushi kawai Maryam ta yi domin bata da tacewa, sai da su kai Nafeesa har gida sannan suka koma na su gidan.

***Tun da Nafeesa ta koma bayan ta yi sallah kallo kawai ta Sa tanayi.

Mammah ta ce, "ai da karatun littafancen gwanda miki kallonma wallahi."

Nafeesa ba ta ce komai ba sai murmushi.

Sai da Nafeesa ta gama kalle films din tsaf wajen 10 kan ta tafi daki ta kwanta, sha biyun Dare dai,dai ta fara mafarkin Nafseen na Online kamar da wasa ta farka,ji ta yi barcin ya bace a idonta gabadaya,wayarta ta dauko ta kunna,abun mamaki tare suka hau online awannan lokacin.

Sallama ya yi agroup din marubuta kasancewar komin dare ba a rasa yan surutu aciki.

Nafeesa.......

Urs Xayyeesherth
https://www.facebook.com/106494781436168/

_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_

PAGE 12

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

☹️KO KU TUNAMIN JIYA NAYI MISTAKE NAKARASA 11 MAIMAKON 12 DAN KUNGA GUNTUNE🤣TO SHI KE NAN ABARSA A KARASHEN 11 DIN KAWAI YAU GA 12

😂😂ANATA MAGANA KAN SIRRIN DA NAFEESA ZATA FADAWA MARYAM KAR KUJI KOMAI SIRRIN NA NAN TAFE🥰🥰

Wayarta ta mutu,wani irin tsaki tayi domin batama lura da cewa chajin wayar ya kusa karewa ba sai ganin mutuwarta da ta yi adai,dai lokacin da tafi bukatar wayar Amman ba dama,ba ta San lokacin da kwalla ya fara zubo mata ba gashi ba nefa alokacin ji take tamkar An rabata da muradin rantane baki daya,kuka tayi mai isanta har barci ya dauketa batare da ta sani ba.

Da Asuba kuwa Mammah na tashinta kan ta yo alwala sai da saka wayarta chaji, tsabar wayar ta kona mata rai bata kara bi ta kanta ba sai da ta gama shirin tafiya skul,ko kunnata ba tai ba, tasa acikin Jakarta kawai.

Tare da suka fito da Mammah ,Ita tai Skul Mammah kuma asibiti shi ko Sabeer tun karfe bakwai ya tafi skul.

Nafe daya suka shiga sai da aka sauke Nafeesa Kan Mammah ta huce asibiti.

Nafeesa na Sauri zata shige Skul kicibis tai da taron mazaje sun mamaye kofar gate din makaranta, Mutansir ne da abokansa.

Zagayeta sukayi suna wata irin dariya ta k'eta.

"Ke Kin Isa ko? Kin yi shaharar Da har ni zaki Mara cikin mutane? Ni zaki tozarta yar matsiyata,makauniya,ke wai atunaninki Dan me nake sonki ne ma? Kin taba tambayar kan ki hakan? A kyau dai inajin Fatima ta dama ki,bare kuma azo maganar arziki yau dinnan zaki San ni kika Mara kan wani marubuci Mara aikinyi Da bai San kina yi ba, yau zan nuna miki ni wanene agarinnan, zan yi abun da ba Wanda ya isa ya fito nema miki hakki ko ahukuntani, kinfi kowa Sanin waye mahaifina bare kuma azo maganar waye ni karan kai na ." Cewar Mutansir yana zagaye Nafeesa, maganar yake cikin izza yana mai nuna mata hannu

Kuka Nafeesa ta fara, "Dan Allah kayi hakuri kar Ku chutar dani, natuba Dan Allah kuyi hakuri ba zan kara ba,komai kace inyi zan yi Amman karka batamin rayuwata,ni Yarinyace ka jikaina da na iyayena karka cutar dani Dan Allah." Ta durkusa kasa tana mai bashi hakuri.

Daga Mutansir har Abokanansa wata irin dariyar mugunta suka fara awajen.

"Alokacin da ki ka mareni,kika ci min mutunci,kika tozartani kin tuna cewa ke yarinyace? Ai da Yarintartaki ki kai amfani ko? To ba shakka nima ayau da Yarintartaki zan yi amfani ta yadda ba wani namiji da zai so ki bare ya aureki, ko shi Wanda kike haukar akasan ina da tabbacin bare so ki ba,kin ga anyi biyu babu ko? Adalci daya zan miki, ki zaba tsakanin acide afuska da kuma umm ba sai na Fada ba ai kin gane, duk dai fuskar taki ma ba wani kyau gareta ba." Cewar Mutansir.

Daya daga cikin Abokan nasa ne yayi magana, "Oga ya za ka mana hakane? Karka manta fa ita ba zabi tabaka ba ga mari ga fitsari in kai bazaka Iya ba ka bamu dama kawai mu far mata in an gama sai mu koma ga acide din kaga ba hanyar moruwa to kowanni bangare ke nan."

Muntasir ya yi wata irin hamshakiyar muguwar dariya, "Mole walle ina kaunarka kwakwalwarka na matukar ja, tun kan ya Sa ido su bayyana Ku kai min ita hostel."

