← Book details Sadaka Yalla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 13

Sashe 7

Sadaka Yalla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wake nan ? Baaba tayi maganan tana kallon gyefen da Shatu ke kallo. Baaba dashi Fah muka taho wurinan! Shatu Anya baki ƙwaso miyagu ba a dajin nan da kika shiga da rana? Waye zaki gani a daji a yanxu ,musamman yanda rayuwa ta kasance?. Murmushi Shatu tayi tana cewa " A'a Baaba shine yanxu Fah muke tare dashi...dogo fari yana da suma ƙwantattu irin....Wanzo? Wanzo?? Baaban fulfulbe ta fara kirar sunayen mutanen fulanin kowa yazo bakin ta...Kamin kace kobo tuni mata da mazan da sukayi saura sun fito suna faɗin Inna an Wara Yadikko". Wanzan ne ya fito yana ɗingisa ƙafa da yasha dukan barayin sun masa karaya kusan uku a ƙafa ɗaya. Gwagwgwo meke faruwa? .

Ku kira liman Shatu ta fara hauka , miyagu sun shafe ta. Da jin haka basu tsaya tambayar me ya faru ba ...suka banzama niman Liman don sun san Baaban fulfulbe ba zata faɗi Abun da ba haka ba...yaewindo ne tace " Dama tuni na ke wasuwasun Shatu na da miyagu ,musamman yawon son Rawar ta da shiga dajin ta abun yayi yawa.... Kallon su Shatu keyi kurum sai ta sheƙe da dariya tana nufar bukkan su , tare da shigewa .... yafindo ne tace ma wa Baaban fulfulbe su tsaya a bakin bukkan kar su bari ta fito suyi na daji da ita...jin ko haka mata kusan su huɗu suka tsaya a bakin bukkan wai kar Shatu ta fito ,suna zaman jirar isowan Liman.

❁࿐❁✿✿
Malam Rabi'u ne sai can hantsi ya fito daga ɗakin sa yabar Binta ƙwance ko motsi takasa yi saboda jigata da wahala ...koda ya fito har a lokacin gidan cike yake , Haushi ne ya kama Suwai zuyawa tayi tana basu wuri tana jin malam Rabi'u na tambayar wai meke faruwa? Ana kora masa bayani akan yayi wa ɗan uwan sa me Unguwa ya dawo da matar sa da yasaki yana maganan Sadaka yalla zai Aura ƴar shekara Shatakwas dai dai shi yana haura shekara saba'in a duniya. To meye aibu a ciki? Abun da malam Rabi'u ya fara cewa kenan! Kamin ya cigaba da cewa" Dama zama zaiyi ba matar shine aibu, kuma naga uku ya riga yayi , ai shikenan sai haƙuri... inalallahi wai'ina ilaihir rajiun...kai tirrrr da wannan gida da mutan cikin ta, Suwai tayi maganan tana cigaba da tsiyayar da hawaye. Juyawa malam Rabi'u yayi ganin yaran kowa yayi caaa kan abin da yace...don yara ne suke dashi fatsami guda...amma a haka basu san sun girma ba. Tun da suka bar gidan , matan gidan ke cikin tashin hankali , saki da tsufa ,ai ya bari tayi masa takaba tun da saura kwana nawa ne yayi ƙaura sittuna au saba'una to shi yakai har ya wuce. Amma a haka yake da budurwar zuci na son Auren Ƴar shekara sha taƙwas.

