← Book details Ruhin Fansa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 10

Part 2 ,part 2 ,part 2

Ruhin Fansa Part 2 Complete Hausa Novel · about 11 min read

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*_________________________________*


End


A kallon Ummu kawai Shuzna takeyi sannan ta fad'a jikinta cikin dishewar murya tace"Ummuna Ashe zan k'ara ganinki?".
Shafa fuskarta Ummu tayi tace"kwarai kuwa y'ata,komai kike ciki ina sani,ina jiran lokaci kawai yayi kafin nazo gareki,saiki godewa Yayanki Kuma Baban yaranki danshi ya dauke maki Ummarki ya kula da ita duk tsawon wannan shekarun yana bata tsaro"sunkuyar da kai Shuzna tayi ta kasa cewa komai,sai dai tana jin dadin yarda Ahaad ya kula da Ummanta duk da Shima tashi ce ita ta rainesa,rasa kalmar da zatayi amfani tayi.matsawa kusa da Ahaad Ummu tayi ta Kama duka hannuwansa ,kansa a k'asa yace"Ummu dan Allah kuyi hakuri,nasan Familyna sun cuta maku da yawa"rufe masa baki Ummu tayi tace"nima Family dina ne ae,kayi hakuri bana nufin Shuzna ta cutar dasu,sai dai ina San a d'auki matakin da irin haka ba zata k'ara faruwa ba".murmushin k'arfin hali yayi cike da kunya amma bece komai ba,shi kanshi tsiyar dasu Amaan suke aekatawa ya ishesu haka.cikin k'an k'anin lokaci ta sauya kayan dake jikinta ta fice daga gidan.
Da matuk'ar gudu ya shiga gidan tsaye yayi turus ganin Daddy yana balbale Mummy da bala'i yace"kinyi abunda kika iya,amma ki sani bazanyi maki baki ba,sai dai yau iyalan y'an uwana zasu dawo gida,kin cutar dani Bilkisu,bansan iya wanne abubuwa kika saka na aekata ba,bazan tab'a yafewa kaina ba"ya k'are maganar yana fita daga parlon.
Hannu Mummy ta saka a Kai tace"Amaan aekin komai ya bud'e,mun shiga ukku idan Alhaji ya juya mana baya".
K'arasowa yayi cikin d'akin yace"ae wannan bakiga komai ba akan abunda ke dosomu,Ummu Sha'awa tana raye Ashe Yaya Ahaad shine Wanda ya dauke Ummu,Shuzna k'awar Fadila Kuma itace Najma"dafe zuciya Mummy tayi tace"Amaan karkasa zuciyana ta buga,na mutu ka huta".sallamar Hajiya Sadiya da Islam ya mai da hankalinsu garesu,fuska daure Hajiya Sadiya ta shigo a hassale ta nuna Mummy tace"Ashe ke baki da mutunci?,yanzu mijin nawa kike tunanin zaki iya sakawa a ture daga Gwamnati?,to wlh kinyi kad'an ke baki kaiba,duk wani abunki bayana kika biyo"."Kai Kai Wai meye kukeyi haka ?,yanzu ya kamata mu nemi mafitar tsiratar da kanmu ne,duk abunda muka dade muna shiryawa zai rushe rana d'aya".murgud'a baki Islam tayi ta soma zagaye Amaan cikin d'aga murya tace"naku dai ya tarwatse maciya amana,koka manta yanzu Kai kaje ka kwanto wata rigimar?,Kaine kaiwa yaran Najma yankan rago,ka kuma kashe Mata Naninta ,bayan a baya kayiwa y'ar uwarta Fyad'e ka kasheta,Kuma ka kashe Mata Babanta,kayi hari