← Book details Ruhin Fansa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 7 OF 10

Part 2 ,part 2 ,part 2

Ruhin Fansa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*_________________________________*


Page 31-35


Tafiya takeyi cikin nutsuwa sanye take da uniform na kakin soji tayi matuk'ar kyau a cikinsu,gashin kanta a nannade ta rike cap din a hannu ba zaka tab'a cewa wai Shuzna tayi aure ba ,bare Kuma kace ta haihi su Faida,babban wurin taron ta doso da d'an gudu gudunta ta shigo wurin tabi layi cikin sabbin ma'ae katan da aka dauka sannan ta sanya hular dake hannunta tayi,kamar yarda aka tsara taron yayi kyau sosai kuma anyi jawabai,manyan sojoji aka gabatar ciki harda Ahaad Wanda yanzu yake rik'e matsayin General Muslim ma haka,lokacin da aka gabatar da Shuzna a matsayin Captain ta gidan soji wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta,ta d'aga kanta sama tayi magana a hankali tace"Allah na gode maka,Ina nan zuwa gareku iyalan Kabir Bindawa,wasan yanzu aka fara",tana fitowa daga wurin Nani ta rungume tace"y'ata Allah yayi albarka,wannan ma wani matakin nasara ne a rayuwarki,na tayaki murna sosai y'ata"haka y'an gidan suka koma gida cike da farin ciki ga Shuhada ta zama cikakkiyar lawyer itama ta cika burin nata.
"Ki tashi,ba lokacin baccinki bane wannan,lokaci yayi da zaki cika alk'awarin da kikawa Ruhina ,ki tashi Najma ,ki tashi". firgigit Shuzna ta farka daga baccin da ya d'an dauketa bakinta dauke da addu'ar bacci,duk lokacin data kwanta bacci takanyi mafar amma na yau ya banbanta da ko yaushe,lallai Najwa tana tunanin kamar ta manta da burin d'aukar Fansa dake cikin ranta Wanda ko yaushe yake cin Ruhin ta,"a'a Shuzna lafiya dai ko?"Umti ta fad'a tana kallon yarda Shuzna ta jik'e da zufa,da gudu Fayyad ya k'araso ya rumgumeta cikin kwarancinsa yace"Aunty kice ya daina",Fayyam ne ya rugo wurin shima yana cewa"bani abuna"b'oye abun wasan Fayyad yayi,kallonsa Shuzna tayi tace"my boy kaga Yayanka ne Fayyad ,ka daina binsa haka da gudu sai kunje kun fad'i?".tsalle Fayyam ya daka tare da kwala ihu ya fad'i akan tayil yana kururuwa,wata zuciya tazowa Shuzna ta fizgoshi ta dalla masa mari tare da sakar masa dundu.bai fasa abunda yakeyi ba,cikin Sauri Ahaad ya safko daga bene yace"karki k'ara dukanshi haka,yaron zaki wa duka kamar kina filin daga?,ke waye ya dakeki?". murgud'a baki Shuzna tayi cikin zuciya tace"shi yaro ba'a da ikon masa magana?,Babu abunda ya ajiye sai dukan y'an uwansa,nan jiya sai da ya fashewa Faida goshi yanzu kuma ya biyo Fayyad wallahi bazan dauki wannan iskancin nashi ba"ta d'auki Fayyad tayi wucewarta,k'wafa Ahaad yayi ya d'auki Fayyam yayi ciki dashi.
"Bazai yiwuba Muslim,wannan ba abunda zan iya yarda dashi bane,kayi hakuri bawa Shuzna fuskar Zeenart ba shi yake nuna kazo kace kana sonta ba Kuma,Shuzna tana da miji Kuma gidan uban y'ay'anta zata koma da yardar Allah"Umti ta fad'a.