❁࿐❁✿✿
Bedroom ɗin shiru kakeji babu komai dake tashi sai sautin kukan ta ƙasa ƙasa , hasken Dumb light yasani fahimtar Hajiya Ainu wanda gyefe guda Alh Amin Yero ne zaune a ƙayataccen gadon nasa , saman cinyar sa ɗauke da laptop Yana operating system ɗin nashi hankalin sa ƙwance. Kaman waƙe take ba kuka ba ,duk a ƙarƙashin zuciyar sa kuwa yana jin zafin kukan nata. Cikin dasasheshiyar Muryar ta na wanda tayi kuka har ta galabaita ta fara faɗin" Yanxu Alhaji Abun da kakeyi kana kyautawa ƴaƴan ka kuwa? Kar ka manta kana cutar dani...Ba ason raina nake zama dakai ba a yanxu ,sai dai ba yanda na iya...Ni ban taɓa zina ba ,Allah ya haɗani da miji m....Aini!! Ya Kira sunan ta yana katse ta...tare da watsa mata idanun sa da suka narke suka tarkade suka ƙyaƙafe suka soye a duniya ....I'm so sorry for that! Nima baa son Raina bane. Dole ne tasa ...kuma yawon maganan ƴaƴa da kikeyi nufa ban haihu ba a yanzu ƴata ɗaya na haifa a rayuwa ,kuma tuni ta daɗe da barin gidan duniya. Baka kuma tunanin Allah ya baka a inda bakayi tunani ba ,idan ta yi aure ta samu miji irin ka , me zaka ce ,kuma me zaka ji...nima Fah ƴace! Wani irin zafi yaji zuciyar sa na masa akan maganganun matar nasa Hajiya Ainu. Wanda cikin Rufewa r ido ,ba tare da ya tache maganganun bakin sa ba ya fara fitar wa kaman haka; ke ƴace? Ƴar wakenan? Kin manta a yanda na Aure ki ba gata! Ni nayi Mako komai na rayuwa! A titi kina Bara na Aure ki a SADAKA YALLA!

_#SHARE🙏_

_Masu buƙatar wannan littafin zasu na iya tuntuɓa na kai tsaye Ta wannan Numbobin 08081202932 / 09061466409 ,if you are not ready ,don Allah Kar Kuyi mun magana I have alot to do! Kar mu ɓata wa juna lokaci...sannan masu tambayar littafaina na kuɗi ne ga farashin ko wanne can a saman page ɗin Sadaka yalla!_
[11/6, 6:13 PM] ANTY AISHA MMN TEDDY: *🕊️SADAKA YALLA!🕊️*
_(Baraa ko karuwanci! Funny, romantic and sympathy story)🤦‍♀️_

007
❁࿐❁✿✿

*Masu buƙatar duk ka littafaina zasu na same su complete Inshaallh*
Walijaam₦300
Siyasata₦300
Gidan ƙwarata₦200
Ƴar Aiki na₦100
Dijama ƴar Fulani ₦200
My lady boss₦500
Ƴar maula ₦300
Ƙwarton manya #500
Bintoto
Taɓara₦500
Kawaliya₦300
Zuma da maɗaci₦200
Ƙwaryar sama₦300
Gidan zawarawa₦300
Habibi da'iman da dai sauran su;

❁࿐❁✿✿

A sadaka yalla na kawo ki a halina , nayi maki Komai na Saki kikayi ilimin addini dana zamani , har a yau kika zama haka mai faɗa a ji ,kika shahara kika zama babbar ƴar siyasa har kike da wannan matsayi na commissioner na sadarwa,ki rinƙa ya isa ! Ta katse shi cike da ɓacin rai tana ɗaga masa hannu alamun dakatarwa. Ƙwarai kayi mun duk wannan abubuwan da jero , kuma na gode! A takaice yanzu gaskiya ce baka so! Shi yasa har ka fara tariyo abubuwa da yawa da suka wuce kake Son faɗa mun a yanxu harda mun gorin ka ganni ina Bara a tsakiyar titi a haka ka Aure Ni ka kawoni a halinka...na gode ƙwarai amma kar ka manta da mutunci na ka Aure Ni ban yasar a titi ba... Maganan Hajiya Ainu ne ya kakere mata sakamakon zuwan wani kuka wanda bata shirya masa ba...kukan ne ya kubɓuce mata ,wanda cike da Muryar kuka ta cigaba da cewa" Na gode mawa Allah da tun kan na mutu na kuma rabu da Zia na sai da na faɗa mata wacece Ni da Asalina. Tun kan tasan meye rayuwar bakin ta da ƙwaƙwalwar ta nasha faɗa mata wannan kalmar na SADAKA YALLA! tasan Mahaifiyar ta ba kowa bace fache mabaraciya! A haka ashe bazamu yi nisan zama ba a rayuwa har mai rabawa ya raba! Nikaina ba'a Son raina na fito yawon sadaka yalla ba ,nabar dangi na nabar ƙasa ta , kai kaico ga matan da suka fara yin wannan sadaka yalla ,har ya zama mana abun koyi yau ga irin ta nan. Jikin Alhaji Aminu Yero ne yayi sanyi ƙalau ,don koba komai yana masifar ƙaunar matar nashi Ainu ,tabbas akan ta da auren su ya fuskanta ƙalubale ,don kowa juya masa baya yayi akan wannan Aure ,wanda har yau mahaifiyar sa Hajiya Didi bata ƙaunar Hajiya Ainu .