akan Ummanta sai dai ita bata mutuba,Zeenart kam daka kashe ta mutu sai dai fuskarta aka bawa mak'iyiyarka,Kuma Najma tasan komai akan abunda ka aekatawa zeenart,abun farin ciki da zan gaya maku shine Muslim shine yaron Umma da Kuka kashe Mata y'an biyu to D'an uwanta Bashir yaji komai Kuma shiya dauke Muslim ya renesa,yana nan zuwa gareku".Mari Fadila ta katsawa Islam tace "ke marar mutunci yanzu Iyayen nawa kike gayawa haka?,ae duk abunda ake k'ullawa da Uwarki Sadiya aka yishi,hasalima itace mai kawo shawara,banzaye masu bak'ar zuciya kawai"shak'e Fadila Islam tayi tana kiran"ke harkin isa?,wallahi ko uwarki Bilki bata kaini tasha ba balle ke tsohuwar guzuma jaka dake".jin an banko k'ofa da k'arfi yasa suka juyo da sauri,Shuzna ce cikin shigar Uniform dinta na soji,sai yaranta su hudu suma duk a shigar Uniform.ko wannensu rike da bindiga k'arasa shigowa tayi cikin d'akin tana kallonsu da tsantsar tsana tabbas wa'annan mutanan sun cuta mata da yawa bata ma san meye zata iya aekatawa akansu ba inhar ta biyewa zuciyarta.jin an fasa k'ara yasa suka juyo da sauri ganin Fadila na niyar faduwa yasa Shuzna ta k'arasa da sauri ta fad'o a hannunta Islam ce ta caka mata wuk'a a gefen cikinta,girgizata Shuzna keyi tace"Fadila ki tashi" hannu Mummy ta daura saman Kai tace"wallahi yau saina kasheki kema,baza'a tab'a d'aukar gawar y'ata ita kad'ai ba,hakan bazai tab'a yiwuwa ba"kan Islam tayi gadan gadan Hajiya Sadiya ma tayi kanta nan suka had'e kamar mahaukata suna kokuwa da juna,fizgo hannun Islam Amaan yayi ya wanke ta da maruka har hudu ya soma jibgarta,da sauri yaran Shuzna sukayi kansu,hannu ta d'aga masu tace"stay out of this"Shima k'ok'arin jaka masa wuk'ar takeyi tana zage zage,ganin da gaske shima zata illatashi cikin bak'ar zuciya ya saita bindigar dake hannunsa akan Islam ya danna kunamar ,wata irin ihu Hajiya Sadiya ta saki tayo kan Islam ,Islam ta fad'o a saman hannunta ga jini yana zubowa daga kanta,ko shurawa batayi ba ta mutu a wurin.innalillahi wa'inna ilaihir raju'un kalmar da Hajiya Sadiya ke maimaitawa kawai kenan hawaye na wanke fuskarta yaranta biyu Islam da Aiban Kuma kowa yasan Islam itace rayuwarta yau ga gawar Islam a gabanta ,wani kukan ta kuma rushewa dashi,k'ara kad'an Shuzna ta saki lokacin da Amaan ya janyo yalwataccen gashin kanta take ribom din ya zare gashin ya watsu a fuskarta da bayanta,saurin sakin Fadila tayi ta mik'e ta samu ta kwace kanta tace"kada ka kuskura k'azamin hannunka ya k'ara tab'ani".dariya ya fashe dashi yace"Babu Wanda zaiyi rai a nan daga Ni sai Mummyna Babu wani sarki sai ni a wurin nan"halbi ya soma saki kota ko ina cikin zarin nama Shuzna ta goce ta koma bayansa,rike hannun da keda bindigar tayi suka soma kokowa ,yayi mamakin yarda