Part 2 ,part 2 ,part 2
Ruhin Fansa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Bismillahir rahmanur rahim
Page 1-5 part two (2)
Aiban yana fita da Najma kai tsaye hospital dinshi ya wuce da ita,fadin tsantsar tashin hankalin da yake ciki ma b'ata lokaci ne,gaba d'aya ya rasa me yakeyi masa dadi a rayuwa ya rasa gane shin sama yake ko k'asa,miyan bakinsa ya k'are bayajin zai iya furta ko da kalma d'aya karanto duk wata addu'ar da tazo bakinsa yakeyi,ga kukan Nani da yakeji har cikin ranshi dan shikan baya san kukan mace balle babbar mata irin Nani.ko daidaita parking beyi ba ya fito da sauri tare da daukar Najma yayi ciki da sauri Nani na biye dashi kai tsaye Emergency ya wuce da ita,nurses ne suka bisa baya tare da abokinsa Dr Auwal,d'aya daga cikinsu ne ta rike Nani tace"kiyi hakuri malama bazaki iya shiga ba"janye k'ofar tayi tare da rufewa,wani kukanne ya Kuma kwacewa Nani ta zauna a chair bakin wurin ta rasa abun yi,addu'arta kawai Najma ta samu lafiya,dan idan ta rasa tasan tabbas bazata kumayin rayuwa mai dadi ba.
Duk'ufa Dr Aiban da Dr Auwal sukayi akan Najma amma ba wani labari,dafe kai Aiban yayi yace"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"dafasa Dr Auwal yayi yace"kayi hakuri abokina,ae munyo sa'a da allurai bata gama cika kwanankinta ba kaga akwai yiwuwar bata gama shiga jikinta ba,insha Allah zamu gwada wata hanyar yanzu"cikin sauri Aiban yace"Dr Naman,bara n Kira shi yanzu"Dr Naman zaune yake a k'asar India,shine farkon malamin Aiban lokacin da yake k'asar India yin karatun likitanci,babban likita ne da akeji dashi a k'asar,yana matuk'ar son Aiban saboda maida hankalinshi da kuma kwazo a wurin karatu.bugu d'aya ya dauka tare da fara magana cikin harshen turanci yace"Dr Aiban ya aeki da k'ok'ari?".shima cikin harshen turanci ya ansa da "Alhmddlh sir,dama na kiraka ne akan wata matsala"natsuwa Dr Naman yayi kamar Aiban na a gabanshi yace"ina jinka ".sosai Aiban yayi masa bayanin abunda ke faruwa da Najma .jinjina kai Dr Naman yayi sannan yace"kada ka damu komai zaiyi daidai,ae anci sa'a da allurar bata gama bin jikinta ba,zan fad'a maka alluran da zakayi mata zai tsaida gubar alluran ne,ya zama dole ka taho da ita nan da zuwa gobe kada ka yarda a wuce goben,sai ka kula da fuskar nata ,nasan kasan me zakayi"godiya yayiwa Dr Naman sannan sukayi sallama,cikin sauri ya fita neman alluran balle wahala takeyi yasha wahala sosai sannan ya samota lokacin da yazo Dr Auwal harya gama gyaran fuskar Najma ya rufeta da bandeji ruf baka ganin komai sai farin abu.cikin ikon Allah sukayi mata alluran,sannan ya fita nema masu yarda za'ayi suyi tafiya ba tare da b'ata lokaci ba.
