← Book details Sadaka Yalla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 13

Sashe 11

Sadaka Yalla Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shatu shatuu!!! In wara Wanzan!!! Ta Amsa masa cikin harshen Fulani. Da gudu ta nufi inda Wanzan yake , shi kam Abdul Ahaad ka sa magana yayi da ido ya rakata yana hango bafullacen da ya kirata can nesa suka yi , don ita Shatu ma ta manta da wani Abdul Ahaad . Zufa ne yaji yana tsatstsafo masa. A hankali ya fara takawa tare da barin wurin ,sam ya rasa me zuciyar sa ke ayyana masa a kan Shatu. Ji yayi a wannan lokaci ya tsani Wancen da take kira da Wanzan , ji yake kaman ya ɗaga shi ya buga da ƙasa ya mace ko ya zamana bashi da mamaro sai yaga ta yadda zaiyi Auren. A haka har ya isa inda su Samir suke bai ma san ya isa ba. Oga yadai? Samir ya katse shi yana maganan tare da gyara zaman alburusan sa. Komawa yayi yana zama a wani ice , dake passing ɗin ɗakin da sukayi nasu na kansu a jejin Allah , irin yanda sojoji keyi su haɗa ɗaki da ganyayyaki da itace kuma suyi rayuwar su na wucen gadi kamin su tashi subar wurin. Samir ina jin Sha'awar ta! Ina kuma jin azabtaccen kishin ta ,wanda ban taba jin irin ta ba ,ko nayi akan wata mace ba. Kallon sa Samir yayi sai ya cigaba da aikin sa ...Don ya lura Abdul Ahaad kaman Raina masu hankali yake son yi. Nuradden dake gyefe ne ya amshe shi da cewa " Don Allah JAGABAN kar ka raina mawa mutane hankali just say it freely, you're in love babu wanda fa zai hanaka. Kar ka raina mana hankali. Kawai sai suka sheƙe da dariya. Taɓ Ai Abdul na tausaya maka , Wallh kana masifar Son wannan yarinyar . Yanxu kai zaka iya auren Ƴar daji bafullatana , wacce bata san komai ba ba wayewa ...ina ƴammatan ka Shirley Angelica duka suna ina? Ina Layla ? Kar ka manta Fah su Ammie Layla zasu aura maka..kar ka yaudari yarinya kaga nan da sati uku zamu koma don Allah ka nisan ta kan ka da ita. Kaiii ibeg shut up. Wannan banzan magana ce , dama nace maku Son ta nake? Ai Ni har yau ba'a yi macen da zan so a zuciyata ba ,a takaice mata ma basu da gurbin da zan so su a zuciya ta. Sai dai idan sun nuna suna ƙauna ta bazan ƙi ba. Kawai ku fahimta ,ita ɗin Sha'awar ta nakeyi !. Kuma baxan yarda wancen ƙazamin ya fara sanin ta ba ,Ni zan fara nitso nayi ambaliya a ƙwarƙwadon madarar daɗin ta. Kuma zanyi hakan kamin na tafi . Dole na kauda ƙwala mata akan ta.

Hummmm kuma ban ga laifin ka ba Fah Abdul ,don wallahi Ni yarinya ina Son ta na sona , to indai bafa zamuyi wani abu ba , to a aje soyayyar kawai a gyefe kowa yayi hanyar gaban sa. Nura ne ya katse su da cewa " a'a Fah , mu da muka taho aiki ,kuma mun ƙare ,Abdul bafa a ƙasar nan duka muke zaune ba. Kar ka lalata rayuwar yarinya ka tafi ka barta da damuwa. Bata da kowa ba kuma lallai iyayen ta su ɗau hakan a ƙaddara ba. Sannan kar kaje kuma garin mugun ta koma kan ka.ka tafi ka dawa kana neman ta ido biyu a lokacin da tayi maka nisa , nisan da sai dai kallo. haahaaahaaa!! Suka wani sheƙe da wata irin mahaukacin dariya ,Samir na aje bindigar sa a gyefe tare da ɗaukar latr yana kuna sigari. Wai anan dajin kake tunanin tayi mun sama. To dama Son ta nake? Sha'awar ta kawai nake yi. Kuma da zarar na kau shikenan tayi sha'anin ta kowa yayi hanyar sa. Dama ruwa ba sa'an ƙwando bane. Ƙarya kake yi ,tun da har kake Son lalata rayuwar yarinya ƙarama wallahi kar kuyi hakan. Saura kwana nawa ne zaka Angon ce?. Kai don Allah kyale wannan banzan .

