Part 2 ,part 2 ,part 2
Ruhin Fansa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Page 11-15
Shigowar Daddy mijin Aunty Maryam yasa Najma saurin mik'ewa wani irin bugawa k'irjinta yayi da k'arfi ta tsare mutumin da ido,shima ba k'aramar fad'uwa gabansa yayi ba,kallon yadda aka b'ata fuskar yarinyar yakeyi,k'arasowa yayi inda take yace"kefa musulma ce,kiyi hak'uri ki rungumi kaddararki ki zauna kinji ko"ji tayi wani irin nauyin mutumin takeji da ganin girmansa dan haka babu musu ta zauna,tare da sunkuyar da kanta k'asa.d'agowa yayi yace"Dr yanzu meye abunyi game da fuskar nata?"nisawa Dr Naman yayi ya kalli y'an uwan Drs y'an uwansa dake wurin Dr Ishani ne yace"fuskan ya b'aci da yawa bama da wata mafita daya wuce a canza mata fuska"wani irin razana Najma tayi ta d'ago tace"yanzu hazan dawo da kamanni na na asali ba?"gyad'a mata kai yayi alamar eh, innalillahi wa'inna ilaihir raju'un shine abunda take maimaita hawaye na Kuma wanke mata fuska,da sauri Aiban ya shigo d'akin ya Kama hannuwanta yana girgizata ganin tana neman fita hayyacinta sai da yaga tad'an dawo daidai yace"ki kalleni"d'ago idanuwanta tayi ta zuba mashi su,goge mata hawayen fuskarta yayi yace"ki daina wannan kukan,ur d must strongest women I have ever seen,so karki bani kunya,wannan ma wani matakin nasaran ne,ki bari ayi maki aekin nan,cikin kwanaki kad'an zaki warke,ina so kiyi karatu sosai ki dogara da kanki ki haife abunda ke cikin ki,sannan kiyi k'ok'arin had'a kan Family dinki,ki sani ba'a rama cuta da cuta"shiru tayi can tace"to kayimun alk'awari zaka barni na cika mafarkina ina so in zama soja"girgiza kai yayi tare da shafa gefen fuskarta yace"ga iyayena su zama shaida bazan tab'a hanaki cikar burin ki ba".murmushi ta saki tana zancen zuci."to Alhmdllh hakan yayi kyau,ni Kuma na dauki nauyin karatunta da aekin canjin fuskar da za'ayi mata"Daddy ya fad'a.har k'asa Najma ta d'uko tana zubawa Daddy godiya,hannuwa yasa ya d'ago kafadunta yace"kada ki damu,abunda nake so dai karki bani kunya,ki mai da komai ba komai ba kiyi rayuwa kamar kowa,ki dauka mun zama iyayenki karkiyi fargaba a kanmu"har cikin ransa yakejin kaunar yarinyar kallo d'aya da Daddy yayi mata yaji ta gama zama wani b'are na jikinsa,kallon Dr Naman yayi yace"a fara shirya kayan aekin".gyad'a Kai Dr yayi yace"to wanne suna za'a saka mata a rasid'in da takardunta?".kafin kowa yayi magana Najma tace"yarda Kama ya canza dole komai ya canza,ka samun SHUZNA BASHIR"ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa.shafa kanta Daddy yayi yace "na gode kwarai da kara Shuzna,kinga yanzu y'an matana biyu Shuzna da Shuhada"dariya Umti tayi tace "baban y'an biyu kenan.
Duk yarda Nani taso ganin fuskar Najma hanata sukayi sunsan ba k'aramin tashin hankali zata shiga ba,dan haka sai dai suka ce mata za'a canza saboda wani b'are ya toye sosai,Nani tasha kuka marar misaltuwa amma haka dai ta hak'ura ta zubawa sarautar Allah ido.
After 3 days
Sanye aka fito da ita da kayan aeki a jikinta fuskarta lullub'e da bandeji,kwance take a bed tamkar gawa ,turata akayi zuwa d'akin da za'a kwance fuskar,kowa addu'arsa Allah yasa anyi aekin a sa'a.Aiban ne ya fara warware mata fuskar sannan ta mik'e zaune amma idanuwanta a rufe tana tsoron ganin yadda ta koma,Daddy,Umti Nani duka suna wurin,"Alhmdllh ,Masha Allah "abunda duk suka fad'a kenan,sab'anin Nani da taketa faman wangale baki tana dariyar farin ciki ga hawaye na zubo mata na dadi, mirror Aiban ya dauko ya kara mata a gaban fuskarta ,a hankali ta soma bud'e idonta wanda yalwataccen gashi ya k'awatashi duk da yadda ta kaga fuskarta kamar ba'a toyata ba Kuma tabbas fuskar da aka saka mata mai matuk'ar kyau ce,lallai Umti tayi mata zab'i na gari sai dai fatanta kada hakan ya janyo wata matsalar Kuma.hawaye Umti ta fara da sauri tazo ta rungume Najma tace"Shuzna basan iya misalta maki irin farin cikin da nake ciki ba,kece kika dawomun da fuskar yarinya mafi soyuwa a gareni,wanann fuskar dana bada aka saka maki fuskar yarinyar da Yayanku Muslim yaso ne wato Zinatu,a daren daurin aurensu ta rasu,y'ar aminiyata tace ita,garinya mai ladabi da biyayyah da sanin ya kamata ,fatana dai Allah yasa ki daukemu tamkar iyayenki".hannu Shuzna tasa ta gogewa Umti hawayenta tace"insha Allah bazan baku wata matsala ba,ni dinnan y'arku ce,Zan bada dukkanin biyayyata gareku kun taimakeni lokacin da nawa y'an uwan suka gujeni"sosai sukaji dadin bayanin nata ,kallonsu Daddy yayi yace"wannan ya zama sirri a tsakaninmu,kada Wanda yasan asalin yarinyar nan Kuma daga yau sunanta Shuzna ta tashi daga Najma,gobe Shuhada zata dawo ina so ku gabatar mata da Najma a matsayin Shuzna Kuma y'ar uwata,nasan zata dauka Kuma tayi tunanin kamace kawai sukeyi da Zeenatu"sai da suka daukar masa alk'awarin rufe sirrin har Drs din da sukayi aekin Wanda Aunty Maryam na cikin sannan ya k'arb'i magungunanta da ita kanta suka wuce gida.harta takardun makarantarta sun koma Shuzna Bashir dan haka aka fara neman mata scul danta dage ba zata bari ta haihu ba,ga ciki harya soma d'an nunawa a jikinta,saukinta d'aya bata laulayi mai wahala bazaka tab'a gane a lokacin tana da ciki ba.