A hankali Ahaad ya soma bud'e rinannun idanuwansa wanda suka sauya kala zuwa ja,bin mutanan dake wurin yayi da kallo,sannu kawai su Mummy suke jera masa amma ya kasa ansawa koda mutun d'aya a cikinsu,dafe kansa yayi da yake barazanar tarwatsewa,lumshe ido yayi da k'yar Mama ta lallab'ashi yasha magani sannan ya koma barci,"daga ina kike ke Kuma"Mummy ta jefawa Fadila tambaya.turo baki Fadila tayi tace"Wai Mummy ni kamar wata k'aramar yarinya zaki sakani gaba da tambayar ina naje"share maganar Mummy tayi kawai tace"Wai baki San meya faru da y'ar uwarki bane?"yatsina fuska Fadila tayi da nuna alamun k'osawa da magana tace"naji waye a garin nan da Wanda ma baya cikinsa zaice be sani ba,an tab'a yarinya mai tashe da dukiya daji da kyau,ae ko ina ya dauka an watsa mata acid an Kuma kasheta an sace gawar,ni zanje ciki na huta".bata jira cewar Mummy ba tayi ciki abunta tana kunshe dariyar muguntar da takeyi.
Aiban kam be koma gida ba sai wurin 11 sai da ya tabbatar ya had'a komai na tafiya,Kuma be wani sha wahala ba kasancewar da marar lafiya za'a bar k'asar,da shi da Nani da Dr Auwal ya tsara tafiyan,yana shigowa Hajiya Sadiya ta jefo masa tambayar da yasa y'an cikinsa juyawa"ina fatan bakai ka dauke Najma ba?,bazan tab'a yarda wata alak'a ta kullu tsakaninka da wannan shed'aniyar ba"Hajiya ta Kuma maimaita tambayan,a tsarinshi baya yiwa Hajiya k'arya komai yana k'ok'arin fad'a mata Amma wannan karon saiya tsinci kanshi da fadin "ko kusa Ummana,ni tun da mukaje da Shuhada d'azu gidan to ban sake komawa ba ae,Allah ya tsare gaba ae naji abunda ya faru"tab'e baki Hajiya tayi tare da wucewa d'akinta bata bashi amsa ba.shafa kanshi yayi ya mike tare da nufar part din shi a hanya ya had'u da Muslin ,kallon Muslin yayi fuskarsa dauke da damuwa ,"wai lafiya kuwa?,me yake damunka ne?"Aiban ya tambayi Muslim,had'iye yawu Muslim yayi yace"bari bro ina cikin tashin hankali,shi wancan uban zuciyar yayi saki cikin fushi,gashi yanzu Kuma yazo ya damu da acid din da aka zubawa yarinyar abun d'aga hankalin shine ko gawarta ba'a gani ba,Kuma babu wanda yasan Wanda yayi mata haka,ga Shuhada can na rasa ya zanyi da ita,ni kaina inajin babu dad'i dan inajin Najma tamkar yarda nakejin su Islam a raina"."Allah sarki sai hakuri kayi k'ok'arin shawo kan Ahaad insha Allah zan kula da Shuhada ita Kuma Kuma Najma Allah ya bayyana mana ita,nima dauriya kawai nakeyi.yana tura k'ofar d'akinshi ya hango Shuhada zaune ta had'a kai da gwaiwa sai rafsar kuka takeyi,da sauri ya k'arasa ciki yace"haba haba mana my sweet sis,meye abun kukan Kuma?,ina Ahaad din ya saki matar da aka daura masa a gabanki ?meye Kuma na kuka irin haka?"Aiban ya fad'a,cikin muryar kuka tace"haba Yaya ni yanzu bata wannan nakeyi ba,kaji zalincin da aka aekatawa Najma amma kai kamar baka wani damu ba,nu ina Santa har'a Raina ina jinta kamar ya yarda nake jinku ,duk yarda akayi wannan bak'in zslincin nasan makirci ne"."ya isa haka bana sonji,kiyi hakuri kiyi mata addu'a insha Allah komai zaiyi daidai bana son kuka irin haka"da irin wannan kalaman Aiban ya kwantarwa da Shuhada hankali har ya samu ta daina kuka Kuma ta tafi ta kwanta.
