← Book details Sadaka Yalla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 13

Sashe 10

Sadaka Yalla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

❁࿐❁✿✿
Y RZƘ
A sashen Hajiya Babba ta tadda Ammie da ita kanta Hajiya Babban tana zaune ta miƙe ƙafa tana saka malmalon tuwo a baki , gaban ta ta tasa Tuwon ta na semo miyar ɗanyar kuɓewa ,don Hajiya babba irin tsofaffin nan ne na gargajiya ita duk a abucucuwa ka bata tuwon ta miyar ɗanyar kuɓewa ka gama mata komai , shiyasa kullum ma'aikatan ta suna aikin ɗaura tuwo da saukewa... Muryar Hajiya Babba ne ya katse na Ammie da take cewa " To ke yanxu Fatima ya ake ciki kenan ,saura kwana nawa ne Abdul ya dawo kika ce...nafa gaji da ganin shi kullum a gwauro! Tun da ya bamu wuƙa da nama a samar masa mata a ɗaura masa ai shikenan ,ga Layla ƴar uwar sa ,dama tuni da Soyayya tsakanin ta dashi.... Ehh Haj...Ammie! Ammie!! Muryar Layla ne ya katse su cike da ɗaga murya tare da Muryar kuka take kirar sunan Ammie. Cikin sauri Ammie ta miƙe daga zaunen da take tana faɗin Na'am ƴar Ammie waya taɓo mun ke ne?. Cike da Muryar sangarci a shagwaɓe ta nufi Ammie da take ware mata hannu ta faɗa jikin Ammie tana fashewa da kuka tare da cewa " Ammie yanzu kun ƙara barin sa ne ya koma? Ammie so kuke yi Yah Abdul ya mutu a wannan aikin Nasa ? Wallahi bana So nidai! Bana So! Kawai Ammie kuce masa ya dawo gida. Wallahi Ammie tsoro nake ji... Eyyyaa Yi shiru nan Layla na taho Abinki ,Hajiya Babba tayi maganan tare da ya fito Layla da hannu , wanda ta miƙe tana raba jikin ta dana Ammie tana nufar ƙasan carpet inda Hajiya Babba ke zaune. Bowl ɗin Tuwon ta matsar dashi gyefe tana dafa Layla tare da faɗin " Yi shiru daina kuka bari Kinji . Saura ƙwana ki kaɗan su fito daga wannan jejin . Ni kaina hankali na kullum a tashe yake...sam bana iya rintsawa , tun da ya shiga aikin soja na daina Samun sukuni da ƙwanciyar Hankali , Amma dole muyi hakuri ,domin kuwa Abdul idan muna Son muga ya cigaba da rayuwar sa kaman sauran mutane sai da abu biyu zamu gan shi cikin walwala . Na ɗaya iyayen sa , na biyu kuma shine wannan Aikin Sojan da yake a yanzu. Don haka a matsayin ki na ƙanwa gare sa , kuma matar sa nan da sati Uku add'ua ya fi cancanta mu yawaita masa Kinji Layla na? Gyaɗa Kai Layla tayi tana goge hawayen nata ,don zuciyar ta yayi sanyi bisa ga Kalaman Hajiya babba da tayi mata ,musamman da ta tabbatar mata nan da sati Uku za'a ɗaura Auren ta da Abdul Ahaad ,wanda take jin Son shi fiye da komai na Rayuwar ta. Murmushi Ammie tayi a zuciyar ta tana tausaya mawa Layla don tabbas tasn irin Son da Layla take mawa Abdul Ahaad ƙwatan ƙwatan shi bai mata. Shi har yau yana mata so ne na yaya da ƙanwa! Allah sarki soyayyar Ahaad a jinin ta yake . Allah ya ƙara miki hakuri da halin sa... Ammie tayi maganan a sarari dai dai Hajiya babba na amsawa da Amin ,tana kuma cigaba da cewa " Ai mai gidan nawa sai haƙuri , fatan yanda nake haƙuri dashi kema zaki iya. Dariya Layla tasa tana cewa " Ina Hajiya yanxu Fah ki bar Kiran shi da Mai gidan ki ...nice dai Amaryar ba keba ,don kin masa tsufa. Eiyeeee Fatima kina jin mai take fadi ƴaƴan zamani halin ku sai ku ...Hajiya Babba ke maganan tana kallon Ammie kamin ta sauke idon ta ga Layla dake Dariya har da ƙyaƙyatawa. Ita dai Ammie murmushi take bata ce komai ba ,don ba mai shiga tsakanin Hajiya babba da ƴan jikokin ta ,ka cika zaƙewa sai kaji kunya .
