← Book details Ruhin Fansa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 10

Part 2 ,part 2 ,part 2

Ruhin Fansa Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*_________________________________*
Ga mai neman bayani akan sabon book dina*DIKKO AHMAD* mai fita gobe ya tuntubi 07033636337


Birnin India


Jirginsu ya sauka a garin Mumbai ,juye juye yakeyi yaga ta ina zai hango Umti motar asibiti ta k'araso lokacin da ake fitowa da bed din da Najma take kwance tamkar gawa,can ya hango Dr Naman da Umti,murmushi Umti ta sakar masa sannan sukayo inda yake,rungumeta yayi tare da sakin ajiyar zuciya cikin muryar dake son sakin kuka yace"Umti kinga yarda suka mayarmun da ita ko?"bubbuga bayansa tayi tace"ni dai Aiban dina jarumi ne,dan Allah ya daure komai zaiyi daidai insha Allah"(Umti itace Aunty Maryam k'anwar Aunty Sadiya ,Kuma mahaifiya ga Shuhada da Muslim).risinawa yayi tare da gaishe da Dr Naman shima murmushi yayi sanann ya rungumo Aiban zuwa jikinshi,Umti gaisawa sukayi da Nani ta Kuma jajanta mata,tun a nan Nani ta gazgata tsananin kirkin Aunty Maryam,mota suka shiga tare dabin bayan motar asibitin ,kai tsaye asibitin Dr Naman aka kaita Wanda suke had'in gwaine da Aunty Maryam,d'aki na musamman aka kai Najma cikinsa duk injina da na'urori na gwaje gwaje.office din Umti aka kai Nani ,sannan su Kuma suka duk'ufa akan Najma da take k'afa d'aya duniya d'aya lahira,sosai manya manyan likitoci suka duk'ufa a kanta dan ceto ranta,ajiyar zuciya Umti ta sauke tace"Alhmdllh,nasara ta farko da muka samu shine allurar ko kad'an bata tab'a cikin dake jikinta ba"gyad'a kai kawai Aiban yayi yace "Umti what about her?",dafa kafad'arsa wani baturen Dr yayi yace "soon komai zaiyi daidai"wannan maganar da sukeyi duk a harshen turanci ne.wata allura Dr Naman yayi mata suka tsaya jiran tsammani tare da mak'ala mata wata na'u'ra mai danjoji,addu'a Aiban ya somayi yana a matuk'ar tsorace dan wannan ne lokaci na k'arshe in bata farka ba sai dai ayi hak'uri da ita.ganin danjar jikin na'u'rar zata kawo yayi saurin rintse idonsa ya rike Umti sosai yana karanto duk addu'ar da tazo ransa dan nesan wacce kala ce zata kawo ba,dit dit haka na'u'rar ke k'ara tare da halba tsanwar danja,"Alhmdllh ya Allah,Alhmdllh"abunda Umti ta fad'a kenan,godews Allah Aiban yaci gaba dayi cikin tsananin farin ciki da jin dad'i,ganin Najma ta farfad'o har k'afarta na motsawa.sosai Drs din sukaji dadin nasarar da suka samu,kula ta musamman suka bata sannan aka saka Nurses kula da ita office din Dr Naman sukaje hannu ya bawa Aiban yace"congratulations,na tayaka murnar dawowar y'ar uwarka,insha Allah nan da kwana biyu za'a iya bud'e mata fuska Kuma allurar barcin da aka mata zata saketa,sanann Kuma sai muga wacce hanya zamu b'ullowa fuskar tata"godiya sosai Aiban yayi sanann yayi transfer din kudin da ake buk'ata na aekin yau dan yacewa Umti baya son komai a kyauta ayi mashi kamar kowa.Nani da taji labarin tashin Najma saida ta taka rawar murna,taita zubawa Drs din godiya ,ansha daga da ita sannan aka jata zuwa gida.
Tun daga waje Nani ke kallon gidan dukda ba yau bane rana ta farko da ta fara fita waje ba da Kuma zuwa gidaje irin wa'annan,amma ta jinjina kyawu da tsari na gidan,babban gida ne sosai komai a tsare yake kwanin ban sha'awa ko ina ga filawoyi suna kad'awa.tunda suka shiga takebin wani makeken pic da kallo a parlon na wani Dattijo mai tsananin kyau,amma sam ta rasa ina ta tab'a ganin wannan fuskar sai kawai ta share ta wuce d'akin da masu aekin suka nuna mata,wanka ta shiga lokacin da ta fito har an jera mata abinci a madaidaicin table na d'akinta dan haka taci ta kwanta danta d'an huta.
Har k'asa Aiban ya d'uka tare da gaishe da Abba,cikin sakin fuska Abba ya ansa yace"watanni da yawa malan Muhammad,sai yau har nayi cigiya na gaji"sunkuyar da kai Aiban yayi yace"Abba ayyukane keyin yawa"."to Allah ya taimaka,naji abunda ya faru Allah ya bata lafiya ya kuma tsare gaba,jibi zanje na dubata insha Allah"Abba ya fad'a,godiya sosai Aiban yayi masa sannan ya wuce d'akinsa ya shirya ya koma asibitin,haka Aiban yaketa d'awainiya da Najma ba dare babu rana ko yaushe yana hanyar asibiti da Kuma kashe mata kud'ad'e.
3days later
A hankali Dr Naman yake warware bandage din dake rufe da fuskarta,yayinda take zaune ko hadiye miyau ta kasayi sai fargaba da tsoro,Aiban kam kasa shigowa d'akin yayi,zaro ido Umti tayi tare dayin baya tasa hannu ta rufe bakinta,a hankali Najma ta d'aga idanuwanta Wanda suka zama kalar ja,ta kalli mirror din dake gefenta k'arami,zaro ido tayi tasa hannu a hankali ta shafi gefen hagun fuskarta,wata irin razana tayi ta fasa wata irin razananniyar k'ara ta zube k'asa akan gwaiwowinta,ta fitar da sautin kuka mecin rai.
Wani irin zabura Ahaad yayi amma ya kasa furta komai,zuciyarsa sai ambaton sunan Najma takeyi amma saboda tsabar mishkilanci ya kasa furta koda kalma d'aya.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"shine kawai abunda Najma ke maimaitawa tana sake hararo yarda taga fuskarta gaba d'aya rabin fuskarta ya toye ya jagule ya lalace ta tashi daga Najmarta kyakyawar budurwa,hawayene suka soma zarya a kuncinta,daga Window Aiban yana hangen komai beyi aune ba saijin siraran hawaye nabin fuskarshi yaji.


Stylish star
Jorderh majidadi


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUHIN FANSA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Na
*Maryam ismail Majidadi*
Chapter 2 · 0% Book details