← Book details Rayuwar Rayhana Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 14

Sashe 9

Rayuwar Rayhana Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayhanah ta ga idan ta bari Ibraheem ya ci gaba da cusa mata bakin ciki a kan ‘yammatan kan titi ta fadi babu nauyi, kuma zuciyarta za ta buga. Sai ta yi zaman ‘yan bori a gabansa ta daddage ta fasa masa kuka mai gigitarwa.
Iyakar tsorata Ibraheem ya tsorata, wayar hannunsa bai san inda ya jefa ta ba. Don ya dauka nakuda ce ta zo mata da ciki wata shida. Ya kama ta ya kankame yana kira.
“Mene ne Rayhanah? Haihuwar ce?”
Ture shi ta dinga yi da iya karfinta..
“Ka rabu dani, in ma mutuwa zan yi in mutum mana ina ruwanka? Tunda ‘yan iska sun sa ka juya min baya, to ka mai dani inda ka dauko ni…..”
Dariya ce sosai ta kama Ibraheem da ya fahimci musabbabin wannan ihun da ya kada masa ‘ya’yan hanji, yasa shi cikin tashin hankalin, kada a haife masa bakwaini a tsakar daki.
Ya ce, “To ga bayan na dawo miki da shi, zo ki hau!”
Ya juyo mata bayan, ya yi durkuso a gabanta…..
“Zo ki hau Rayhanah, na daina juya miki shi. Zo ki hau ki riga baby hawa, don ban tashi juya miki baya ba ma sai ranar da Allah ya fito da Da na ko ‘yata duniya Rayhanah, muddin baki daina kokarin azabtar dani da kishinki na shirme ba, wanda ba irin na su Nana Aisha ba.
Kishi ne na halaka da daukar hakki Rayhanah, duk abinda zai munana lahirar ki bana sonki da shi Rayhanah, kuma ba zan zama sanadi ba.
A da, na san Rahane mai yiwa mutane uziri ce, uzri sau saba’in, kafin ta kama su da yi mata laifi, tunda ‘no body is perfect, except our Almighty…..!!!”

Jikin Rahane ya yi matukar nauyi, idonta ta dago a hankali ta kalli mijin nata, shima idonsa a kanta. Sai dai gab yake da ya fidda hawaye.
“Zo ki hau…..”
Ya zube a kasa ya bata bayan. Da gudu ta runtuma ta rungume shi ta bayan, tana fadi cikin kuka,
“Ka yafe min Yaa Himu? Zan kasance cikin tababbu, butulu masu manta alkhairi da rashin godiyar Ubangiji idan baka yafe min ba IBRAHEEM…....”
Juyowa ya yi ya kama ta, fuskar mai cike da kwarjini da kamala, kunshe da murmushi mai kayatarwa yana kada kai.

“Zan yafe miki only in kin hau bayan nan na goya ki, kafin na goya ‘ya’yan Ibrahim!!!”.

Sai ta dane shi, ya mike kamar bai dauki komai ba sabida rashin nauyinta, ya nufi master bedroom dinsu.
Tana tuno kalaman Daddy ne a wannan lokacin…..

“Ibraheem is a nice person… Allah ba kwarzantashi nake yi ba Rayhanatu… wata rana ke da kanki za ki gaya min hakan….
Lokacin da zai sunkuya yana yi muku doki sukutum ke da yaranku…..”

“Ba ka yi karya ba Daddy… bayan kasancewarsa nice, honest ne, kind ne, brave ne, sweet ne, jarumi ne kuma sadauki a fannin nuna soyayyah!!!”

