← Book details Sadaka Yalla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 13

Sashe 9

Sadaka Yalla Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ammie! Ta nanata tana kallon sa cike da mmki tace " Ba Yah Abdul Ahaad Ya dawo ba? Shi basai yazo ba kaine za'a turo ka ɗauke Ni dawowata kenan daga abroad ban to tazali da kowa ba sai bagidaje ƙazami irin ka...ji fa yanda ka cika moton duk da tsami rabon ka da wanka kwana nawa??? Tayi maganan tana kashe shi da ido ta mirror ɗin dake hasko masa fuskar ta ta baya. Duk da maganan nata ya sosa ransa ,amma inda sabo ya saba da cin mutuncin ta... Kiyi haƙuri Hajiya Baya garin ne , sakamakon tura su jejin Kidandan da akayi. What?? Inalallahi wai'ina ilaihir rajiun...au har yanzu ba'a bar mun shi sukuni ba? Ina Hajiya Baaba ta ke? Har tabar Abdul ya kuma komawa halaka? Kai da Allah kayi sauri ka kaini gida yanxu ...sam baxan yarda a kashe mun Miji ba a banza a wofi akan wasu talakawa mara galihu dabbobi. Tun da ta fara maganan Shidai drivern bai ce mata komai ba sai jikin sa dake tsuma na tsoro , don fitinan ta abun tsoro ce , tasha ɗauke ma'aikata da mari ba ɗaya ba biyu ba.... Wannan yasa Drivan saurin ɗaga kai Muryar sa har makerketa yake yace " Eh Hajiya. Shiru tayi bai ƙara jin tace komai ba...sai can kaman ance ya kalleta ta madubi yaga Layla sai sharce hawaye take tare da jan majina. Yau na tabbatarwa cewa ' Su Abie basa ƙaunan Yah Abdul ,yabar sojan nan kuma don dole sai su saka ya koma aikin sa... Bayan da ance Ni za'a ɗaura masa ,na bishi can London mu koma da zama! Dole asan mai yiwuwa bazan yarda ba gaskiya sam.....
****
Kamin Shatu takai Ruga Kam Yammaci tayi don Rana har ta faɗa gari ya fara duhuwa. Baaba kam a waje ta tsaya da ƴar titilan aci balbal ɗin ta ,tana zaman jirar isowar Shatu , don hankalin ta tashi yake ƙwarai idan takai wannan lokacin bata iso ruga ba. Tun daga nesa ta hango hasken acibal bal bal ɗin baaban fulfulbe. Murmushi Shatu keyi tun daga nesa take ƙwaɗa kirar Gwagwgwo na dawo! Kamin wani lokaci tuni kowa na rugar yasan da dawowan Shatu. Don yanda take wage murya ko yaron goye ne sai yasan da dawowan ta. Zuciyar Baaban fulfulbe ne yayi sanyi cike da jin daɗi take faɗin Yauwa ƴar Amanan Gwaggo . Ƙarakowa tayi tana riƙe Baaba a tare suka nufa buka... Ƙwaryar nono na musamman da ta tanadar mata ta ɗaga ƙasan gadon kaban da suke kwana tare baaba na ɗauko mata da liddayi. Fura ta ɗauko mata tana ajewa a gaban inda Shatu tayi warwas ta mike ƙafa na gajiya . Cikin salɓi na Fulani Baaba ta fara mata damun tana yi tana tambayar ta ya kasuwa...anan ko Shatu tafara kora mata labari har da na ƙawarta Rabi , miƙa mata furar tayi Shatu na amsa da hannu biyu tana cewa " Yowa Gwaggo ko Rabi zata taho muna zama tare dake anan .

Tun da ta fara maganan Rabi baaban fulfulbe bata ce mata komai ba sai a yanxu ta bata amsa da: me yasa zata taho gare mu? Bata da iyaye ne? . Eie Gwaggo Iyayen ta basa anan. To ai zata iya komawa gare su. Na fison muyi rayuwa daga Ni sai ke Shatu . Gwaggo ....maza sha furar ki ki tahi wasa dandali. Shiru Shatu tayi don ta lura Baaba bata son maganan Rabi komai yasa??? Tambayar da take mawa kanta kenan. Kaman yanda Baaba ta faɗa mata haka tayi tana gama shan nonon ta miƙe tana fichewa daga bukkan a lokacin Har Baaban fulfulbe tafara barci. Wannan yasa bata san lokacin da Shatu ta fita ba.
****

Ammie!! Ammie!!! Muryar Layla ne ya karade ko ina na falon . Tana kirar Ammie kaman wanda take cikin wani masifa ya same ta. Jin shiru yasata ba Ammie a falon yasata kallon ɓarayin da wata ƴar Aiki uwale take tsaye ta rakuɓe kaman marainiya , don ƴar tijarar Layla ta dawo. Kallon banza ta watsa mata kamin tace " Ina Ammie?? . Bakin Uwale ne ya fara rawa daƙyar ta iya cewa " Tan..tan..tana ɓangaren Hajiya Babba. Ajiye handbag ɗin ta tayi a gyefe da sauri ta juya tare da Nufar sashen Hajiya Babba.

*Yau page ɗin ba yawa a gantale😂 gashi free page ya kusa ƙarewa... regular ₦300 vip group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko MTN card ta wannan Numbobi 08081202932*
[11/8, 4:05 PM] ANTY AISHA MMN TEDDY: *🕊️SADAKA YALLA!🕊️*
_(Baraa ko karuwanci! Funny, romantic and sympathy story)🤦‍♀️_

009

*Masu buƙatar duk ka littafaina zasu na same su complete Inshaallh*
Walijaam₦300
Siyasata₦300
Gidan ƙwarata₦200
Ƴar Aiki na₦100
Dijama ƴar Fulani ₦200
My lady boss₦500
Ƴar maula ₦300
Ƙwarton manya #500
Bintoto
Taɓara₦500
Kawaliya₦300
Zuma da maɗaci₦200
Ƙwaryar sama₦300
Gidan zawarawa₦300
Bafullatanan Ruga₦200
Habibi da'iman da dai sauran su;
Chapter 9 · 0% Book details