****
Jah baya Shatu tayi da sauri tana shirin sakin ƙwaryar nonon dake hannun ta. Ɗago da lulun idanun sa yayi yana kallon ta kamin ya sunkuyar da kansa ƙasa kaman mutumin kirki masu ruwa a ido . Baaban fulfulbe ne ta kalli Shatu wanda dawowanta kenan daga bukkan su Wanzan . Lafiya Shatu ? Sai kace wanda kika ga bako baki taɓa sanin sa ba?. Gwaggo na san shi mana! Amma tayaya ya taho nan?. Uhmmmm kiji mun ke da shiririta , ke da bakin ki ki cemun wani ya taba rako ki har nan rugar, Ko bashi bane wannan ?. To ko jiya ya zo nan ya dade baki dawo kasuwa da wuri ba . Hummmm nisawa Shatu tayi tana faɗin kuma baki faɗa mun ba. Ta ƙare maganan tana nufar inda Abdul Ahaad yake a wannan karon cikin shigar su ta Soja. Bin ko ina na wurin yake da kallo tare da mmkin wai bil adama ke rayuwa a wannan jeji haka. Gani nazo! Tace masa tana murmushi. Murmushi shima yayi mata kamin yace " Ai wurin Gwaggo nazo ba wurin ki ba. Saurin kallon shi tayi ,suna haɗa ido taga ya daga mata gira alamun eh ,sai kuma ta juya ga Gwaggo dake ta murmushi . Ohh Gwaggo Kinji daɗi kenan wurin ki aka zo, to sai mene Aradu ban damu ba. Tun da kamin azo wurin ki anzo wurina ba adadi. Dariya Baaban fulfulbe tayi tana cewa " Aiko kin damu ,tun da gashi kin nuna kishin ki a sarari. A'a Gwaggo shine yabani haushi ..wuri na Fah yazo wai amma yace ba haka ba. To ya sanki ne da zaice wurin ki yazo? Uhmm kefa yarinyar nan kin cika tsiwa Gwaggo ina Iyayen Aisha suke? Wannan hawan jini zata samaki. Shiru Baaba tayi sai Shatu da tace " To waya ce maka ina da iyaye? Gwaggo ce Umma na Kuma Baba na..ita na sani ina ta kuma tayi mun komai . Gwaggo faɗa masa kece ki ka haifen". Juyowa Gwaggo tayi cike da jin tausayin ɗiyar nata ,tace " Shatu dama kina da wata uwa bayan Ni? Ai kece komai na haka nice koman ki Shatu. audull Sunan naku ne ta ƴan zamani bana iya faɗa. Laaa dariya Shatu tasa tana cewa " Ya akayi kika san sunan shi Baaba? Sunan shi Fah Soja!