Kara durkusa gabansa Nafeesa ta yi, "Dan Allah kayi hakuri karku batamin rayuwata Dan Allah, nace Dan Allah." Maganar take cikin kuka har ta shide ta kasa fadin komai ma.

Daukanta sukai cikin hanzari tana ihu Amman ko kadan ba mai jinta domin sun toshe mata bakin, hostel din maza suka nufa dakin d Mutansir yake, ga dakin duhu baka ganin komai jefa Nafeesa sukai kan katifar tare da fita, Mutansir ya shigo yana wani banbankarewa.

Kayan jikinta ya fara kokarin rabata da su,tun tana motsi har ta yi shiru illa ajiyar zuciyar da take.....

Urs Xayyeesherth
https://www.facebook.com/106494781436168/

_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don cigaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_

PAGE 11

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

🤣🤣DAN ALLAH KAR KUYI KORAFIN GAJERANCIN FEJIN NAN

Ce ta amsa tare da fadin, "Wa'alaika salam."

Batare da ta lura da sunan ba.

Jameel (Nafseen) ya yo reply da , "Ah ya naga kamar bakuwa muka yi agidanne."

Nafeesa ta tura da alamar dariya, "Tab ai ko ni ba bakuwa bace nafi wata agidannan fa, ko kai na rigaka."

Kamar yadda tai dariya Shima hakan ya yi, "Kin San Bamai? To indai kin San Bamai shi kan shi na rigasa zuwa gidannan."

Xayyeesherth ce ta katse masu magana da, "Ah Ah Yaya Jamilu adai rage mana."

Maganar Xayyeesherth ne ya baiwa Nafeesa damar kallon sunan da kyau kamar yadda take tsammani Jameel Nafseen ta ga an rubuta,batare da ta Ankara ba wani irin farincikine ya mamaye zuciyarta, ihu ta fara tana tsalle da rawa ta ma rasa me za ta yi illa rungumar wayar da tai tana rawa da tsallenta.

Xayyeesher ya maidawo da Reply, "Ke Xayyishatu ina wasa da ke ne? Dare ya yi maza jekiyi barci manya na magana kina sako baki."

Dariya Xayyeesher ta yi, "Aradu ban kwanciya yau kam sai naga ka sauka tukunna nima."

"Iyee,ina fadi kina fadi to kinyi abakin chocolate din ki." Cewar Nafseen.

Alamar kuka ta tura, "Haba Yaya Jamilun ba ma haka,gudnyt walle na tahi sai da sahe."

Ya ce, "Yawwa Yar Albarka,Allah tashemu Lafiya."

"Byebye adai kula ban da...... Bata karasa ba ta Sa emojin gudu.

Dariya ya yi, " Allah ya shirya mana kai in ki ka Shiga hanuna zan baki mamaki."

Nan take Xayyeesher ta sauka tana Dariya, Nafeesa kuwa tunda taga sunansa ta ma kasa maido masa da reply kallon sunan take karayi da Mamaki shin daman da gaske zata yi Magana da Nafseen aduniyarnan har suyi wasa da dariya? Ga yadda tai tunani Sam ba haka yake ba, tunaninta zai kasance mai girmankai da jijji da kai amman ko Kadan hakan bai samu ba.

Mentioning Sunanta Yayi ganin cewa ta bace cikin gidan, "@Nafeesa ko dai kin bi sahun Yarinyarcen ne kinyi barcin?"

Wani irin bugu taji zuciyarta na yi ganin yadda ya ambaceta cikin bazata,tana kokarin yi masa reply kenan...

A yi hakuri👏bana da chajine Amman in sha Allah gobe zan yi typing awadace,Ku taba wannan Ku lashe😘😘Ina yinku masoyana son so fisabillillah🥰

Urs Xayyeesherth
https://www.facebook.com/106494781436168/

_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_

PAGE 13

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

🤦‍♀️🤦‍♀️ALLAH SARKI MASOYAN ASALI ATA HAKURI DANI RASHIN TYPING KAN LOKACI KUN SAN DALILI KE JAWO HAKAN😁NASAN ZAKU MIN UZURI KUMA HAKAN BA ZAI HANA NI GANIN RUWAN COMMENTS BA🥰

GAREKU MASOYAN NAFEESA FATAN BURINKI YA CIKA😁

A dai,dai lokacin da yake shirin yi mata mai gabadaya Nafeesa tai wata irin kara mai kama da na damusa,damkosa tai kawai ta fara jibga ba ji ba gani,jin ihunsa ya Sa sauran mazan da ke waje shigowa ko ajikinta kamar batai komai ba, dukansu ta farayi bilhakki da gaskiya,gabadaya sunyi Jina,jina ba kwari bare karfi,kan kace me har sun fara Jan jiki suna tserewa ahankali,gabadaya sun tsorata "anya kuwa Nafeesa ba namiji ba ce,in ko macece to ba tantama aljanace."abun da wani cikinsu ke ta fada kenan shi ko Mutansir da yafi kowa jibguwa nan take ya sume awajen.
Chapter 5 · 0% Book details