← Book details Ruhin Fansa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 9 OF 10

Part 2 ,part 2 ,part 2

Ruhin Fansa Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*_________________________________*
Page 41-45


Da fara'arsu suka k'arasa akan milisar da Mama ke zaune,kallonta Shuzna takeyi cike da matuk'ar kewarta,Babu laifi Mama ta k'ara tsufa babu laifi,cikin d'oki Shuzna ta k'arasa gabanta ta duk'a tare da rungumeta ta baya ta sark'o kanta dai dai wuyanta,da sauri Mama ta d'ago fuska a hankali tace"Najma",da yake suna hayaniya babu Wanda yaji me tace sai ita Shuznar,murmushi kawai tayi tace"Mama barka da hutawa".k'ara kura mata ido Mama tayi jin muryar Shuzna sharewa tayi ganin ba fuskarta bace tace"yauwa yarinya"labari sukeyi amma kab hankalin Mama yana kan Shuzna yarda takeyin abubuwa da matsa k'afa yasa take ganin kamar Najma ce zaune a wurin,a b'oye sai share hawaye takeyi.shigowar Amaan yasa Shuzna mik'ewa tsaye tana kallonsa,wani irin zaro ido yayi bakinsa na k'yarma ya d'aga hannu yana nuna Shuzna yace"ke..e..ke...Zee...na...t"da sauri ya dafe kanshi ya fice da gudu yana k'ok'arin sakin ihu yana bubbuga kanshi yana so ya gane ko dai yana da hankali.Daddy suka gaisar sannan suka isa gidansu Islam,anan da taga Shuzn yi tayi kamar bata Santa ba,anan suka had'a kawancen yarda babu Wanda zai zargesu.sosai Hajiya Sadiya ta k'arbeta.ta jima sosai a gidan kafin tayi masu bankwana tace su zauna zataje gida ga Driver dinta nan yazo,tun da suka fita ,Amaan kam baya ya bisu dan yana so ya tabbatar da abunda ya gani,da sauri tasa Driver ya taka burki daidai wani super market,har kusan Faduwa takeyi data fito tayi kan wata kyakyawar mata dake shirin shiga mota hawaye suka wanke fuskarta tace"Ummu,Ummu"juyowa matar tayi ta kalleta kawai ta shiga mota kafin Shuzna tayi wani yunkuri tuni Driver din yaja motar yabar wurin,hawaye suka Kuma zubo mata da k'yar ta k'arasa mota ta shiga,Amaan ko ihu ya saki a cikin motar yace"menene haka yake neman zautar dani?,ni da hannuna na kashe Zeenart ,haka Ummu amma meya sa sukemun gizo a idona?,wannan ba abunda zai tab'a yiwuwa bane"da gudu ya taka mota ganin tasu Shuzna tayi masa nisa har suka iso bakin gate dinsu yaga gidan sannan ya koma gida a matuk'ar rude.