Shuzna tayi k'arfi haka duk da yasan ko a da can tana da k'arfi ba ragguwa bace amma beyi tunanin a yanzu zai kasa kwace hannunsa gareta ba,a tsawace yace"ki sakeni ko kuwa kiyi ta ranki"Murmushi Shuzna tayi ta kallesa ido a ido tace"aeni Amaan tun daga ranar daka rabani da iyayena,yar uwata,D'ana da Kuma Nanina from that very day u took my life,shiyasa yanzu bana tsoron na mutu,amma sai naga bayan tantiri marar tsoran Allah irinka,saina tabbatar nice ta k'arshe da zaku lalatawa rayuwa a duniya gaba d'aya".murd'eta yayi ta dur'usa k'asa,cikin dabara ta samu ta d'ago ta zare hannunta daga jikinshi ta wanka masa maruka har biyu ta kuma ingijesa yayi baya,juyawa tayi zata dauki waya ta Kira y'an sanda ,cikin sand'a ya daura Mata bindiga a Kai yace"tabbas yau saikin mutu,haka sauran yaranki da tsohon mijinki da Uwarki sai sun mutu kinga duk abunda kika mallaka nawa ne"motocin y'an sanda dana soji ne suka shigo gidan,kafin kace me sun zagaye gidan ,daga ciki harda General Muslim da General Ahaad,sai shugaban Shuzna kuma Wanda take jagorancin team dinsa a yanzu haka,parlon suka shigo harda Aiban,"ku tsaya daga nan idan Kuma har kukayi wani abu marar kyau to tabbas zata mutu yanzu",ganin da gaske yake yasa suka ja baya,kallonsu General Asam yace"dole fa yanzu ayi zab'i na k'arshe ,sai an harbi Amaan"zaro ido Aiban yayi da sauri ya k'arasa wurin Mamanshi tare da riketa jikinsa ta fad'a ta saki kuka tace"Aiban ya kashe mani ita,ya kashe mani Islam,Islam ta tafi ta barni Aiban"juyar da fuska yayi yana share guntun hawayen dake zubo masa rungumeta yayi yace"Hajiya kiyi hakuri,hakan Allah ya rubuta".kamar daga sama sukaji k'arar halbi Wanda basu gani ba harsunyi saranda kowa daukarsa Shuzna ya harba,ganin Ahaad da bindiga a hannu yasa kowa ya kalli inda yake Kallo,k'ara Amaan ya saki ya dafe k'afarsa da Ahaad ya harba ya zube anan wurin,wani kukan Mummy ta Kuma saki tace"Ahaad karka kashe d'an uwanka,dan Allah kabarmun yarona Ahaad"ta wuce gabansa zata duk'a,da sauri ya riketa ya kawar da kansa gefe"daku kamani gara na kashe kaina,bazan tab'a bari na mutu a hannunku ba"kanshi ya saita Mama tana kiran"a'a Amaan karkamun haka".kallonta yayi hawaye na zubowa daga idonsa yace"ki yafemun Mummyna"kafin tayi magana ya harbe kansa a take ya mutu a wurin ko shurawa beyi ba.y'an sanda suka kwashe su sai office dinsu Fadila kam a sume aka kwasheta sai asibiti,har Dr Jamil an kamo tare aka rufesu a office din y'an sanda.duk abunda sukeyi Daddy yana jinsu daga part dinshi be fitoba ,ya rasa meke masa dadi,kwakwaran motsi baya iyayi.cikin sati d'aya aka shirya komai aka Kai ,Mummy ,Hajiya Sadiya da Dr Jamil kotu,Shuhada da barista Abbas sune suka tsayawa Shuzna,ba wani b'ata lokaci suka ansa laifukansu,kotu ta