Dafe kai Muslim yayi yace"Umti kada kiyi mun haka dan Allah,na tsaya tsawan shekaru ina kallonta kamar Zeenat na bari ta haihu ne kafin na bayyana mata soyayyata,Umti ki taimaki d'anki Wanda tsawan Shekara 5 kenan aka kashe masa masoyiya ya shiga tashin hankali har yanzu ya kasa samun wacce zata maye gurbinta".d'aga masa hannu Umti tayi tace"ya isa haka Muslim bawai bana tausayinka bane ko wani abu ba a'a ,kasan zanfi kowa san ganin farin cikinka,amma kaddara bata zo da Shuzna gidan nan danka aureta ba,na gama magana Kuma kada in k'ara jin kayi maganar da wani".duk'ar da kansa yayi cikin ladabi yace"to Umti insha Allah zanyi kamar yarda kike so,amma ki sani babu ranar da zan iya yin aure ko naga wata da kaina nace ina santa".yana gama fad'an haka ya tashi ya fice daga wurin.tashi Umti tayi ta wuce d'akin Shuzna samunta tayi kwance tayi rubda ciki ,jin an bud'e kofa yasa Shuzna juyowa ganin Umti yasa ta tashi tace"a'a Umti aeda kin aeko sai nazo basai kin taso da kanki ba"kallon Faida tayi yarinyar kyakyawar gaske gata fara tas tace"kije wurin Ummanku(Nani)Ina zuwa kinji".da gudu Faida ta gice daga d'akin.gefan gado Umti ta zauna tace"Shuzna yau zan sauke alk'awarin dana dauka kanki,kinga komawarki nan Nigeria ina tsoronsa sai dai babu yarda zanyi tunda aeki ya kaiki can(zataje yin wani aeki Nigeria),Kuma ko ba aeki nasan tabbas zaki koma gida,wannan fuskar dana baki Wanda nasan kinsan fuskar Zeenart ne y'ar aminiyata,Kuma itace wacce D'ana Muslim zai aura,wannan fuskar bata cancanta a badata ga kowa ba,saboda ba kalar kowa bace,lokacin da aka kawoki,duk da kina a sume amma naga idanuwanki suna fitar da hawaye,naga kina da San k'ara rayuwa,baki da wani muradi daya wuce wannan,shine dalilin da yasa na dage wajen neman mafita a kanki cikin yardar Allah kuma muka samu nasara,Ina so ki sani Zeenart kasheta akayi ba mutuwa tayi ba,yankan rago akayi mata saboda sanin wani sirri da tayi,zan gaya maki Wanda yayi mata haka,amma ko da wasa kiyi mun alk'awarin bazaki tab'a fad'awa kowa ba".jinjina Kai Shuzna tayi tace"Umti basai kin rok'eni ba,zan iyayin komai a kanki". murmushi Umti tayi taci gaba da cewa"Amaan shine Wanda ya kashe Zeenart"a matuk'ar firgice Shuzna ta kalli Umti baki na rawa tace"dama ya santa ne?"."dalilin mutuwarta ne yasa ta gitta a rayuwarsa,tabbas zaki fuskanci k'alubalan da yawa daga wurin Amaan,amma insha Allah zaki tsallake Kuma duk wani sirrin da yasa ya kasheta Zeenart ta gama bayyanamun komai insha Allah idan lokaci yayi zan baki,ke dai ki kula da kanki".Umti bata jira cewarta ba tayi waje abunta.jujuya Kai Shuzna takeyi a tsawace yace"Wai kai wanne irin mutunne Amaan?,tabbas ka kasance azzalumi mai rusa farin cikin kowa,tabbas ka shirya ina zuwa gareka,ba Kuma zan tab'a tunanin kai D'an uwana bane".wayarta data soma ruri ta dauka ganin Barista Abbas yasa ta dauka da sauri tace"Ina zuwa yanzu"kashe wayar tayi bata jira komai ba tayo waje kawai,masu tsaronta suka taso tare da bud'e mata mota ta shiga ,kamar kullun da mota biyu suka fita .ba wani nisan tafiya sukayi ba ta k'arasa inda zasu had'u da Barista Abbas zama tayi a d'ayar kujerar dake kusa dashi tace"barka da zuwa Barista, harka huta daka fito haka da wuri?". murmushi yayi yace"ae dole nayi abunda ya kawoni k'asarnan,balle Kuma aeki daku manya ranki ya dade,nasan zaki shiga rud'ani dajin abunda zan fad'a maki amma karki wani damu kaddara ne yazo da haka,Fadila itace wacce tayi niyar sakawa ayi maki Fyad'e a Kuma ranar