← Book details Royal Consort Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 34

Sashe 31

Royal Consort Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A office of investigation,’yan matan suna zaune gaba dayansu Aliya ta shigo da saurinta
“Wai da gaske ne abinda nake ji shukra ta samo hujja mai muhimmanci?” Rukayya ce ta bata amsa
“Ehh da gaske ne,an ce wasu kalmomi ne na china kuma ba kowa yake iya gane me suke nufi ba” Afrah da take zaune tace
“Lahh abinda shukra ta nuna min,nace ta mayar basu da amfani” sameerah ce ta kalli Afrah
“Lallai ta qara takar sa’a kenan” Afrah ta miqe tsaye
“Ta yaya zaki ce ta taki sa’a,taga abu mara ma’ana,ni banyi tunanin zai iya zama wani abu ba,amma ita ta dage har sai da ta fitar da abu mai ma’ana a ciki,kuma kice sa’a ce?” Shiru Sameerah tayi,Afrah ta cigaba
“Wannan halin naku shi zai kaiku ya baro,wai ta taki sa’a saboda kawai ba zaku iya yaba mata akan qoqarin da tayi ba” kowa tsit yayi a wajen don kuwa gaskiya Afrah ta fada,baqin ciki kawai sukeyi.

A office din director kuwa,lady sumayya ce cikin bacin rai take fadawa director
“Yarinyar nan fa yin kanta tayi ba tare da izinin kowa ba,ko da ta samu abu mai muhimmanci amma mu bai kamata ace mun zuba ido ba,ya kamata a hukunta ta domin tayi gaban kanta….” basma ce ta katseta
“Duk da gaban kanta tayi amma ta cece mu ne gaba dayanmu daga abinda zaije ya dawo idan labari ya jewa sarkin china cewar an tura ladies investigators a matsayin ladies-in-waiting domin suyi binciken qarqashin qasa,yanzu kuwa ana samun hujja a kan wanda ake tuhuma ai komai ya qare,kuma muma mun tsira daga mu har mai martaba” harara sumayya ta aika mata,basma ta sunkuyar da kanta,director ce tace
“Yanzu ina yarinyar take”
“Naga kamar bata cikin nutsuwarta,shiyasa nace taje ta huta” nadeeya ta bata amsa.

