← Book details Sadaka Yalla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 13

Sashe 8

Sadaka Yalla Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shigar Hajiya Ainu siyasa shi ne musababbin faruwar komai tun daga salsila. Ranan da baxasu taɓa mantawa ba itace wannan rana ,wacce Hajiya Didi Mahaifiyar Alh Yero tayo kirar su da tsakar rana akan tijara da fitina nata. A wannan Rana Hjy Ainu tayi kuka ta gode Allah akan zagi da tijarar da tasha na Hajiya Didi ,tana cewa ta gama mata da ɗa ,kuma Aure zai ƙara zaya Auri ƴar uwan sa da suke ƴaƴa maza . Dama ta daɗe bata haihuwa ba , sai da tafi shekara goma ,gashi tun da ta haifi ɗaya zia wato Zainab mai sunan Hajiya Didi bata ƙara haihuwa ba. Tana bukatar jikoki da yawa yayyame da ita don haka Aure zaiyi. Wannan magana ya ɗaga hankalin Hajiya Ainu da mijin nata wanda yake shahararren ɗan kasuwa kuma ɗan dangi ,don dangin Alh Yero Auren hadi suke ,akan shi ya fara auro bare kuma SADAKA YALLA,wannan yasa Sam Hajiya Ainu bata da fari a idon Hajiya Didi. Da wuraren yammaci suka baro gidan dan Hjy Didi da yake gaskiya layout. Maama Maama!!! Zia ta Kira sunan ta kusan sau uku ,kamin Hjy Ainu ta juya tana saurin ɓoye damuwar ta...Maama meye Sadaka Yallah? Hajiya Grandma duk idan tana son Saki kuka sai tace maki Sadaka Yalla! Meye shi Maama?. Cikin ƙaƙalo murmushi Na dole kawai sai hawaye ya fara wanke ma wa Hjy Ainu idanu , No my baby! Don't put it on ur mind Zia. Ba komai , nice Sadaka yalla Kar ki manta ko gaba ko me kika zama kika gansu suna Bara a titi kar ki ƙyamace su nima Sadaka Yalla ce Maaman ki........ƙiiiiiiiƙuuuuuuuuuuu kawai kakaji a tsakiyar ƙwalta titin tsakanin ɗan Magaji gaskiya.....Wata babban moto ce ta shigar masu gaba , wanda moton nasu sama tayi kawai sai tayi cikin wani ƙwatantazo....wannan kenan! Gigif Hajiya Ainu ta tashi daga ƙwancen da take sunan Zia kawai take ambato ,Wanda cikin sauri Alh Yero ya kamata yana rungume ta jikin shi tare da fara mata Addu'oi , don yasan Abun da ya tada ita cikin kiɗima tuno da abubuwan da suka faru shekaru goma da suka wuce ne. Rungume shi tayi tsam tana fashewa da kuka mai ban tausayi da ƙaryar da zuciya ....

❁࿐❁✿✿
RUGAR KIDANDAN kuwa komai sai dai muce Alhmdllh, domin kuwa sun samu sauƙi daga dukkan wasu masu kawo masu hari. Ƙwana biyu aka yi ana mawa Shatu riƙiya a tunanin su jinnu ne suka shafeta duba ga yanayin weather n. Haka ta ƙwana huɗu bata fita ko ina ,kullum tana kewayen bukkan . Shiko Abdul Ahaad tun bayar rabuwar sa da Shatu su Nura da Samir suka fara ce masa mijin ƴar Fulani da sokana iri iri...wai saboda bada kula har ruga yakai ta...Kai tun baya tunanin yarinyar yafara tunanin ta a zuciyar shi .... A ranan da yakai kwanan su Baƙwai ne da haduwa da kansa ba tare da kowa ya sani ba ya nufi cikin rugar...acan gyefe ya tsaya inda babu mai hango sa....Shatu ya gani a tsakiya anyi da ira ,wani mai waƙar shantu da irin ƙoroson nan na mutan jeji yana bugawa ita kuma sai rawa take tana juya jiki kaman wanda babu ƙashi a jikin ta... Wani dariya Ne Abdul keyi wanda shi kan shi bai Son ya iya wannan dariya ba. Ganin yanda Shatu ke rawar hauka ,ita a dole wai Rawa take shiko mai ƙoroso sai ambaton sunan ta yake yana buga shantu mai kama da ƙwarya. Zokaga fulanin rugar yanda suka yi rumfa suka rufe wurin kowa na bin Shatu da kallon burgewa...a takaice a haka Abdul Ahaad ya shagalta wanda bai koma jejin su ba sai yammaci.............