yankewa Mummy da Hajiya Sadiya zaman gidan yari na shekara biyar da tarar dubu d'ari bibiyu,sannan su mayarwa Najma da dukiyarta.Fadila kam Shuzna bata yarda an kaita kotu ba,yarda taga tanata faman kuka da rokon Shuzna gafara ,ga tausayina Nasirah da Shuzna keji yarinyar bata da damuwa,tun kafin ayi wannan rigimar dama aka dauke Mama da Nasirah aka had'asu dasu Ummu dasu Faida.cikin sati biyu aka sallami Fadila suka dawo gidan Shuzna,ga Umti da Daddy Bashir sunzo Family ya hadu sai tattauna sukeyi da sanin abubuwan da suka faru a da.da gudu Shuzna ta shigo rike da wasu takardu ."a'a har yanzu kina nan da wannan shiriritar taki ?"Ummu ta tambaya, murmushi Shuzna tayi ta rungume Mama tace"Hajiya Mama yau jikarki ta koma da sunanta Najma Jafar Bindawa,Komai nawa ya koma da sunansa na da".Alhmdllh Umti ta fad'a ta dafa kafadar Shuzna tace"y'ata Najma kiyi hakuri da rasa fuskarki"rungume Umti Najma tayi tace"ba komai Mamana".tureta Muslim yayi yace"dallah malama tashi anan,zaki karyamun Mama".rigiman hakan suka fara Ummu ta janyoshi tace"barsu suje Sojana ae nima ga y'ata nan"ta fad'a tana janyo Shuhada jikinta ta had'asu ta rungumeta,hannuwansu ta had'a wuri d'aya tace"nima ga ma'auratana na had'a,zanyiwa Muslim da Shuhada aure"kowa dariya ya saka ,Shuhada ta boye fuskarta jikin Ummu,janyo hannunta yayi yace"haba masoyiya kunyata kikeji ne?".dungure masa Kai Mama tayi tace"gaba d'aya baku da kunya Kai da wancan labcecen bayahuden"harara Ahaad ya maka Mata wanda tunda ya zauna saika dauka baya d'akin.shigowar Aiban d'akin yasa suka takaita dariyar sai da ya gaishe da kowa sannan ya zauna kusa da Mama,"kaga yaron kirki mai tarbiya ,sannu da zuwa Aibanu".danna k'afar Mama ya farayi sannan yace"Mamana nazo neman aure fa"."yi sauri gayamun wace mai sa'ar ce?,gaskiya na gaji da zamanku hakanan dama".sunkuyar da kansa yayi alamar kunya sannan ya rad'a Mata a kunne,"Alhmdllh,Alhmdllh,Allah na gode maka,Aiban Allah yayi maka albarka Kuma na maka alk'arin baka abunda kake so Koda hakan zai Zama abu na k'arshe da zanyi,Allah ya shiga lamuranka,na baka Najma duniya da lahira".wani irin bugawa da k'arfi zuciyar Ahaad yayi ,"toshi Papa waye zaku bashi ya aura?"Fayyam ya tambaya."baba ko ubanwa,aeshi wannan fad'in ran nashi bazai barshi yayi aure ba".turo baki Fayyam yayi yaja hannun Nasirah yace"sai kiyi dama ae halinkine"tunda Nasirah ta dawo gidan Fayyam yake kula da ita,baya yarda kowa ya tab'a ko da wasa,"tsohon marar kunya Wanda yayi gadon ubanshi".
Bayan sati biyu
Ko wanne b'angare Shirin biki sukeyi ba k'akkautawa, yayin da Ahaad tun ciwo yana cinsa a tsaye har yakai gaya kwantar dashi ko fita bayayi kullun yana kwance kawai.ko kad'an Mama ta hana kowa ya kulashi tace a barshi can shiya sani.