Har yanzu Shuzna hawaye sun kasa tsayawa akan idonta,ga k'afarta da takejin kamar bazata dauketa ba tunda ta shigo parlon tayi wurki da Jakarta hannu tasa ta b'aro glasses din dake wurin ta cusa hannuwanta cikin yalwatacciyar sumar gashin kanta ta zube a wurin.Ahaad shine Wanda ya fara ganinta kafin Nani ta k'araso gareta shi harya iso da sauri ya rike hannunta dake zubar jini yace"subhanallah,meye haka kikeyi,kin jiwa kanki ciwo"."meye yake samunki y'ata?"Nani ta tambaya.kuka Faida ta saka tace"Aunty ki tashi please".rike hannun Ahaad Shuzna tayi tace"naga Mamana,Allah itace na gani,kafin nayi wani abu ta b'ace ta barni"riketa sosai Ahaad yayi ganin yaran sun rud'e yasa ya dauke Shuzna cak ya wuce sama da ita,Nani kuma ta Kama su Faida zuwa d'akinsu.koda ya kaita d'akin gefen bed ya ajiyeta ya dauko first aid box ya soma gyara mata hannun,duk zafin iodine a ciwo ko motsawa Shuzna batayi ba ,kanta k'asa kawai yake kallo idanuwanta sunyi jajawur.kallonta yayi yace"ki kwantar da hankalinki,wannan ba shine mafita ba,kinsan kina da aeki a yau da dare nan,idan kika kuskure kin fad'i daga amincewar da abokan aekina suka baki".ganin yarda yayi maganar a daure ya koma mata tsab oganta a wurin aeki .mik'ewa tayi tare da Sara masa tace"insha Allah General Ahaad".kallonta kawai Muslim keyi Wanda yake tsaye bakin k'ofa,da hanzari ya k'arasa shigowa ya rike hannuwan Shuzna hawaye na silalowa daga fuskarshi yace"Ashe kece Najma k'anwata,Ashe ke jinina ce?".a razane Najma take kallonsa tana son tuno abubuwan da suka faru a baya,bakinta na rawa tace"tabbas kaine Yayana Wanda Mummy ta kashe d'aya kai Allah yasa ka rayu,sai yau na gane dalilin da yasa nake matuk'ar son Daddy Ashe shine Uncle Bashir dinmu,na dade ina ganin kamarsa da Ummuna amma na share hakan,Ashe a cikin Family dina nayi rayuwa,Allah na gode maka".da gudu ta fad'a jikin Muslim tana sakin kuka,Nani ma kukan takeyi had'e da dariya ,matsowa tayi tana shafa fuskarshi tace"munyi kewarka sosai Muslim,ka yafe mana tabbas dani aka had'a kai aka rabaka da mahaifiyarka,amma munyi hakan ne dan ceton rayuwarka"sunkuyar da kai Ahaad yayi yana jin wata matsananciyar kunya ta rufesa da sauri yabar d'akin yana jin wani iri daban saboda halin Mummy.nan Nani ta basu labarin komai,kwafa Shuzna tayi tace"nikam bazan tab'a iya yafewa wad'annan mutanan ba,ko yaushe su suna kawo hari akan farin cikinane".dafata Muslim yayi yace"ko dan Hallaccin da Aiban yayi maki bai isa ace kin gafartawa k'anwarsa da Ummansa ba?,duk da nasan Islam itace ta kawo shawarar a zuba maki Acid Kuma ita ta siyo ta bawa Fadila kuma ita tasa Fadila tasa ayi maki Fyad'e".murmushi Shuzna tayi tace"Kuma Mamanta harda hadin kanta aka yimun allurar mutuwa ko?,Kuma Islam itace wacce ta gayawa Ahaad nice Shuzna bayan daya saka aka kamo masa ita".zaro ido yayi yace"a ina kika San wannan?"."ina tare daku a India amma ruhina yana nan Babu wasu bincikena da ban gama ba,abunda ya rage shine sora d'aukar hukunci".