Tunda asubar fari Aiban yayi sallama k'ofar d'akin Hajiya,ansawa tayi tana fadin"shigo mana Muhammad aena tashi",shiga yayi samunta yayi zaune a bakin bed tana sanye da hijab da alamaun sallah ta gama,duk'awa yayi har k'asa yace"Hajiya ina kwana?,an tashi lafiya?".cikin sakin fuska da tsananin soyayyar d'an nata tace"lafiya qlau Muhammad,lafiya na ganka da sassafen nan?".sun kuyar da kai yayi cikin jinjina maganan da yakeson yi mata can k'asan mak'oshi yace"Hajiya zan tafi wani aeki India yanzu da safen nan"."Muhammad yanzu kuwa ,tafiya har India ba shiryawa tafiya"."Hajiya tun jiya nasan da tafiyar to ganin ban dawo da wuri ba shiyasa ban sanar maki ba,aekin na gaggawa ne,kuma munyi magana da Abba a masallaci yanzu ,zanyi kusan sati biyu a can"jinjina kai Hajiya tayi tace"to shikenan ae da yake sha'anin aekin ceton rai ne,Allah ya bada sa'a ya kuma tsare"da Ameen kawai yake ansawa sannan ya taso ya fito domin shiryawa.zuwa k'arfe takwas ya gama shiri har breakfast yayi dan Hajiya tsareshi tayi,sallama yayi da mutan gidan sannan ya fita,adaidaita yahau ta k'arasa dashi asibitin,kai tsaye Emergency ya wuce ya samu Najma tana nan yarda ya barta sai dai an shiryata shi kawai ake jira su wuce airport,shafa kan Najma yayi cike da matuk'ar tausayi yayi magana a hankali yace"Allah ya baki lafiya Khadija,Allah Kuma yasa fitarki k'asarnan ya zama warakar dukkanin wani abu dake damunki,Allah yasa ki samu sabuwar rayuwa ki mance da burikan daukar fansa dake ranki dan ba'a gyara b'arna da b'arna".guntun hawayen dake idonsa ya goge aka tura gadon da take aka sakata a motar asibiti sannan suka dauki hanyar airport,lokacin da suka isa kusan jirginsu na haramar tashi dan haka basu wani b'ata lokaci ba suka shiga cikin mintoci jirgin nasu ya lula cikin sararin samaniya suka doshi k'asar India.
Tunda ya tashi ya soma had'a kayanshi a akwati ,duk wani abunda yake buk'ata sai da ya had'ashi sannan ya dauki wayarsa daketa faman ruri murya can ciki yace"ya akayi ne?",lumshe ido Muslim yayi yace"haba Sulaiman yanzu bazaka d'aga tafiyar nan ba?,ka duba jikinka ko kwari babu Kuma bamu k'arasa abunda ya kawo mu ba"."kaga malan idan zaka je ka shirya in Kuma baka zuwa ni yanzu zan Kama hanya"be jira ansar Muslim ba ya kashe wayarshi,akwatinshi ya janyo daidai na matafiya ya fito yakoyi sa'a duk suna dining suna break ,ciki ciki ya gaishesu sai kuma yayi shiru daga duken da yake,Mummy tasan y'an mishkilancin suna saman kai idan za'a shekara a haka bazai ce komai ba shiyasa tace masa"Ahaad tafiya zakayi ne?"kai kawai ya iya d'aga mata alamar eh,"haba ka zauna ka idasa warkewa mana"girgiza mata kai yayi alamar a'a ya mik'e tare da d'aga masu hannu yasa kai ya fice,yaransa suka karb'i kayan dake hannunsa ,sannan suka jera motocinsu suka fice a hanya suka d'auki Muslim dan haka suka dau hanyar Niger Delta".
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan k'arshe.
Kamar kullun majidadi ta dawo,ina fatan yarda muka fara lafiya Allah yasa mu gama lafiya,sannan Kuma inji ruwan comments kamar yarda aka saba mu farantawa juna rai.
Stylish star
Jorderh majidadi
Page 6-10
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUHIN FANSA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Na
*Maryam ismail Majidadi*