Samir ya katse shi ,kamin yace " mata Fah yake tsoro , amma yayi faɗa da maza inbN da tsoro har wannan yarinyar abun wani tsayawa dogon magana ce akan ta. Yanxu kaji Abokina ya za'a yi ka sameta. Amm kana ji yanxu haka tana da wanda take so kuma yake Son ta. Amma kasan Ni samun soyayyar ta Abune mai sauƙi , sai dai ƴar daji ne ,ba zata amince dani nayi wani Abu da ita ta hanyar zina ba. Dole mu san mafita. Shiru su duka sukayi ciki harda Nura , da a yanxu yace " Gaskiya kayi magana ,ai zina ma bai dace muyi da wannan yarinyar ba ,sai rashin imanin namu na soja yayi yawa. Kai da Allah dama mu soja muna da wani imani ne?. Yayi maganan yana cewa " ka fidda mana mafita kawai. Shiru Nura yayi kamin yace " To ka turo su Abie su nema maka Auren ta bayan ka yi nasarar samun soyayyar ta. Dukan su wani irin kallo suke bin Nura dashi ,kamin Abdul yace " Amma dai yanxu ka gama shan barasa hala?. Dariya Samir yayi yana cewa " Jagaban kawai muyo hayar iyaye su nema mana Aure. Mu samu ƙwararrun masu gini , a sati suyi maka gida dai dai a nan. Sati uku ne dama ,ka Aure ta na sati biyu ,ka min nan duk jarabar taka da sha'awar nata Duk sun tafi ai ,shi kenan sai mu kama gaba , kaga dai na daya baxaka sha dukan walakiri ba , ta sunna ce! Na biyu ka bar mata gidan aiko wannan ta tashi da arziki , sa siyar su ƙara shanaye ....Dariya suka sheƙe dashi su duka don har Nura ya dara , a yanxu yaji ba laifi tun da Aure n Shatun yace zaiyi na sati biyu!
****
Ɓangaren Shatu da Wanzan rarrashin ta yayi tayi akan zai shawo Umman shi ya bata haƙuri ta amince da auren su , sun fi awa uku suna hirar soyayya. Wanda sai da rana ta fara faɗawa sannan suka rabu ta juyo zuwa bukkan su... Waƙoƙin ta take yi na Fulani har ta ƙarako bukkan su. Gaban ta ne ya faɗi ganin Abdul Ahaad tsaye yanda ta barshi haka ta same shi ,sam ta manta dashi sai a yanxu da suka ƙara ido biyu. Hamm.Hamma!! Ta faɗi sunan Muryar ta na rawa ,kamin tace"Na manta da kai kayi haƙuri Aradu Wanzan ne yazo... Hannun sa yakai yana rufe bakin ta cikin sauri ,wanda bai taɓa mata ba , jin zafi yayi kirar sunan Wanzan da tayi ...No I hate it . Bana so naji kina kirar Sunan Wannan ɗan uwan naki ! Kin san me yasa?? Yayi maganan yana kallon ta ido cikin ido , itako Shatu tsoro ya gama kamata jikin ta sai rawa yake karrr³ bata taɓa ganin sa cikin irin wannan yanayin ba..duk ya sauya mata tamkar damusa mai harin wani... manyan idanun sa sun rine daga fararen nan tass Zuwa jahh. Cike da tsoro ta girgiza masa kai na alamun a'a ". Sauke hannun sa yayi yana sauke nannauyar numfashi mai huci yace "Saboda ina Son ki!
Baya tayi da sauri tana dafe ƙirji da hannu biyu , na shiga La'ilah ha'ilallahu! Ni ɗin Hamma Wallh ƙarya ne! Nifa kake so kai ɗan binni kace kana Sona! Gwaggo!! Ta ƙwaɗa kirar Baaban fulfulbe cikin ɗaga murya da tsorata. Ji tayi ya matso ta yana haɗeta da jikin shi ...wani abu tayi yana mata , wanda ta rasa gane kangadon ina take duniya ko a lahira...bata ji bata gani...numfashin ta ne ya fara season , kawai sai taji ɗiff tayi luuuu tana faɗawa jikin shi alamun numfashin ta ya ɗauke ....Abdul kuwa sam ya gaza zare bakin sa daga nata cigaba yayi da tsotsan.......

*Tofah Babban magana shin Shatu zata Auri Abdul Ahaad ? , Kuma manufar sa zai cika ,bayan ya aure ta zai rabu da ita ko kuwa ƙaka??? Hummmm masoya free page zai ƙare a page na gaba ,ku hanzarta wajen siyan naku domin ki samu ayi tafiyar dake...don Allah kar ki saya ki fitar mun na roƙeki. Regular group ₦300 vip ₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ki tura katin MTN ta wannan Numbobi 08081202922 idan littafin ya kammala complete ɗin shi duka 1k*
[11/9, 7:01 AM] ANTY AISHA MMN TEDDY: *🕊️SADAKA YALLA!🕊️*
_(Baraa ko karuwanci! Funny, romantic and sympathy story)🤦‍♀️_

Last free page
(Shafin ƙyauta ya ƙare daga wannan)

10

*Masu buƙatar duk ka littafaina zasu na same su complete Inshaallh*
Walijaam₦300
Siyasata₦300
Gidan ƙwarata₦200
Ƴar Aiki na₦100
Dijama ƴar Fulani ₦200
My lady boss₦500
Ƴar maula ₦300
Ƙwarton manya #500
Bintoto
Taɓara₦500
Kawaliya₦300
Zuma da maɗaci₦200
Ƙwaryar sama₦300
Gidan zawarawa₦300
Bafullatanan Ruga₦200
Habibi da'iman da dai sauran su;
Chapter 11 · 0% Book details