Girke girke aketayi a gidan fitowar Shuzna kenan daga d'akin da aka bata ta safko kitchen ta nufa ta samu Umti suna aeki tare da masu aeki,sirrinawa tayi tace"Umti barka da safiya,sannu da aeki"murmushi Umti ta sakar mata tace"yauwa y'ata Shuzna sannu da tashi"d'aukar rova da Shuzna tayi yasa Umti k'arb'a tace "a'a y'ata jeki zauna ki huta yanzu jikin naki ya fara nauyi,ae munma gama rigimar Shuhada ne yasa aka yi aekin nan da yawa".jin ihun murnar Shuhada yasa suka gane har Aiban ya dawo daga d'aukota daga airport kenan,Umti kawai take kwalawa kira,ta shigo kitchen din da gudu turus ta tsaya tana kallon Shuzna tace"wow Masha Allah ,Umti ina kika samo mai Kama da Aunty Zeenat?"ta k'arashe maganar tana rungume Umti,dariya Umti tayi tace"y'ar uwar Baffanku ce tazo daga Canada y'ar Auntynku data rasu"hannu Shuhada ta mikawa Shuzna tace"am Shuhada nice to meet u"dan a tinaninta Shuzna batajin hausa ma.fara'a Shuzna ta fad'ad'a duk da sarai ta gane Shuhada amma ta wayence tare da mika hannu itama tace"naji dadin haduwa dake Shuhada,sunana Shuzna "zaro ido Shuhada tayi tace"la ashe kinajin hausa,Allah nayi tunanin bakiji dan wannan kyau ae sai a dauka balarabiya ce ke"dariya duka suka saka sannan ta janyo hannun Shuzna da sauri wai su fita da sauri Umti tace"ke malama kiriniya kiyi a hankali tana da juna biyu"turus Shuhada ta tsaya tace"u mean matar aurece Umti?"."eh amma sun rabu da mijin shiyasa ta dawo zata zauna damu"cike da matuk'ar tausayi Shuhada tace "Allah sarki Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi".da ameen suka ansa sannan suka fito,Shuhada sai zubawa Shuzna labarin garin lagos takeyi,cikin rai Shuzna tace lallai rayuwa wai mahaifata ake bani labari irin haka.kafin kace me har Shuhada ta Kira Muslim ta fad'a masa y'ar uwarsu mai Kama da Aunty Zeenat tazo,shikam bancin aeki yasha kanshi niya yayi ya gudo yazo yaga mai Kama da zeenart dinshi.
Bayan wata hud'u.
A yanzu rayuwa kam ta matuk'ar camzawa Shuzna ga wata irin Shak'uwa da sukayi da Shuhada komai tare sukeyi sun zama kamar y'an biyu,a dole Shuzna ta hak'ura da school saita haihu saboda tun wata biyar cikinta yayi wani irin nauyi ya fara girma sosai ga kumburin k'afa data fara fama dashi,sai dai computer scul da taketa zuwa danta k'ara gogewa kafin ta koma makaranta,Shuhada ma tsaida karatun tayi duk da ita Law take son karanta sai dai ta koma zuwa computer scul din itama.sanye ta fito da doguwar riga batayi wani k'iba ba sai dai jikinta ya canza ga ciki ya fito mata sai dai tayi wani irin haske da kyau,wani irin fad'uwa gabanta yakeyi tunda ta tashi yau,da k'yar take janyo k'afarta harta safko daga stairs da sauri Shuhada ta k'araso tare da riko hannunta tana mata sannu dariya Shuzna tayi tace"sai kace wacce take dauke da wasu uwayen kaya?","ae yanzu kinfi ma koma fama da nauyi,Allah dai ya raba lafiya"ta rikota ta taimaka mata suka zauna a chair d'agowar da zatayi sukayi ido biyu da Ahaad kallan kallo aka shiga yi tsakaninsu,kauda Kai Shuzna tayi tare da tab'e baki wata irin tsantsar tsanar Ahaad takeji a kanta da k'yar take had'a yawu har wani d'aci d'aci takeji a mak'oshinta maganar Shuhada ta dawo da ita daga tunanin data tafi ta d'ago tana kallonsu wannan shine"Yaya Muslim sai wannan Yaya Ahaad ,shima kamar d'an gidan nan yane,duk in sukazo garin nan anan suke zama"gyad'a Kai tayi ganin su Umti sun tsareta da ido yasa tace"sannunku da zuwa ,ina wuni".da "lafiya "kawai Ahaad ya ansa ya wuce ciki abunsa.shikam Muslim zama yayi yana kallonta yana jinjina tsananin Kama tsakaninta da Zeenat ji yayi ciwansa ya zama sabo Amma a haka ya daure ya ansa gaisuwar sannan shima ya wuce ciki.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.
Stylish star
Jorderh majidadi
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUHIN FANSA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Na
*Maryam ismail Majidadi*