← Book details Rayuwar Rayhana Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 14

Sashe 4

Rayuwar Rayhana Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana kwance ruf da ciki a doguwar kujera, exercise wears ne a jikinsa. Da alama ya yi exercise din ne ya gaji yake hutawa. Ta karasa ta zauna a kujerar gefensa kanta a kasa ta yi shiru.
Ya ji bude kofarta da fitowarta amma bai juyo ba, don ya san ba wani abu za ta ce masa ba, shima bai san me zai ce mata ba.
Amma ga mamakinsa sai ya ji ta zauna a kasan kujerar da yake kwance muryarta na dan rawa ta ce,
“Don Allah don Annabi ka yi hakuri Ya Himu, Allah ni ban san abin da zan dinga ce maka bane shi yasa nake yin shirun..”
Ya yi shiru bai tanka mata ba. Sai ta sake cewa cikin damuwa ta gaske,
“Ka gaya min abinda kake so in dinga gaya maka din, sai in gaya maka…”
Bai juyo ba amma dariya ce ta kama shi, a kalla ta nuna ba ta da wani ra’ayi nata na kashin kanta sai nasa.
Ya mike gaba daya ya zauna sosai a kujerar ya mike santala-santalan kafafunsa a kan tebirin gilashi, ga alama ya yi matukar yin sabo da irin wannan zaman.
Ya dube ta a hankali ta sadda kai tana share hawaye ya ce,
“Yaa Ladif! Ke kam baki da aiki sai kuka kamar matar mamaci? To ai kinga abin da bana so din kenan, kukan.
Rayhanah ya za ayi na ga farin ciki da walwala a fuskarki? Bayan Daddy ya ce min kina hira har da dariya, ko duk a cikin rashin son nawa ne Rayhanah? Me zan yi ki saki jiki dani ki daina sani a gaba kina min kukan nan?”
A hankali amma da alamar fusata cikin consonants and vowels din sentence din da zai fito daga bakinta tace,
“Ka daina tuhumata a kan Yaya Khalipha!”.
“Saboda kada in taso miki da son da kike masa?”
“Ka ga abin da bana so din kenan”.
“Sai in yi shiru, ni ina aurenki kina tunanin wani can?”
“Ni na ce maka ina tunanin sa?”
Ta fada muryar na kara yin rawa.
“Kada ki yi min kukan saurara….. dago ido ki dube ni…..”
Ta kasa dagowar sai da ya sake maimaitawa a dan zafafe.
Cike da nauyi, da tsoro da firgita ta daga idanunta a hankali ta dube shi.

