← Book details Sadaka Yalla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 13

Sashe 4

Sadaka Yalla Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali cike da lura take sauka daga stairs ɗin underground ɗin...wanda ganin ƙayatuwar ƙasan wannan wuri har ƴar laptop ɗina na kuɓcewa arxiƙi ɗaya bata sha ƙasa ba ,da nace typing kuma sai an ƙwana biyu🥴 . Allah dai ya taimaka na riƙe ta ƙammm bata kai ƙasa ba. Falon shi ake kira da alnnar duniya a ƙayatuwa da ƙyau da dukiyar da tayi ihunn wayyooo ...hasken falon kaɗai yanda yake haskaka idon ka ya sani faɗin gloves ɗin ma wurin na daban ne ba irin namu ba.

❁࿐❁✿✿

Shiru shiru yasa ta miƙewa tare da nufar bathroom don ganin mijin nata daɗewar nasa yayi yawa ,duk da kasancewar tasan bai san da shigowar ta ba. A bakin ƙofan ta tsaya tana miƙa yatsanta tare da danna wani wuri daga jikin ƙofan ,nan take ƙofan ya ware. Ƙafan ta tasa kai tsaye tana miƙa kan ta cikin toilet ɗin... A tsaye ta ganshi haihuwar uwan sa ,da dye a hannun sa.... Yana kallon ƙaton mirrow n dake privacyn ...bin duk wata kafa na gashi a jikin sa yake da wannan dye ɗin baƙi yana ɓatar da tsufan sa ko nace furfurar sa don Alh Aminu yero yakai kusan kimanin shekaru 70 saba'in a duniya...attajiri mai fama da giyar kuɗi tun ƙuruciya kuma tantiri wanda tantirancin sa ya zarce na da yawa samarin mu a yau! Ɗago idanun sa yayi yana kallon ta ba kunya idon sa a soye kaman ba mai wannan shekarun ba yana faɗin Hajiyata brk da dawowa!kasa basa amsa tayi don a yanxu tsoran mijin nata ya fara kamata Wani ƙirjin Hajiya Ainy ne ya buga , a zuciyar..............

_Kuyi manaji da wannan yanxu na dawo daga aiki a gajiye ,idan kin karanta pls kar ku manta kuyi mun share ngd🙏_

_Littafin na kuɗi ne kamar yanda kuka sani Regular payment₦300 VIP membership ₦600 Spc 1k...Zaki iya turo da kuɗin ki ta wannan asusun bank account 6037312299 Mohammed A'isha Keystone bank ko ki tura katin MTN ta wannan Numbobi nawa 08081202932 ƴan Niger zaku biya 600f katin airtel..._

*MAMANTEDDY*
[11/3, 3:18 PM] ANTY AISHA MMN TEDDY: *🕊️SADAKA YALLA!🕊️*
_(Baraa ko karuwanci! Funny, romantic and sympathy story)🤦‍♀️_

Free page
004

*AUNTY AISHA MMN TEDDY*

_Littafin na kuɗi ne kamar yanda kuka sani Regular payment₦300 VIP membership ₦600 Spc 1k...Zaki iya turo da kuɗin ki ta wannan asusun bank account 6037312299 Mohammed A'isha Keystone bank ko ki tura katin MTN ta wannan Numbobi nawa 08081202932 ƴan Niger zaku biya 600f katin airtel..._

❁࿐❁✿✿

*Masu buƙatar duk ka littafaina zasu na same su complete Inshaallh*
Walijaam₦300
Siyasata₦300
Gidan ƙwarata₦200
Ƴar Aiki na₦100
Dijama ƴar Fulani ₦200
My lady boss₦500
Ƴar maula ₦300
Ƙwarton manya #500
Bintoto
Taɓara₦500
Kawaliya₦300
Zuma da maɗaci₦200
Ƙwaryar sama₦300
Gidan zawarawa₦300
Habibi da'iman da dai sauran su;

Cike da zafin namaa kuma cikin sauri Hajiya Ainu ta jah ƙafarta daga toilet ɗin cikin ɓacin rai tana fichewa don ganin Alh Yero a wannan yanayi baƙaramun ɗaga ranta yayi ba ,da sosa zuciyar ta ,kullum zuciyar ta na ɗauke da famin abubuwa na baƙin ciki na mijin nata....a yau ganin sa take tamkar ƙwarto ta ke kuma jin kaman ba harramin ta ba.

Falo ta fito tana kaiwa da komowa don sam ta gaxa fita daga apartment ɗin nashi , a yau bata jin zata iya ɗaga masa ƙafa tayi haƙuri kaman kullum kaman kuma yanda ta saba. Kusan mintuna talatin ta fara jiyo sanyayyar ƙamshin sa, hannun sa riƙe da briefcase ta alhazai ƴan kasuwa masu damawa ƙwarai. To Hajiya Ainu na wuce". Ɗago da idanun ta tayi tana watsa masa wani irin kallo mai tattare da tuhuma , kamin ta girgiza kai tana haɗiye wani ɗaɗɗatan yawu da ya shige da ƙyarrr...motsa laɓɓan ta tayi cike da salɓi da sanyin jiki irin nata tace " Allah ya kiyaye hanya Alhaji". A kowani hali a kuma ko wani yanayi ina roƙon Allah ya kiyayeka daga sharrin shaiɗan da faɗawa halakar sa...tsayawa yayi yana juyo da hankalinsa sosai a kanta tabbas ya fahimci inda maganan nata ya dosa ,amma sai ya dake tamkar bai gane ba....jin shirun nata yasa shi cewa " Amin Amin Matan! Amma meyakawo wannan maganan da tsakar yammaci haka?. Yayi maganan irin na yagaggun Alhazan bariki . Murmushi Hjy Ainu tayi don komai da zaiyi sai dai ta kallesa a ido kawai ...ba komai Alhaji wai dai addu'a ce , don rayuwar mu a yau ya zama abun da ya zama. Fatana dai a kullum mu ka sance masu gudun duniya mu na rinƙa tunawa da ƙiyama. Don idan mun lalata ƴaƴan wasu ka tuna kaima ka haifa kuma abun da kayi za'ayi mana ka..idan baka haifa ba ,ƴan uwan ka sun haifa maka.