Cikin Muryar rarrashi mai tattare da nadama kan abun da ya aikata a yanxu yace " Kiyi haƙuri Ainu..nasan ba laifin ki bane ,nayi kuskure dana jefe ki da wannan kalam, kiyi mun afuwa! Nasan...kamin ya ƙare maganan ne ta juya masa baya tare da jan bargon ta ,kasantuwar weather ɗin da muke ciki na sanyi ...mu tashi lafiya shine abun da tace tana juyawa tare da rufe idanun ta kaman mai barci ,amma kuma sam ba barcin take yi ba , damuwa da abubuwa da yawa da suka faru suka shiɗe take tunawa a dai dai wannan lokaci........Waiwaye adon tafiya! Tuna baya!!
Maaama Daddy!!! Muryar Zia ya karaɗe ko ina na cikin wannan gida. Sakin glasscup ɗin dake hannun ta Hajiya Ainu tayi tana fitowa daga Kitchen cikin sauri a tunanin ta wani abu ne ya samu ɗiyar nata ɗaya tilo. Ɓangaren Alhaji Yero da ya gama sanin wacece Zia a hankali ya sauke jaridar hannun sa yana kallon inda Zia take tsaye a kan stairs ɗin falon. Dafe ƙirji Hajiya Ainu tayi cike da Son jin lafiya wannan kira da tsakar rana tace ' Zia!! Kecewa da dariya yarinyar tayi wanda ashekaru baxata haura 7 zuwa taƙwas ba , murmushi tayi tana faɗin i love You Maama! I love Daddy!! I lab u both.... Murmushi Hajiya Ainu tayi kamin suyi magana Zia tayi ɗakin ta da gudu cike da ƙiriniya ta haye stairs ɗin....I lab you much my dear daughter. Cewan Alhaji Yero . Itako Hajiya Ainu juyawa tayi tana girgiza kai cike da jin Son ɗayar nata ainun.

***

Safiyar Lahadi wannan rana ,ranace da duka suke gida kasantuwar weekend , Zaune suke duk familyn Wato Hajiya Ainu da Alh Yero sai kuma ɗiyar tasu Zia ,wacce take kusa da ƙafan mahaifin nata tana akan carpet ɗin dake ƙasa , gaba ɗaya hankalin ta na akan ɗan mini laptop ɗin ta pink na Yara ,Wanda babu abun da take yi sai playing games . Ƙarar buɗewar Gate ne yasata miƙewa da gudu tana tsalle da tafi na yara tare da cewa" Yeeeee Daddy gamai photographer Nan yazo! Suna a haka ne sai ga sallamar mai hoton da suka ɗauko shi musamman a wannan weekend don Jin dadin wannan a hali... A haka kullum suke rayuwa , cike da jin dadi da walwala da kuma ƙwanciyar hankali. A wata Ranan Monday ne Zia sai tuƙuƙi take tana haɗe gira sama da ƙasa ,kamin Alh Yero da yake miƙo mata school bag ɗin ta yace " Lele na waya taɓa mun ke?. Kaman ko jira take cike da Muryar yara da hauka tace " Bakai ne ba Daddy ,Kullum baƙwa kawoni wuri zuwa school I'm always coming late Dad! One period nake rasa kullum...meye matsalar Maama da Daddy ne?. Murmushi yayi yana dafata kamin yace " lele na azo lafiya bashi ne ba?. Eh to amma nidai yau ya kamata kayi magana Da Vp . A haka a wannan rana sai da Alhaji Yero yakaita sukayi mata da Vice sannan ya samu sukuni...
Chapter 7 · 0% Book details