*****

Tun daga wannan ranar da Ibrahim ya nunawa Rayhanah, ita wani bangare ce na rayuwarsa da ba zai iya rayuwa ba ita ba, fushinta a kansa zai iya gurbata rayuwarsa. Rayhanah ba ta sake yin irin wautar da ta yi a baya ba, ba ta sake takurawa Ibrahim a kan ‘yammata ko wayarsa da mutane ba.
Ita duk mai son Ibrahim ma duk kyanta da matsayin da take takama da shi ko na iyayenta tausayi take ba ta. Annabi (S.A.W) ya ce,
“Imanin dayan ku baya cika har sai ya sowa dan’uwansa Musulmi abin da yake sowa kansa”.
Ta yarda ta amince Ibraheem abin so ne, ba kowacce mace mara aure ce za ta iya dauke ido a kansa ba, don haka ta kama addu’a ta kama Ibrahim, ta kuma hada da kau da kai daga mu’amalarsa da kowa.
Illa kullum tunaninta shine hanyoyin da za ta bi ta kara kyautata aurenta, ta kara martabarta a idanunsa. Tunda ita din dai da ba kyakkyawar ba, ba ‘yar kowan-kowa ba, ita Allah ya kashe ya baiwa.

Already Ibrahim ya gama duk abin da zai yi a Chicago, amma ganin cikin Rayhanah ya shiga wata tara sai ya bari sai ta haihu don su jewa Daddy da tsarabar da za ta gigita shi, don ko kusa bai taba gaya masa Rayhanah na da ciki ba.
Shi Daddyn ne dai yake faman tambaya sai ya yi dariya ya ce,
“A ci gaba da addu’a Daddy”.

A dai-dai lokacin EDD dinta ya cika, don haka bai cika yin nisa da gida ba, haka ko tafiya yake on the street waya suke, sai idan driving yake. Shima din earpiece na jikinsa, da ta yi kira zai sauka gefen titi ya amsa.
Ranar litinin, bayan gajeruwar nakuda ta haifi diyarta mace mai kyau, abin mamaki mai matukar kama da Mami, duk da cewa kalar iyayenta ce (choculate) har sun fi ta haske. A labour - room na asibitin (Illinois).
Ibrahim da shi aka karbi haihuwar, kuma sai da aka sake dinketa kamar kwarya (kamar yadda yake fadi).
Shi da kansa ya goge jaririyar da olive oil (Zaitun), ya nadeta cikin shawul ya rungume yana yi mata huduba da kalmar shahada cikin kunnuwanta, ya dura mata zam-zam, ya tauna dabino (ajwa) ya sa mata a baki, sannan ne ya bari Nurses suka karbeta suka yi ta wanke ta.
Ashe har da dattin ciki ya kara mata baki, da aka gama wanke ta sai ta koma kamar Abida. Rayhanah da ta dubi yarinyar da Ibrahim ya dora mata a kan cinyarta sai da ta tsorata…..
Yarinya kamar Abida ce ta haife ta, cleft din Ibrahim a kasan habarta, ga beauty point din Mami.
Sai ta ji hawaye na diga daga idanunta suna sauka a fuskar jaririyar da ta tabbatar Mami da Abida ba za su karbeta a matsayin jininsu ba, duk da cewa dasu take kama, saboda daga jikinta da suke gani kaskantacciya sauran cuta ta fito. Sai ta yi wani tunanin da ya sanyaya mata zuciya, tunanin cewa,
“ Jawahir za ta goya ta, Aziza za ta dauke ta.”

Rayhanah ji ta yi hankalinta ya dugunzuma ya yi gida Nigeria, gara ayi wacce za ayi tsakaninta da Mami wannan boyayyen aure ya isheta, ba za ta yarda Mami ta sheganta mata ‘ya ba, tunda ba ta san da auren ba.
Babban takaicinta a kullum idan ta tuno tozarcin da Mami ta yi mata sanda take zargin Daddy da nemanta.
A wancan lokacin ba ta dau al’amarin da zafi ba saboda rayuwarta dake reto a gidan iyayen rikon nata, amma yanzu da ta samu nutsuwa da karin hankali ta yadda ba karamin tozarci da wulakanci Mami ta yi mata ba. Mutumin da yake makwafin mahaifi agareta.
Ta dauki ‘yar sosai a jikinta, tana kallon kyakkyawar fuskarta wadda ta ji hanci da ido, da dan bakinta mai kyau kamar Dr. Asma’u Mansur Takai….
Sai ji ta yi Ibraheem ya rungumesu ta baya.
Dukkansu rufe idanunsu suka yi ruf, daga su har jaririyar, a sakamakon shigowar wata sabuwar kauna da soyayya mai girman da baya misaltuwa da ta kara shigewa cikin zukatan kowannensu.
Tsayin minti biyar sannan Ibrahim ya karbi Babyn daga hannunta yana kallo yana murmushi, ya ce,
“Mami na ce….. sunanta NANA ASMA’U!’
Cikin karaji Rayhanah ta ce,