Kee da Allah ya isa haka nan..wannan wani irin shashanci n magana ce? Ƴar dana haifa kike mawa fatan tsiya Ainu? . Kallon sa tayi ido cikin ido kamin ta wadeda kanta ƙasa , tana girgiza kai tare da faɗin ba haka bane ba , Ai gaskiya ce dama kuma ita tana da ɗaci....naga bamu da ƴa ko ɗa a duniya a yanxu ,kawai dai....ya isa Ainu! Bana Son irin wannan maganganun yana tada mun da hankali da kuma ɓata mun rai. Don haka ki daina shi indai ina wurin. Har kin cire rai ga Zia tana raye kenan,dama na daɗe da fahimtar kin sa mawa kanki ƴata ta mutu...to koda zan shekara Ɗari ko hamsin bazan cire wa raina cewar babu Zia a rayuwa ba...tana nan kuma zata dawo gare mu Inshaallh. Yana gama maganan ya juya ran sa ɓace don har ya manta da haɗuwar sa da ƴan iskan matan da suka saba shigewa Alhazai saboda son Abun duniya. Raka shi tayi da ido ,wanda kawai sai zuciyar ta ya karaya ,tsugunawa tayi ƙasan capet tana fashewa da wani irin kuka lokaci ɗaya kewar ɗiyar nasu ya dawo mata sabo fil tamkar yau ne komai ya faru na baƙin ciki a gare su ....

❁࿐❁✿✿
Inalallahi wai'ina ilaihir rajiun abun da kowa na gidan mai unguwa yake faɗi kenan masu kuka nayi masu bamawa Baba Mai unguwa nayi! Baba kawa girman Allah kayi haƙuri wannan abu baiyi ba...Da tsufan ku ace ka Saki Inna? Dukan ku babu ɗan ƙasa da shekaru Saba'in kawai sa suwai ta fashe da kuka wacce take surika wurin mai unguwa. Shi ko mai unguwa babu nadama faɗi take Ni na saketa ...ina buƙatar mata mai jini a jika don haka aure zanyi ,sadaka yalla zan Aura ,gasu Nan a hanyar unguwan gwado sai wanda ka zaɓa har da ƴar sha bakwai...
SADAKA YALLA! Suka maimaita cike da tashin hankali... wanda bai basu amsa ba sai cewa yayi " A yau a kwashe mun komai na dakin nan don a satin nan zan Auro Balaraba. Yana faɗin haka ya juya yana gyara malinmalin ɗin sa tare da fichewa daga gidan . Suwai ne tasa haɓar zanin ta ,tana goge hawayen dake zubo mata , tare da kallon sasan ƙanin Baba mai unguwa wato malam Rabi'u. Su dai haka nan Allah yayi su ruwan jaraba ,har tsufa basu da dama. Gomma malam Rabi'u bai kai tsufan mai unguwa ba...amma a haka yake da matar sa kullum baya gajiya da ƙwanciya da su...ba rana ba dare. A haka ƴaƴan su suka girma suka gansu ...sai dai suji masu kunya badai su suji mawa kan su ba. Saboda jaraba irin na malam Rabi'u idan yana saduwa da ɗaya daga matan nasa dama su biyu ne ,ɗaya tana ƙofa ne tana gadi ,yana gamawa da ta ciki sai ta fito itama ta kama gadi ,na wajen ta shiga...a haka sai su wuni jungum suna abu ɗaya... Idan kuwa dare yayi sai sukai salatu a dare kuwa duka gado ɗaya yake saka matan yayi da wannan yayi da wancen abun bayi da kyau amma shi jaraban sa tayi masa yawa.
"Da yawa masu karanta wannan littafin na Sadaka yalla zasu ga labarin kaman irin fiction story be ,but is not ,wallahi abun nan is really ya faru kuma presently yana kan faruwa na wannan gida . Haka na sadaka yalla , Kar ku karanta kuce is it just a fictional , ba haka bane ,nayi ne don da yawa mazaje su wa'aztu ,don nasan mabiyana da mata da maza ƴammata duka kuma bin labari na ,shi yasa na tsaya na tace na kuma kawo maku wannan don faɗakarwa ,gashi Fah aƙwai dariya😂 abun dai yana a gaba... muje zuwa! Duk wannan abun dake faruwa da tsakar rana sam basu sani ba...su dudu ana can ƙasan malam Rabi'u ana ibada😂 . Suwai ne ta leƙo sasan tana ganin Binta inda dama tasan bai wuce ita zata gani ko dudu ɗayan su na gadin ɗaya . Takaici ne da haushi ya kama Suwai cikin wani irin murya tace " Hala Binta baku ji mai ke faruwa a gidan nan bane? . Cikin borin kunya Binta tace " Banji ba meke faruwa! Taɓe baki Suwai tayi tana cewa " To ki sanar mawa Malam Rabi'u mai unguwa ya saki Mama saki uku yanxun nan. Inalallahi wai'ina ilaihir rajiun Binta ta hau nanatawa tana salallami ,wanda suwai bata tsaya jin na bakin ta ba , ta fice daga sasan cike da tashin hankali.
Chapter 4 · 0% Book details