Shukra da gabadaya ta rasa ma wane tunani zata yi,tana zaune ta lumshe ido ita kadai take magana da kanta
“Dama shi ne? Shi ne ? His majesty The king” bude idonta tayi,da sauri ta qara lumshe su tare da cewa
“Na shiga uku na,yanzu tunda na san shine mai martaba lallai sai ya hukunta ni akan rashin girmama shi da na dinga yi,ina magana dashi kamar naga sa’a na,dama mai martaba ne? Shikenan tawa ta qare”
Nan da nan ta fara tunanowa tun ranar da suka fara haduwa,ta tuna ya taba ce mata
“Ya bata imperial order” (Dokar karagar mulki wacce sarki ne kawai yake bada ita) da lokacin da yace mata bai taba hawa katanga ba,da lokacin da yace mata yayi umarni a turo ‘yan sanda,kuma taga ‘yan sandan da suka zo ba ‘yan sandan sirri bane ‘yan police bureu ne,ta tambayeshi yace mata
“Ai duk qarqashin ikona suke” da lokacin da yace mata zai bata kyauta a maimakon mai martaba,ai kyautar shi da ta mai martaba duk daya ne,da lokacin da ya kaita royal library tayi karatu,da lokacin da yace mata ya kori masu gadin dare na qofar fada saboda ta wuce don ba zai iya qara tsugunnawa ta taka shi ta haura katanga ba,abubuwa da yawa suka dinga dawo mata,a hankali ta furta
“Lallai ni shashasha ce,ashe akwai abubuwa da dama ya kamata na fahimta,amma meyasa yace min shi dan sandan sirri ne?” A take ta tuno lokacin da take daka matsa tsawa sai dai ya zabi daya,ko ya haura katanga,ko kuma ya duqusa ta taka bayanshi ita ta hau.
“lallai na shiga uku na lalace,duk mai martaba na dinga yiwa haka? Lallai sai yasa anyi min kisan da ko gawata ba za’a gane ba”
Muryar sameer ce ta ratsa kunnen ta
“Shukra shukra” shi da manager da gudun su suna nemanta,idonta a lumshe suka tarar da ita,duk kiran da suke qwala mata kamar bata ji,hannu sameer yasa ya bugi katakon da ta jingina dashi,a hankali ta bude ido,manager ne yace mata
“Lafiyarki kuwa? Ana can ana ta cewa an kama lady investigator a quaters din baqi,har mai martaba ma yaje wajen” da sauri tace masa
“Kaga mai martaba?” Sameer ne ya saki murmushin jin dadi
“Abin mamaki ko? To idan kika ganshi kamar abokin mu dan sandan sirri” rintse ido shukra tayi jin abinda sameer ya fada,ganin bata ce komai ba ya cigaba
“Da gaske fa,idan baki kula sosai ba sai kice mutum daya ne” har yanzu bata ce komai ba,manager shima yace
“ yanzu fa mutane sai su dauka abota nake da mai martaba,don kamannin su babu maraba” shukra da sai yanzu ta bude idonta tace
“Ai shi ne,wannan mutumin da kuke magana shine mai martaba” tuntsire mata sukayi da dariya,sameer yace
“Mai martaban ne kike ganin shi a arha ko? Lallai kin samu matsala,kama ce kawai”
“Da gaske nake,har magana munyi dashi,Wallahi shine mai martaba,alhinin da kuka sameni inayi kenan,ji nake kamar zanyi hauka” zamewa sameer yayi qasa yai zaman dirshan tare da cewa
“Mai martaba ne nasa shi shan shayin dole,na dinga dura masa nace masa kuma dole sai ya shanye,na bashi ganda nace ya cinye a cikin kasuwa,na shiga uku” manager da ya fisu qarfin hali yana tsaye yace
“Ni da muka taho tare na sarqe mai hannunshi ciki nawa,nai ta ɗaka masa duka a qirji,yana ta cemin indaina dukanshi,ba’a taba dukanshi ba,na ce masa,na dakeshi din” shukra ce tace musu
“Dukkanku ai naku mai sauqi ne,ni fa….taka….takashi nayi a baya na hau Katanga” dukkansu sun shiga tsananin tashin hankali,idan kaga fuskarsu sai kace saqon mutuwa aka aiko musu.

Mai martaba yana zaune a grand palace da takaddar da shukra ta samo a qauters din baqi da IG ya kawo masa,sun duba yadda suka karanta sunan wani qauye ne da yake bayan gari kuma kusa da gaɓar ruwa,hakan yasa mai martaba yayi umarnin suje su bincika qauyen ko zasu samu wata hujja a wajen,yana zaune da abin a hannunsa yana kallo,a hankali yace
“Me yasa zamu hadu da ita a haka? Me yasa? Kai ban so haka ba,yanzu yaya zata ji? Kamar ta yadda dani ni kuma na ha’ince ta ko?” Shi kadai yake maganganun sa.

Su shukra da duk tsoro da alhini ya cika su suna nan inda suke zaune,wasu ladies-in-waiting suka qaraso wajen,ta bayan shukra suka shigo shiyasa basu kula da zuwansu wajen ba,ta gaban ce tace
“Kece Shukra Anas Malak ta Office of investigation?” Juyowa shukra tayi tare da cewa
“Yes my lady” matar ta qara cewa
“Ki biyo mu a baya,domin mai martaba ya nemi ganinki” ai manager da yake tsaye qafarsa ta kasa daukar shi,kamar zai fadi dai yai saurin qarfafa jikinshi,a ranshi yace
“Shikenan ta faru ta qare,an fara da shukra saura mu” sameer kuwa ido yayi qifi qifi a zaune.

