Part 2 ,part 2 ,part 2
Ruhin Fansa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Page 16-20
Sosai Umti ta fahimci halin da Shuzna take ciki dan haka ta matso kusa da ita tace "taso muje d'aki ina son muyi magana"yunk'urawa Shuzna tayi Umti na rik'e da hannunta sai jera mata sannu Nani takeyi ,suna shiga d'akin Umti a gefen gado suka zauna duka hannuwanta Umti ta Kama tace"Khadija ki tattaro duka hankalinki ki bani,naga yanayin da kika shiga Kuma na fahimta lokacin da kika ga Sulaiman,Sulaiman dai anan yayi karatu gidan nan tamkar gidansu yake,baya da maraba da d'ana Muslim,ni ina da tabbacin Sulaiman bazai wani kulaki a gidan nan ba,to kema ki share kada ki sake ki bashi k'ofar dazai gane kece Najma,ki bari harya safko da kanshi ya nuna soyayyarki sannan ki bashi kai"a matuk'ar razane Shuzna ta d'ago dara daran idanuwanta tana kallon Umti cikin k'asa da murya tace"Umti har abada,har abada bazan tab'a iya komawa gareshi ba"murmushi Umti tayi tace"y'ata kada fushin yayi yawa,kici gaba da addu'a insha Allah komai zaiyi daidai,Ahaad ba mugu bane kawai kun samu matsalan fahimta ne".
"Wallahi ki taso in yi tafiyata ni kad'ai ,bana so ruwa ya samemu a waje,yau tafiyan bamai nisa zamuyi ba"Shuzna ta fad'a tana k'ara kallon bubun dake jikinta na atamfa,murmushi tayi ,hannu Shuhada ta karkad'a akan fuskar tata tace"yadai uwar biyu,ko sirikin nawa yayo waya a sasanta ne kike ta cika fuska da fara'a haka"yunk'urawa tayi zata kamo Shuhada,aeko ta kauce tana babbaka dariya"wallahi zanyi maganinki a gidan nan,inawa kaina dariya ganin nasa atamfa,inaga tun ina yarinya na yarda saka Kaya haka ko da nayi auren bana sakawa"."Kuma kinsan kinyi bala'in Kyau sosai,fatana dai Allah ya saukeki lafiya mu koma school".haka suka fito suna tattaunawa gwanin birgewa suka Umti da Nani sallama suka fita a k'afa dan Shuzna ta samu ta motsa jikinta.fitarsu ba dad'ewa sama tayi bak'inkirin hadari ya soma cida iskar damuna mai sanyin dad'i ta fara kad'awa ko da wanne lokaci ruwa zai iya tsugewa,kamar Shuzna zatayi kuka ta k'ara k'ank'ame d'an k'aramin gyale dake jikinta tace"wayyo Allah,bana son ruwan nan ya tab'ani".kallonta Shuhada tayi tace"aeko to inmun tsaya bamu san yaushe ruwannan zai Kai ba,gashi babu abun hawa,ki daure mu k'arasa".Jan k'afa kawai Shuzna takeyi dan takai k'arshe ji takeyi kamar zata fad'i a wurin ga sanyi da takeji har k'arma ta soma,jin ruwan ya fara sauka yasa Shuzna lunshe idanuwanta tanajin safkar ruwan har cikin ranta,kafin wani lokaci sunyi sharkab da ruwa har d'igan ruwa sukeyi.
Motace ta gittasu sai dai baka iya gane waye yake ciki,tsayuwa Shuzna tayi tana mayarda numfashi.motarce ta dawo gabansu ta tsaya,lek'owa driver din yayi wanda yake zaune da kayan sojoji yace"madam ".dariya Shuhada tayi tace"la Samuel"haba bata tsaya komai ba tayi gaban motar tace"Shuzna ki shiga baya zakifi sakewa".da k'yar Shuzna ta shiga k'araso gaban motar,gabant ne yayi mugun fad'uwa,ga k'amshin turarenshi daya addabi hancinta bata da wani zab'i haka yasa ta k'arasa shiga kawai ta zauna.d'ukowa yayi saitin kunnenta yace"y'ar lukuta idan kika fasamun laptop sai dai mijinki ya biyani kayata"ya Kuma juya tamkar bashine yayi maganar ba.dan d'agawa tayi ta zaro laptop din ta daura masa bisa cinyarsa,,hannunta yad'an shafi jikinshi yarrr suka ji gaba d'ayansu,amma ko da wasa bai nuna yaji wani abu ba, kallonta yayi yace"kinji dadi kin tab'ani Kuma kinsan saina rama,idan so kikeyi maza su tab'aki to ki komawa mijinki danmu gidan nan ba y'an iska".sake da baki haka Shuzna ta bishi da Kallo ,ji takeyi ae yama gama da ita,kafin tace wani abu motar ta tsaya kawai sai ta saki kuka ,lokacin har Shuhada tayi cikin gida,shima fitowa yayi ya zagayo inda take yace"malama a fito mana daga mota,dan bama tai maka maki zanyi ba gara ki fito da kanki". k'ok'arin fitowa tayi amma k'afarta ta rike sai kawai ta Kuma rushewa da kuka ta rumtse ido sosai tana yarfa hannu tana fad'in"wayyo Allahna,wayyo Nani ,Ummuna k'afana bazan iya fitowa ba Allah"sosai tayi masa kyau ya saki baki yana kallonta ganin zata bude ido yasa yace"Dallah malama rufemu baki Shagwab'a na yara ne ba tsofi jawarawa irinku ba".maganar ta shigeta sosai ,hannu yasa ya kamota kawai sai ta saki murmushi mai wuyar fassaruwa.