Abin da ta gani cikin idanun Ibraheem din suna da yawa, ga kishi, ga rikici, ga neman rigima, ga neman tada zaune tsaye….. sannan ga so da kauna mai yawa….. so yake ayi ta rikici kada a daina ba shi da alamun saukowa idan ba a fadi yadda yake so ba.
Sai ta mike ta yi dakinta da sauri-sauri da gudu-gudu don zuciyarta da gangar jikinta ba za su iya jure rikicin nasa ba. Shine bai son a zauna lafiya sai dai ya yi ta tone-tone kamar kaza, to ita ina yake so ta jefa ranta?
Eh, da gaske ta so Khalipha domin mutum ne mai kyautata mata, mai son ganin walwala da farin ciki a fuskarta da zuciyarta…. Mai son inganta rayuwarta, mai darajata a duk lokacin da Abida ta wulakantata.
Mai nuna mata cewa nakasa ba hujjaba ga jera kafada da sauran mutane! Yaya Khalipha yace da ita a lokuta da dama “You are only disabled if you truely believed you are .........!! He’ll stand by her even when the whole world turns its back on her..... he's indeed her pace-setter!!!
To mai yi maka wannan ya za ayi ba za ka so shi ba? Tunda ita zuciya an halicceta ne da son mai kyautata mata???
To Allah mai juya al’amura bai nufi za su yi aure ba, ya canza mata da shi, kuma ta karbi canjin, ta gane abubuwa da yawa wadanda a da ba haka suke ba.
Wato sai da Ibrahim ya zo ne da ‘yar mu’amalarsu ta tsahon lokacin nan ta soma rarrabe abubuwa. Ta fahimci ta so Khalipha so ba irin wannan da take yi a yanzu ba. So ne na rama halacci ga wanda ya yi maka alheri.
So ne wanda ba ta taba jin tana sha’awar hada jiki da Khalipha ba, zuciyarta ba ta taba rikicewa don ta ga Khalipha ba, ko don ya kalle ta. Amma shi wannan (Ya Himu) ….... ??? Ta girgiza kai.
Ba za ta iya fassara abubuwan da take ji a zuciya da gangar jikinta a kansa ba. Shine ke gigitata, shine ko magana ya yi mata ko ina a jikinta sai ya amsa. Shine bacin ransa ke kassarata ya sanyata kasa yin komai including barci da cin abinci dolen dan adam.
Shine mutum na farko da ya rungumeta ya hada da jikinsa da nata ya zuba mata wasu chemicals cikin bakinta da sassan jikinta gaba daya, da suka karkashe kwayoyin son Khalipha da birbishinsu daga kowane sako da kowanne lungu da kusurwa na jiki da zuciyarta.
Suka dasa wata bishiyar, wadda ta yi sauri ta fidda rassa da korran ganyayyaki suka yi girman da suka rufe kofar zuciyarta ruf, daga tunanin kowanne Da namiji cikin dan lokaci kadan, suka shimfida tasu katuwar dardumar suka zauna suka baje, suka yi kane-kane suka kankane ko ina, suka yi babakere a kowanne angle. (Kusurwa).
Wannan shine matsayin Ya Himun a yanzu da ba za ta iya fassara masa ba. Ba ta san kuma wata hanya da za ta bi ta nuna masa hakan ba. Ta yarda ya ci gaba da zargin nata da tone-tonen nasa in sha Allahu ta daina damuwa, in ba haka ba Himun so yake ya tarwatsa mata zuciya.
Sai ta soma nemawa kanta abin debe kewa don ta raba kanta da damuwa da fitinar Ibrahim, kawai sai ta dauko biro da exercise book ta ce
“Bari in fara RUBUTU!”
Sunan farko da ya fado mata a zuciyarta shine, bari in sawa littafin suna RAYUWAR RAYHANAH! Bari in rubuta labarin rayuwata tun daga kauye zuwa birni. Bari in bawa ‘yan’uwana mata da masu irin lalurata labarina ko sa sanyawa zuciyarsu hope da salama… (kada su fidda rai da rahamar Ubangiji (waraka) domin shine mai sanya cuta mai kuma yayeta a sanda ya so.
Babu wata cuta da aka saukar a bayan kasa ba tareda an saukar da ita tareda maganinta ba. Cuta lokaci daya take shiga, amma waraka sai lokacin da Allah YA so. Duk kudin ka duk mulkin ka, lafiya ta Allah ce.
Rai dai, baya rabuwa da rabo, saidai idan ya kare!
Cikin littafin nan ba zan manta da mutum biyu masu muhimmanci ga rayuwata ba. (DADDY) Dacta Mansur Balarabe Takai da Abdullahi Mansur Takai (YAYA KHALIPHA…..) ba zan manta da IYA BILKI ba, da ADO da ya yi sanadiyyar da na fito daga kauye har a yau na samu alfarmar zamantowa barin rayuwar YA HIMU na mallakeshi a matsayin MIJI NA.
Really it’s a blessing….. a mysterious miracle ba isa ta ce ba dabara ta ba......!!!
Watakila idan na rubuta yadda nake son YA HIMU zai fi fahimta ya yarda dani ya daina zargina a kan Yaya Khalipha........
Ya daina azabtar dani da fushinsa, wanda ya fi zafin bulala a dukkan jikina….......
Ba zan manta da Jawahir ba…. Ita ma MAMI ba zan taba mantawa da ita ba. Na yi mata uzuri sau (70) a bisa yadda rabuwar mu ta kasance, domin a da, ba haka take ba…. “
Haka ta yi ta rubutu tana tsiyayar da ruwan biro. Sallah da wanka, shan tea, cake da juice dake cikin firij a kicin dinsu kadai ke tada ita tsawon kwana uku.
Ta tattara Ibrahim da iyayen cefanensa ta watsar, ko tattasai daya ba ta taba ba. Daga baya ta fahimci ya samu kuku da mai gyaran gida duka Turawan Ohio ne. Taji yana kiransa Benjamin.
Idan ya gama girkin yana aje mata a dining ya kuma danna mata intercom ya sanar da ita, ‘to’ kawai take cewa, amma yadda ya aje haka yake daukar abinsa.
Ibrahim ya soma damuwa, me yarinyar nan take yi a daki tsayin kwana hudu ba ci ba sha? Kada fa yaje wani abu ya sameta, ga shi ta garkame kofa da mukulli ta ki cire shi daga jikin kofar.
Wai ita ma nan fushi ta yi kenan? Ban da ya damu da rashin cin abincin ta Allah sai dai ta yi ta gaji ta fito ko sati daya ne.
Dawowarsa kenan daga asibitinsu ko farar rigar likitocin dake jikinsa da abin wuyan sa bai cire ba ya doso dakin nata, da karfi yake bugawa sosai yana fadin
"Ba za ki bude ba Rayhanah?"
Banza ta yi da shi ta ci gaba da rubutunta. Tana fadi cikin ranta,
"Idan ka balla kofar ai taka ce ni ina ruwana?".
Bugun duniya Ibrahim ya yi amaryar ta ki budewa, har hannayensa sun fara zafi. sai ya juya ya nemo sikundireba da wuka ya zo yana kwance kofar. Ita dai ta ji dan sukur-sukur amma ba ta kawowa ranta kofar yake kwancewa ba.
Ibraheem so ya yi ya bata bahagon mari hagu da dama, amma a yadda ya risketan bisa study table tana ta rubutu sanye da belted- waist –shirt din da ya fara ganinta da ita a singapore, ta yiwa gashin kanta tufka mai kauri guda biyu ta makalesu da farin dutse (bead) ta zama kamar wani fure da mutum zai so daukewa ya gudu ko ba’a bashi ba, sai ya daskare a tsaye.
Rayhanah ta ji ya kwance kofar ya kuma shigo, amma juyowa wannan ba ta yi ba. Ya tabbatar ba za ta kalle shi ba, ba za ta yi mishi magana ba.
Sai ya tabbatar lallai fushin nata na gaske ne. Wace irin miskilar mata Allah ya hada shi da ita haka!
Allah sarki Doctor I.M Takai, komi nasa kwancewa ya yi ya kasa marin da ya shigo da niyyar yi, ya jingina da kofar sakamakon kafafunsa da suka ce; ba za su iya daukar nauyin gangar jikinsa ba.
Chapter 4 · 0% Book details