Da dare ta shirya cikin Uniform dinta na kalan Soji tayi matuk'ar kyau sosai ,sai dai har yanzu idonta akwai alamar ja ja a jiki,sai fidda kamshi takeyi,da gudu Fayyad ya shigo d'akin tare da rungumeta yace"Ummu kije dani bana son Zama anan",k'arasa daure igiyar takalminta tayi tace"haba Super hero ,kasan bazan dad'e ba kuma Ummanku na tare daku,aeki ne na gaggawa yazo mun"ta k'arashe maganar tana janyo hannunsa suka sauko daga bene ,har a ranta tana matuk'ar son Fayyad saboda Shima yarda yake tsananin sonta da nuna kula gareta,a kusa da Nani ta zauna ta rungumota tace"Nani zan tafi"."kai kinyi matuk'ar kyau y'ata,bara muyi photo a tare"wayarta ta d'akko take hotonsu da Shuzna ya bayyana tun bata girma sosai ba,camera ta shiga ta soma daukarsu tare,d'aya ta rungumeta,d'aya ta Mata kiss a kumatu,d'aya Kuma sukayi duka harda yara,mik'ewa tayi ta sumbancesu su duka ta nufi hanyar fita da gudu Fayyad ya k'araso ya rike hannunta Cuo din madara ya bata yace"kinyi mantuwa baki sha madarar ki ba"duk'awa tayi murmushi dauke fuskarta Tasha madaran sannan ta shafa kanshi tace"na gode".kanne Mata ido d'aya yayi tare da sakin murmushi yace"Allah ya tsare,ya Kuma karemun ke Ummina,ki kulamun da kanki,ko yaushe ina alfahari dake,kedin garkuwace ta gari garemu,ko yaushe zaki kasance a zuciyar Fayyad Aiban"sak fuskar Ahaad ya koma mata,duk wani abu nasu yayi kala d'aya,rungume yaron tayi tare da saka masa albarka hannu ya d'aga mata yace"masoyiya am gonna miss u"dariya duka suka saka a parlon,sannan duka yaran sukayi mata Allah ya tsare sannan ta fita daga gidan, Driver yaja motarta zuwa babban barikin soji a katsina,da d'an gudu gudu ta shiga d'akin taron,k'amewa tayi tare da sarawa manyanta irinsu General Ahaad, General Muslim,General Akiyy da dai sauransu duk manyansu sun hallara ,ansa Mata sukayi kafin ta k'arasa jikin wani k'aton allo Wanda Computer ke ajiye a gefansa bisa tebir ta soma masu bayani tiryen tiryen akan yarda akayi aka kwashe kud'in matai Makin shugabansu,sannan ta Kuma fad'a hanyoyin da za'abi a kawar da irin wannan b'annar tasha wahala sosai kafin ta gano Wanda sukayi aekin dan da gani Shima k'warone a computer.
Tafa mata sukayi tare da Mata jinjina dan tabbas sun jiniinawa k'ok'arinta ba kad'an ba,hakan ya k'ara Mata kima a wurin aekinta,gabanta ne yayi mugun fad'uwa da sauri ta soma karanto addu'a ta samu taji daidai sannan taci gaba da godiyar kyaututtukan da take samu.ba su suka Kama hanyar gida ba sai bayan sallar asuba,Muslim yaja Ahaad yace"muje idan an ajiye Captain Shuzna gida sai driver dinta ya mikamu kaga Amaan bai bada motar an kawo ba"ba yarda ya iya haka suka shiga motar sai faman had'e rai yakeyi,yayinda Shuzna keta jan siririn tsaki dasun had'a ido ta b'allah masa harara.murmushi kawai yayi ya kawar da kansa yana Mata akamar zaki gane kuranki.
