← Book details Sai Na Auri Marubuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 18

Sashe 18

Sai Na Auri Marubuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Kabeer ne ya masu tsawa tare da fadin, "Shi wa?"

"Shi,shi din." cewar su

Tsawa tare da ruwan addu'ar ya kara yarfa masu, "Na ce ku fadsmin shi wa?" ya karasa maganar yana feshe masu turaren hannunsa

"Shi MUTANSIR din."

Kabeer ya ce, "Waye kuma MUTANSIR?

nunu Maryam suke suna, "ita ta san shi kuma tasan komai."

Nan da nan jikin Maryam ya fara rawa ta kasa magana sai Mammah ce ta ma Kabeer bayani atakaice tun da itama ba ta gama sanin komai ba.

Dawowa yayi ga shedanun ya na , "Waya turo ku? ku fada mun ko kuma in cigaba da azabtar da turaren nan."

Kukan Wahala suke suna fadin, "Amina,Amina budurwar Mutansir ta turomu mu kasheta,mun zo tana barci ba dama muyi abun da mukaso aikatawa masu tsaronta sun fi karfinmu hakan yasa mukai nisa da barcin nata ya zarce wanda ta saba, sun hanamu mata komai mu kuma bazamu barta ba har sai ta rabu da Mutansir."

Kabeer ya yi ajiyar zuciya, "Wai shin ku wasu irin Shedanune? me ta tare maku? na ga shi Mutansir din ke son ta ba ita ke son shi ba,ina mai tabbatar maku da cewa ku fita ku bar ta ko in cigaba da azbtar da ku."

Haka dai Kabeer yata fama da azzalumai da kyar suka tafi,suna tafiya kuwa Nafeesa ta samu barci.

Cikin damuwa Mammah ke fadin, "Fatan dai ba komawa tai ba?"

Kabeer ya ce, "Aa ba matsala wannan normal barcine nan da anjima ko cikin dare zata farka."

Mammah,Sabeer da Maryam suke hamdala

Godiya sosai Mammah tayi Kabeer tare da sa albarka,Maryam kuwa sai da ta rakashi har wajen motarshi.

Godiyar ita ma ta fara mai,cikin fara'a yake fadin, "Ki dai na godiyarnnan ban so,an kusa kiran Sallah ki koma gida,sannan in da hali kima NAFEESA alwala kan ta farka,In sha Allah gobe na tashi daga aiki zan zo mu karasa yadda za a abullowa lamarin."

nan sukayi sallama.

***********Misalin karfe shabiyu na dare Nafeesa ta fara kiran sunan Nafseen," Uncle Dan Allah karka mutu, in ka mutu nima ba zan..........

*HAR YANZU DAI MUNA CIKIN GASAR NAN😉LAMARIN NA MUSSAMANNE AKWAI WANI ABU DA BAN BAYYANAR DA SHI BA CIKIN FEJINNEN KO WACECE ZATA IYA FADAMUN? NAFEESA TA FARFADO LOKACIN DA TAJI KAMSHIN TURAREN SAHIBINTA,KAN DAGA BISANI SHEDANU SUKA BIYO BAYA🤔KU TUNA LOKACIN DA NAFEESA TAI WANNAN BARCIN MEYA FARU ALOKACIN? SANNAN BAYAN WANNAN ABUN YA FARU ME YA KARA FARUWA DA YASA BARCINTA NISA😉A BAYYANE ABUN YAKE AMMAN BA KOWA ZAI FAHIMTA BA😉FATAN ALKAIRI MASOYANA🥰*

DOMIN TURO SHARHI KO AMSA

08103080717

Urs Xayyeesherth

✍️ Xayyeesherthul-humaerath
Chapter 18 · 0% Book details