da Dr Jamil yayi maki wannan allurar,ta ajiye lemu a firij dinki shine Ahaad ya taka sawun b'arawo ko ince Allah yana sanki ya kub'utar dake daga tarkon Fadila,Ahaad yasha lemun da Fadila ta ajiyene kuma shine Wanda yayi maki Fyad'e a wancan lokacin a tak'aice dai shine uban y'ay'anki".jefar da glass Cup din hannunta tayi a matuk'ar razane ta mik'e tace"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,ni ,ni Shuzna Ahaad shine Wanda yamun wannan abun?"take kalamansa da yake kiranta da Dabba,mazinaciya,dak'ik'iya suka soma dawo mata radau a kunne kamar yanzu yake fad'a mata haka,ihu ta saki Allah ya taimaka wurin rufe yake da glass Babu Wanda zai iyajin sautin muryarta,hannu tasa ta dod'e kunnuwanta tace"a'a,a'a hakan Sam bazai yiwuba,na tsane shi,na tsane shi,meyasa duk wani farin cikina Ahalina suke k'ok'arin rabani dashi".dafata Aiban yayi yace"meye haka kikeyi?sai kace wata warda aka fad'awa mutuwa?meye da Ahaad din?Wanda yanzu zaki godewa Allah kin haifi yaranki da aurene,ba shegu bane da ubansu".lokaci d'aya fuskarta tayi jawur harda k'asan idonta had'e fuska tayi kamar an saukar mata da mutu ta kalli Aiban da idanuwanta Wanda suka firfito waje alamun tsananin b'acin rai cikin kausashiyar murya tace"na tsane shi,na tsane shi,har abada bazan tab'a sassautawa wani daga cikinsu ba,sun tarwatsamun rayuwata"."duka abunda aka yi maki ke shaidace Babu saka hannun Ahaad a ciki,wannan ma kaddara ce kawai,Ina so ki sani zafin kiyayyah baya canza komai Shuzna"."haka zalika bazan tab'a bari suyi nasa a kaina ba wannan karon,yanzu ne zan fuskancesu,meye amfanin rayuwa idan har za'a rayu babu martaba?,zalinci kawai suka saka gaba,suyi farin ciki yau Baba Kabir ya zama Governor a garin katsina ,dan zuwa gobe tunaninsu zai hargitse ne gaba d'aya"files din da Barista Abbas ya ajiye mata ta dauka ta fice daga wurin suka bita da ido.
Tunda ta shiga mota take kuka harta k'arasa gida,goge fuskarta tayi ta fito cikin izza tana tafiya shan gabanta yayi yace"Najma daga Ina kike?".a hassale tace"daga inda ka aekeni malan".sosai ran Ahaad ya b'aci da ansar data bashi ya daure fuska ya nunata da hannu"yake ki kiyayeni,niba tsaranki bane da zakina fad'amun duk abunda yazo bakinki,sake maki da nakeyi baya nufin ki rainani kuma,ki rika shiga yarda kike so kina fita Kuma ki dawo lokacin da kike so". murmushi tayi tace"kasan Dabba abunda yazo kanta kawai takeyi ,yawan kasuwancin Dana saba na tafi".ji kakeyi tas tas tas ya daiketa da kyawawan maruka.ko gezau batayi ba bare Kuma ta nuna masa Marin ya shigeta ta nunashi da hannu tace"wannan ya zama na k'arshe da wannan k'azamin hannun naka zai sake tab'a wani b'angare na jikina,bazanyi mamaki ba tunda gadon zalinci kayi,Ahaad na tsaneka ,na tsaneka ,na tsaneka bana son sake ganin fuskarka ina Dana sanin kasancewa a cikin zuri'arku"wata irin zuciyace kecin Ahaad ya rud'e gaba d'aya tunda yake a rayuwa ba'a tab'a gaya masa ba'a sanshi ba,ko wacce macce burinta ya kulata,amma yau shi ake gayawa haka,dandanan idonsa ya canxa yace"ni kike gayawa haka"."ka sani bazan tab'a yafe maka kusantata da kayi ba,ni yarana ba yaranka bane,kada ka k'ara nuna wata alak'a a tsakaninku,ka fita daga rayuwata dan Allah".
7years later
Allah ka gafartawa iyayenmu kasa muyi kyakyawan karshe
Stylish star
Jorderh majidadi
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUHIN FANSA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Na
*Maryam ismail Majidadi*
Chapter 7 · 0% Book details