“Ban yarda ba, sai in ita da kanta ta amince a kira ta Asma’un…..”

Idanun Ibrahim suka yi mici-mici yana kallon ta da mamakin dalilin wannan ANGER haka a kan sunan mahaifiyarsa. To sunan Mamin ne ba ta so ko Mamin ce ba ta so?
Ko kuma me take nufi da sai idan ita da kanta ta yarda a kira yarinyar Asma’u?
Bai gama tunanin da yake yi ba sai gani ya yi Rayhanah ta goye ‘yarta da tawul din da take kunshe ciki, ta yi lullubinta yadda ta saba ba tare da tunanin cewa a asibiti take ba, kuma likitanta bai sallameta ba ta doshi kofa.
Ibraheem tsayawa ya yi yana kallon ta ya daskare a tsaye kamar statue (mutum-mutumi). Bai ankara ba har ta kai kofa, sai ya yi azama da sassarfa ya cimmata ya damko hannunta.
A rikice ya ce, “Rayhanah ina za ki je? Tafiya za ki yi ki barni Rayhanah? Me na yi miki? Ko ko ba ki yi farin ciki da kyautar da Allah ya bamu bane? Ko don na ce zan sawa ‘yata sunan mahaifiyata? Above all ma ina za ki je ne?”
Hawaye na kwarara a kan fuskarta ta ce,
‘TAKAI!”
“Takai???”
Ya fada cikin sigar tambaya.
“To wajen wa?”
Ya sake fadi a gigice. Ba tareda ya jira amsar farko ba. Ta kai tafukanta ta rufe fuskarta ta soma shesshekar kuka kafin ta ce,
“Wajen Inna Juma da Inna Zinaru”.
Wannan lokacin Ibrahim ya fara fusata.
“Saboda na ce zan sawa ‘yata suna Asma’u? Ko don tsuntsun soyayyata ya tashi don kin haihu dani?”
Ba ta ce komai ba, sai girgiza kai take tana kuka.
“Zinarun ta ci uwata….. ta ci ubanta! Ke idan kina da hankali har za ki sakota cikin wadanda za ki yi tinkaho da su? To amma ba da wannan jaririyar da ke bayan ki ba ko?”
Ta fiddo ido jike da hawaye ta ce,
“Ai ita zan kai can, sai ni in dawo”.
“........Da yake kutumar uban Zinaru ne ya yi cikinta ko? Sakko min ‘yata!”
Ya mika mata hannu. Shi kansa baisan sanda wannan ashariyar da bai taba yi ba koda wasa ta sulmiyo daga bakin sa ba. Cikin kuka mai fitowa tun daga karkashin zuciya ta ce,
“Idan sama da kasa za ta hadu, ba zan baka ‘yata ba ka kaiwa Mami....….”
Ai ba ta idasa rufe bakinta ba ta ji saukar marin da ya tafi da jinta da ganinta na wucin gadi, har sai da ta ga wuta da gilmawar taurari, kafin ta farfado ya sake shimfida mata wani, ya fizgo yarinyar dake bayanta, wadda a take ta soma canyara kukan da ya ratsa har cikin kwakwalwar Ibrahim…..
Chapter 9 · 0% Book details