Baaban fulfulbe ne ta katse ta da cewa " kaji mun tselen ƙwaaa. Sunan da aka raɗa masa kenan. Ni bari naje bukkan su Wanzan naji yanda lamarin yake a yanzu ,ko Umman nasa zata amince .kai Gwaggo ki rabu dasu don Allah ... A'a ba ayi hakan ba Shatu , ƙawayen ki da sa'oinki duk sun yi Aure , kin ga kema yanxu yaci ace kina naki ɗakin mijin. Ɗan taɓe baki Shatu tayi tana jin haushin yawan maganan Umman Wanzan da take yawan mata. Tunanin me kikeyi haka? . Taji Muryar sa ya katseta , wanda ta faɗa duniyar tunani har ta fara mantawa da mutum tsaye kusa da ita ,don tuni Baaba ta ɓace ma ganin su. Kallon sa tayi kawai sai tayi rau rau da ido sai hawaye sharrrrrr³ , shiiiii ya isa bari kuka Kinji Shatun Gwaggo. Murmushi tayi jin ya haɗa ta da Farin cikin rayuwar ta wato Baaban fulfulbe , amma duk da haka hawayen basu daina sauka mata ba. Cikin Muryar kuka mai kama da shagwaɓa take faɗin " Hamma dole nayi kuka ,kuma baxan daina ba. Meyasa? Ya tsinci harshen sa da mata wannan tambayar wanda kai tsaye ta basa amsa da "Saboda bana da iyaye , basu san asali na ba , shi yasa Umman Wanzan take cewa Wanzan bazai Aure Ni ba..Hamma don Allah ka kalle Ni fah , me na rasa nidai ba mummuna ba ba kuma wacce take da tawaya ba..tun da Wanzan yana Sona ina Son sa ,basai su bar mu ba ...wani dammm yaji ƙirjin sa ta buga masa , yayin da kansa tayi masa nauyi. Ammm Aisha kina Son Wanxan ? Eh Sosai Hamma! Amma me yasa baki da kunya ta fulani?. Yayi maganan kan sa tsaye yana mmkin yanda yarinya ƙarama ke faɗa masa tana Son Wanxan ,Wanda Haushi ne kawai yaji ya kamsa ,sunan ma bai so ta nanata. Kallon sa tayi cikin rashin fahimta tace " Kunya kuma?. Huuuu Iskar bakin sa ya furxar cike da kauda maganan yace " Ya kike da gwaggo?. Uhmmmm nima har yanzu Ban sani ba ... kaka tace, haka na sani . Kallon ta yayi kai tsaye yace" amma ai ku Fulani kuna Aure a shekaru ƙalilan , eh mana. Ta basa amsa tana kallon sa kamin ta cigaba da cewa " Binto tayi Aure yanxu kasan yaran ta nawa? Girgiza mata kai yayi alamun a'a . Murmushi tayi tana cewa " Uku. Gaban sa ne ya buga Damm". Yace uku Fah kika ce. Eh mana. Ta basa amsa tana kallon fuskar sa tare da daga kan ta sama. Amm yanxu Wancen waye sunan shi kike cewa?. Yayi maganan yana ya mutsa fuska. Wake nan? Ta tambaye shi tana sauraran jirar wa zaice. Saurayin ki mana. Ohh mijina Wanzan. Gyaɗa mata kai yayi yana cewa " amm sai kuma ya tsaya kame kame. Me zaka ce wai Hamma Soja". Kina ji kun taɓa wani Abu dashi ne? . Yayi maganan yana sauke lulun idanun sa a fuskar ta .. data rasa fahimtar inda ya nufa. Ban gane ba , me muka yi dashi ...bikin shaɗi za muyi a wannan watan. Ba wannan nake nufi ba. Ba mata da miji suna wani Abu ba , idan sunyi Aure ko zasuyi. Girgiza kai tayi , tana cewa " Meye Abun? Ban san shi ba Hamma faɗa mun ! Bai taɓa taɓa maki Hannu ko jiki ba. A'a ta basa amsa cike da haukan yaran ta. Kamin ta kuma cewa " Hamma faɗa mun me akeyi? . Kallon ɗan ƙaramin bakin ta yayi da yanda take motsa su , a hankali ya lumshe ido yana cizar laɓɓan sa na ƙasa. Yah Allah! Shine Abun da ya furta a zuciyar sa ,asarari kuma cewa yayi " Meye Hamma da kike cemun a Hausa?. Murmushi Shatu tayi tana cewa " Yaya kenan! Kamin yayi magana ne yaji baƙuwar murya yana amsa kuwa a falfaladan wannan bukkuna ....
Chapter 10 · 0% Book details