❁࿐❁✿✿
A washe gari ne tun safe Shatu tayi shirin fita kasuwa don ƙwarya uku ta cika da nono tana ɗaurasu duka akan ta ... Kamun rana ta fito tuni ta isa cikin garin Zaria ,ƴan nono dake anan tudun Wada . Tun daga isowan ta masu adaidaita da suke zama a wurin suna jirar masu hawa suka fara tsokanan don sun san ta da surutu suna cewa ":a'a yau fulfulbe ne da kan ta,Allah yayi maku fitowa daga hannun kidnpers .Harara ta watsa mawa ɗan liti dake tsokanan ta ,dariya yasa yana cewa " Haba Shatu me yayi zafi? Shawara kar ki koma Ni zan baki gida na kiyi zama da Matana a can. Kin guje mawa....kai ɗan liti ya isa...Ai to Allah yakawo mana wasu sojoji masu kama da Samudawa...ka gansu ne? Ai dole ɓarayin nan su gudu. Zaro ido Ɗan liti yayi yana cewa " Ai Shatu naji labari...Allah dai yasa bakiyi gudu gwari ba...su ƴan kidnp sun gudu ,ke kuma wani sojan ya ɗauke ki ya gudu dake.... Kallon shashasha tayi masa tana sauke ƙwaryar ta ,tare da fara sayar da nonon . Kamin kace kobo saboda Shatu yarinya ce mai surutu ga sokana sosai take da farin jini kowa na Son ta...tana zuwa da nono kaman ta zubar tuni ya ƙare . Harhaɗa ƙwaryar take a wuri ɗaya kamin ta juya ta kalli Rabi dake kusa da ita...duk idan an ci abu a bata ,ita ba sayar da nonon take ba. Abun ka ga Shatu baki baya iya gani yayi shiru , cewa tayi " Ohh ke Rabi a haka zaki ƙare ,kullum bakya sana'a sai zaman jirar wani yaci ya baki?. Kema ya kamata ki na rinƙa ɗauko nono kina sayarwa daga rugar ku. Kallon ta Rabi tayi sai a hankali tace "Shatu ai Ni bana da kowa anan!. A'a ke ba Fulani bace?. Shatu tayi maganan tana aje ƙwarya tare da Son Jin Amsa. Gyaɗa kai Rabi tayi alamun eh kamin tace " Ni Fulani ce Amma ta buzaye.ba anan Nigeria nake ba ,ragowar nayi daga ƙasar mu... Ni sadaka Yalla ce! Wani irin bugawa Shatu taji ƙirjin ta yayi....kan ta ne ya wani irin juya mata yana mata gab³ wanda bata taɓa jin irin wannan juyin ba... Dafe kan ta tayi da ƙwaƙwalwa r ta ke juya mata....Ganin ta dafe kai yasa Rabi saurin kama ta tana faɗin Shatu lafiyar ki? . Kusan minti ɗaya tayi bata ce komai ba ,sai can ta nisa tana cewa " Ni ji nayi kaman na taɓa jin wannan sunan Me kika ce? Ɗan maimaita mun...

#Share🙏

*Free page zai ƙare a page 10 ku hanzarta wajen mallakar taku ... regular payment₦300 VIP ₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932*
[11/7, 12:10 PM] ANTY AISHA MMN TEDDY: *🕊️SADAKA YALLA!🕊️*
_(Baraa ko karuwanci! Funny, romantic and sympathy story)🤦‍♀️_

008

*Masu buƙatar duk ka littafaina zasu na same su complete Inshaallh*
Walijaam₦300
Siyasata₦300
Gidan ƙwarata₦200
Ƴar Aiki na₦100
Dijama ƴar Fulani ₦200
My lady boss₦500
Ƴar maula ₦300
Ƙwarton manya #500
Bintoto
Taɓara₦500
Kawaliya₦300
Zuma da maɗaci₦200
Ƙwaryar sama₦300
Gidan zawarawa₦300
Bafullatanan Ruga₦200
Habibi da'iman da dai sauran su;

❁࿐❁✿✿

Sadaka Yalla Mana Rabi ta kuma nanata mata a karo na biyu....shiru shatu tayi tana faɗawa wani tunanin ta dabam ,wanda ganin hakan yasa Rabi cewa " Shatu tunanin me ne kikeyi haka?. Yamma nayi ya kamata ki koma rugar ku kamin gari ya rufa. Hummmm nisawa Shatu tayi tana miƙewa tare da ɗaukar ƙwaryakun nata da ta tattara su wuri guda. Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tana ce mawa Rabi " Yanzu Rabi ke anan zaki ƙwana kenan ,baku da buka irin namu? . Murmushi Rabi tayi cikin mai da damuwar ta ta hanyar nuna komai ba komai ba tace " Eie Shatu anan dama muka saba ƙwana kinga can ƙarƙashin kadan kubanni anan nake kwana kullum , koda kin taho gobe bana nan kika zo can zaki same Ni . Gyaɗa mata kai Shatu tayi alamun to, kana ta juya don nufar rugar Kidandan kai tsaye.
***
Saukar ta kenan daga filin jirgin Aviation dake nan cikin garin Zaria...fuskar ta kacame babu harka ,babu kuma alamun mai wannan fuskar tasan wani abu wai shi kirki ,kallo ɗaya zaka yi mata kasan irin wa'anan yaran ne ƴaƴan manya marasa mutunci tijarar ru ,wanda basa ganin kiman talaka sam. Idon kowa na wannan Aviation na akan ta ,ganin sunan tana gida nageria ne ,amma shigar ta duk ya sha banban dana mutanen ƙasan. Shiga ne tayi shi irin na turawa , duk da kasancewar tasa doguwar riga ce mai launin milk ta kuma yane kanta cikin ƙaramin mayafin rigar. Malfa ta ɗaura kalon dressing ɗin nata tana fara takowa izuwa inda take hangar drivern da ya taho ɗaukar ta . Barka da isowa Madam Layla! . Drivern yayi maganan tare da ɗan risinawa na girma yana buɗe mata murfin moton , Kallon shi tayi tana kauda kai kaman bata ji mai yace ba, tana shigewa moton cikin yatsini da rashin mutunci. Ɗan tsaki tayi dai dai yana rufo murfin moton tare da shiga mazaunin sa yana fara driving. Kusan mintuna biyar batace masa komai ba ,duk da Tambayar dake cikin ta Issa ya hanata tambayar a tunanin ta tayi hakan ƙaskanci ne. Kai Waya baka izinin tahowa ka ɗauko Ni ?. Tayi maganan tana wani irin hura hanci na tijara ,cikin sauri Drivern yace " Afuwan Hajiya , Hajiya Ammie ne ta aiko Ni.
Chapter 8 · 0% Book details