Suna shiga parlon tana k'ok'arin kwace hannunta daga rik'on dayayi mata amma sam yaki bata dama.da sauri Umti da Nani sukazo suka kamata suna mata sannu,Umti tace"tun d'azu naketa faman zullimi gashi dai sai da ruwan ya tab'aki,ga Yayanku Aiban can ma yazo tun d'azu yake zaryar nemanki.sai lokacin Aiban ya d'ago yace"Babyn Aiban kije ki canza kaya bana son sanyi ya kamamun ke"dakuwa Umti tayi masa tace"ungo wannan yaushe ka zama marar kunya haka?"sosa k'eya yayi yana dariya,Bayan Nani Shuzna tabi da take cewa"Maza kizo kiyi wanka da ruwan dumi ko zaki daina jin sanyin nan".Ahaad kam bin bayanta yayi da Kallo yadda rigar ta d'ame a jikinta yana kallon yarda hips dinta suke juyawa jin yana neman fad'awa wani yanayi yasa yayi saurin kawar da kanshi suka gaisa da Aiban ya wuce part dinsu,yana shiga ya Samu Muslim yana aekin danna waya,be kulashi ba ya soma zare rigar dake jikin shi,"Wai dan Iskanci mutun ya shigo d'aki amma be iya ko kallon Wanda yake a d'akin ina amfanin bak'in hali wacce ma macace zata iya zama da kai a haka mugu kawai"wani irin duka Ahaad ya kawowa Muslim cikin sauri ya goce ya fice da sauri yana dariya tare da rufo d'akin.kwafa Ahaad yayi ya fad'a toilet.
Lokaci na tafiya,kwanaki suna karewa,mintina na tafiya hakan ne ya faru a rayuwar su Shuzna ,cikinta harya shiga watan haihuwa,zaune take a compound din gidan tayi d'ai d'aya akan tabarma tayi wani irin girman ciki ga k'afarta data kumbure ,yau tunda ta tashi takejin wani irin matsanancin cikin mara saboda dauriya ta shanye ciwan taki fad'awa kowa,Aiban ne gefenta yana yanyanka mata apple tana ci,d'ukar da kanta k'asa tayi tana taunar lips dinta kamar zata huda "ciwanne ko?,tun safe ina lura da ke amma kin wani gardama ki tashi muje asibiti"Aiban ya fad'a yana niyar mik'ewa,isowar Ahaad wurin kenan zai dauki wayar Umti data bari a wajen yana d'ukawa yaji an ruko hannunsa ,batasan ta rike hannun Ahaad ba ta k'wallah k'ara tace"wayyo Allah marana,Yaya zata fashe,ku taimakeni dan Allah".a kidime Aiban yace"Ahaad ka sakata mota bara na kira Nani"be jira ansar Ahaad ba yayi cikin gidan da sauri,shikam kallonta yakeyi yadda ta jike da gumi sai siraran hawaye dakebin kuncinta ga lips dinta data taune sukayi jajir dasu,tayi matuk'ar bashi tausayi da sauri ya sab'eta dukda nauyin da tayi haka ya daure ya sakata mota hakan yayi daidai da fitowar Umti da Nani ,Aiban kasa yin komai yayi dan dole Ahaad yaja motar zuwa asibitin.
Dr Naman ne da Umti ke kanta,Aiban kasa shiga d'akinma yayi,tasha bak'ar wahala Wanda harsun fidda ran zata iya haihuwa da kanta sai kawai ga kan baby ya taho,yana fitowa kuma wani ya biyo baya,sai kuma ga wani,suka saki kuka a tare Alhmdllh kawai Umti ke fad'a.
Bayan minti talatin Umti ta fito ita da wata nurse Ahaad ne kawai a wurin Umti ta saki gud'a tace"yau na zama kaka,kaka Kuma harta y'an ukku,yau bansan wanne irin farin ciki nakeyi ba"ta k'arasa wurin Ahaad tare da daura masa yaro na farko tace"ga Hassan"sannan ta daura na biyu tace"ga Hussain"sai Kuma jikata ta k'arshen mace wato "gambonsu".wani irin Kallo Ahaad yake binsu dashi ganin tsantsar kamarsa da yaran babu abunda suka baro nasa,yayi matuk'ar kidima da ganin wannan kamar,dariya Umti tayi tace"kana kallon kamarku ne ko?,kada ka damu Allah yana iya halitta haka,ina Aiban ne?"kafin ya bata ansa sai ga Nani da Aiban sun iso cike da farin ciki suka k'araso garesa tare da d'aukar yaran suna zumudi dajin dadi,da sauri Nani ta shiga d'akin da aka kai Shuzna ta rungumeta tare da sakin kuka.itama Shuzna kukan ta saki tare da rungume Nani,shigowa Umti tayi ta daura duka yaran akan cinyar Shuzna tace"kibar kukan nan ki kalli abunda kika haifa"a razane take kallon yaran taba kallon Ahaad dake tsaye gabanta.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe
Stylish star
Jorderh majidadi
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUHIN FANSA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Na
*Maryam ismail Majidadi*