Kaya Muslim ya ajiye masa yace"ka tashi ka shirya mu tafi,lokaci yana kurewa".Jan pillow yayi ya rufe fuska cikin dishewar murya yace"kuje kawai bazan iya fita ba".sai da Ummu tayi da gaske sannan Ahaad ya shirya cikin blue din shadda suka saka mai matuk'ar tsada sai black din huda da black din takalmi sai fitar da sihirtaccen kamshi sukeyi.haka suka tafi daurin auren.wuri ya cika makil da mutane na nesa dana kusa,baka iya banbance wurinwa wane yazo,dafe Kai Ahaad yayi da yaji yana barazanar tarwatsewa juyawa yayi yaga babu mai kallonshi ya samu ya fito daga cikin masallacin can baya ya koma ya zauna tare da had'e Kai da gwaiwa yana jin jiri,jin hawaye masu dumi yayi suna bin fuskarsa..kamar daga sama yaji ana cewa an daura auren Muslim da Shuhada,Aiban da Fadila sai Ahaad da Najma akan sadaki naira dubu d'ari.a firgice ya d'ago yana jin tabbas mai shelar nan bejiwa kunnensa daidai ba.murmushi Aiban yayi masa lokacin da suka had'a ido yazo ya kamashi ya d'auki babbar rigarsa daya cukurkude ya ajiye a k'asa"ace ango ya b'ata kwalliyarsa haka?,kakkabe rigar yayi ya saka masa ya Kama hannuwansa yace"Congratulations angon Najma Allah ya bada zaman lafiya".tangare k'eyarsa Muslim yayi yace"raggon maza,ashe kasan kana Santa ka saketa"kasa furta komai Ahaad yayi sai murmushi kawai da godewa Allah da yakeyi a ranshi,"kada ka damu,ni bazan raba zuciya biyu ba,ina tabbatar maka itama Najma tana sanka ".Jan hannunsa sukayi zuwa cikin mutane fara'a kawai yakeyi yana gaisawa da mutane haka har suka samu damar komawa gida bayan hotunan da suka sha sunyi kyau kamar y'an ukku.koda suka shiga gidan an tsara wurin sosai anayin y'ar dinner,kujerune ukku inda su Najma suka zauna komai nasu iri d'aya fuskarsu a rufe sunyi masifar kyau.rike hannun Ahaad Umti tayi tace"yarona muje ka fara zab'ar matarka a can"binta kawai yayi a wurin ta tsakiya ya tsaya inda Shuhada take kenan,har zai budeta Kuma ya fasa ya tsaya yana k'are masu Kallo su duk'a,matsawa yayi can hannun dama sannan yasa hannu ya yaye lullubin take fuskar Najma ta bud'e Tasha kwalli,ihu mutanan wurin suka dauka tare da tabi ana masu ruwan nera da turare,sosai abun ya k'ayatar.
5years later.
Yarinya kyakyawa ke gudu ta fad'a jikin Ahaad tace Daddy "kacewa Ammi ta kyaleni ni bazan koma gida ba"Farna ta fad'a tana fad'awa jikin Aiban,dariya Ahaad yayi yace"Captain kibar yarinyar nan wurin Babanta,bazata bimu bafa"dariya sukayi Najma tace to"nima zan tafi da little Najma kuwa"ihu Farna ta saka ita bazata yarda ba,fuska Fayyam ya yatsina yace"u idiot keep queit mai bakin parrot kawai"ba musu ta hadiye ihun da takeyi tasan yanzu sai tasha dukan tsiya..
A yanzu Fadila yaranta biyu Little Najma da Mahamud,sai Nasirah da take wurinta, Shuhada kuwa ukku dan Muslim yace saiya ta taddosu yara,Islam itace babba sai Afnan sannan Salim shine auta,Najma kam Faida da Fayyam sai Farna kawai data k'ara.sosai suke kaunar junansu suna zaman lafiya komai ya koma lafiya suna sada zumunci,a cikin satinne Kuma aka saki Hajiya Sadiya da Mama,shikam Jamil shekara Goma zaiyi dan haka yanzu yayi rabi,sosai Mama da Hajiya Sadiya suka canza zaman lafiya sukeyi suna Kuma San jikokinsu da iyakansu gaba d'aya suma ko wacce ta koma d'akin mijinta,Ummu ce kawai taki yarda ta sake aure take zauna da tsohuwa Mama Wanda tsufa ya fara kamata.
Fadin irin soyayyar da Najma da Ahaad sukewa junansu b'ata lokacine yanzu kam Babu abunda ke rabasu zaman lafiya sukeyi da nunawa juna matuk'ar soyayyah.
*alhmdllh, Alhmdllh,Allah na gode maka daka bani ikon kammala k'arshen littafin nan,Allah ka yafe mana kurakuren dake ciki,Allah kasa kuma a amfana da abunda ke cikinsa*


*Sakon godiyata ga masoya Ruhin Fansa,na gode kwarai da nuna kauna a agareni,sanso fisabilillah,wannan littafi sadaukar ne ga masoya labarin Ruhin Fansa*


Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.
Stylish star
Jorderh majidadi
Chapter 10 · 0% Book details