A can qauyen da aka tafi bincike,IG yana bakin ruwa yasa aka bincike jiragen ruwa da zasu bar garin,ba’a samu komai ba,lieutenant ne ya qaraso tare da cewa
“Yallabai duk inda zamu duba mun gama dubawa bamu samu komai ba” jinjina kai yayi
“Bani taswirar qauyen na gani (map) “ bude takaddar da map din take akayi,kulkin da yake hannunsa yasa ya nuna wani waje
“Nan wajen ya kamata ace akwai gidan ajiyar kaya “ da sauri lieutenant yace
“Ehh Assistant sun tafi shida jaleel suna wajen”
IG ne yayi gaba suka bishi a baya,suna isa wajen daidai lokacin da jaleel yake cewa
“Tunda bamu samu komai ba ya kamata mu bar binciken nan haka,mun duba ceiling,mun duba rijiyoyi amma bamu samu komai ba” jin haka IG yace
“Toh ku wuce mu tafi kawai” cikin jin dadi jaleel yabi bayanshi haka sauran ‘yan sandan ma suka fara tafiya,IG ne ya tsaya cak tare da juyowa yana qarewa wajen kallo,jaleel ya fara rarraba ido,juyowa IG yayi ya koma ya fara zagaye wajen a hankali yana qarewa ko ina kallo,hakan yasa duk suka biyoshi a baya,daidai wani gini ya tsaya tare da cewa assistant lieutenant
“Kace baku samu komai a cikin dukka ginin ba?”
“Ehh yallabai,na tabbatar babu komai a ciki” jinjina kai IG yayi tare da matsawa kusa da ginin da dora hannunsa,alamun sabon ginin qasa ya gani domin hannunsa ya lakuto taɓo,kulkin da yake hannunsa yasa ya fara dukan wajen,har sai da yayi rami,dama sabon gini ne ko bushewa baiyi ba,idonshi ya saka ya leqa,nan ya hango kayan bindigogi manya manya,da wasu akwatuna da bai san menene a ciki ba,juyowa yayi ya kalli lieutenant
“Kaje yanzu yanzu a sanarwa wakilin sarkin china cewar mun samu qwaqqwarar hujja akan Kim young Dal”
“Yes sir” lieutenant ya fada tare da barin wajen,cikin jaleel ne yayi wata irin murdawa,domin a tsorace yake amma ko kaɗan ba zaka gane hakan a fuskar shi ba,IG yasa sauran suka sauke ginin aka fiffito da duk kayan da suke ciki,kayan makamai ne masu matuqar yawan gaske.

Mai martaba a tsaye a grand palace,ya goya hannayensa sai kai da kawowa yake yana zagaye wajen,ɗaga murya yayi
“Waye a nan?” Chief eunuch ne ya shigo tare da rusunawa ,mai martaba ya tambaye shi
“Wai yaushe zata qaraso ne? Na jita har yanzu shiru” qara rusunawa yayi
“Ka gafarce ni your majesty,saboda ana bin matakan tsaro ne” jinjina kai yayi tare da yi masa alama da hannu ya tafi.

Shukra tana quaters din ladies in waiting na grand palace,a tsaye take ta daga hannayenta sama suka caje ta tsaf suka tabbatar babu wani mugun abu a tattare da ita,babbarsu tace musu
“Ku shiryata,ku bata kaya ta saka” ta fice
Wani kwali suka dauko,suka fito da kaya daga ciki suka miqawa shukra,kallon su ta tsaya yi
“Menene wannan?”
“Kaya ne,ba zaki iya zuwa ganin mai martaba da wannan uniform din naki ba,dole sai kin canja” karbar kayan shukra tayi,kaya ne irin wanda special court ladies suke sawa,ta saka riga da skirt sunyi mata kyau sosai,fitowa sukayi tabi wanda zasuyi mata rakiya zuwa wajen mai martaba,suna tafe a hanya tana zancen zuci
“Ko me yasa yallabai….au mai martaba yake nema na? Ko zai gafarta min ya yafe min idan nace masa ban san shi sarki bane?” Suna tafiya tana ta kalle kalle domin kyawun grand palace ba na wasa bane,bata taba gani inda aka qawata waje kamar haka ba,tana ta kalle kallenta amma gaban ta na dukan shida shida,domin bata san me mai martaba zaiyi mata ba.

Oum tasneem ✍️
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤

ROYAL CONSORT

©️ marriam mayshanu…. ✍️

Page 28
Chapter 31 · 0% Book details