Daidai k'ofar layin sukaga motar Ahaad fitowa sukayi tun a nan,Ahaad yace"to Kuma waya kawo motar anan?".jinjina kai Muslim yayi yace"nima ina zan sani".ko kulasu Shuzna batayi ba ta wuce tare da tura k'ofar parlon tanajin gabanta yana dukan ukku ukku kamar zuciyarta zata bud'e kirjinta ya fito,ganin duhu yasa ta matsa wurin makunnin kwan fitilar ta kunna,a hankali ta soma juyowa kamar mai tsoron d'akin baya tayi tana jin jiri na neman kwasarta ,murza idonta tayi ganin kamar dishi dishi take gani,lallai ba mafarki bane,wani irin zananniyar k'ara ta saka wacce ta karad'e duka illahirin gida ta Kuma kwala wata k'arar tace"Nani,Fayyad"jin motsin mutum ta bayanta yana niyar shak'areta yasa ta juya da sauri zaro idonta tayi cikin muryar kuka tace"sai kayi dana sani,sai kayi nadamar zuwanka duniya,Amaan ka tabka babban kuskuren k'ara kashemun farin cikina"duka ya kai Mata a fuska ta goce ta kai masa wani duka a wuya,k'ara ya saki ya nemi hanyar fita,yaransa guda biyu suka rufa masa baya,cikin zafin nama ta rufa masu baya ta zare bindigar dake jikin wandonta ta soma harbi ta ko ina ,da gudu Muslim da Ahaad sukayo cikin gidan jin ihun Shuzna,bangajesu Amaan yayi sukayi waje,itama turesu tayi ta rufa masu baya,cikin sa'a ta harbi Amaan a k'afa,sai yaronsa d'aya akan cinya ,kafin ta k'arasa garesu suka shige mota suka ja da gudu.dafe kai Ahaad yayi yana Kiran"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"Nani da Fayyam ne kwance cikin jini anyi masu yankan rago,gaba d'aya parlon ya b'aci da jini,da gudu Ahaad ya k'arasa ya d'ago gawar Fayyam sai yaji hawaye nabin kuncinsa,yau d'ansa ne a hannunsa Kuma wai k'anensa ya masa yankan rago ya kashesa.jin muryar su Ahaad yasa Faida da Fayyam fitowa da sauri,mak'alk'ale Muslim Faida tayi tace"Uncle suka kashesu ,suka yankasu muna kallo,Uncle a idona,wani ne mai Kama da Papa,muma suna nemanmu Fayyam ne ya buga masa katako a kai ya janyeni ya b'oyeni a bayan k'ofa"nuna gawar su Fayyad kawai takeyi a take ta sulale jikin Muslim sumammiya,shikam Fayyam jikin Ahaad ya kwanta ya kasa cewa komai .girgiza Faida Muslim yakeyi amma shiru,ruwan sanyi ya zuba mata amma ko motsawa batayi ba,sai yanzu tunanin Ahaad yazo masa akan Shuzna janye yaran yayi daga jikinsa ya fito da gudu yana kiranta duk da ji yakeyi kansa tamkar zai tsage,Shuzna kam fad'uwa tayi akan gwaiwowinta tana sakin kuka ,da gudu Aiban ya fito daga mota ya k'araso ya rumgumeta yace"kiyi hakuri,kada ki d'auki doka a hannunki,nayi maki alk'arin zanbi hakkin D'ana a ko wanne yanayi".ganin hakan yasa Ahaad sunkuyar da kai ya koma ciki tare da jingina da bango ya dafe kansa.Aiban yanayin tozali da hawar su Nani,besan ya soma hawaye ba.ruwa da yawa Fayyam ya ebo ya watsawa Faida ya girgizata da k'arfi yace"kema tafiya zakiyi ki barni?,ki tashi kada ku barni ni kad'ai ina sanku sosai"ya k'are maganar tare da sakin kuka mai karfi,wani dogon numfashi Faida ta saki itama tana sakin kuka,ba arziki aka Kira Dr yayiwa yaran allurar bacci su duka biyu dan nema sukayi su zare masu.
Cikin awanni kad'an aka gama shirya gawar Nani data Fayyad,Shuzna kam ta koma kurma ko motsi batayi ha daga inda take,har aka fita da gawarsu.ganin Shuhada ta shigo a rude yasa Shuzna sakin kuka ta rungume Shuhada suka saki kuka a tare. Kamar daga sama sukaji magana"yanzu ba lokacin kuka bane,ki Zama jaruma ki share hawayen kije ki gama da makiyanki,ki kawar dasu daga datsewa duk wani bawa farin ciki,ina so yau ki Zama ta k'arshe wacce zasu tarwatsa wa rayuwa Najma"jin muryar Ummu yasa suka juyo da sauri su duka.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.


Jorderh majidadi
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUHIN FANSA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Na
*Maryam ismail Majidadi*
Chapter 9 · 0% Book details