← Book details Rayuwar Rayhana Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 14

Sashe 6

Rayuwar Rayhana Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A fannin sittiru ba irin atamfar da ba ta daurawa in dai kalarta za ta amshi bakar fatarta ta haskakata, ba sai ta dubunnan nairori ba. Ta nairorin ma sau dubu sai ta zabi mai rangwamen kudi ta barta, in dai kalarta ta amshi fatar jikin ta, saboda sanin sirrin atamfa ajikin matar bahaushe, atamfa ko wacce iri ce kyau take indai a jikin Rahane ne. Kuma ita ce favourite regular attire dinta.
Wannan ita ce, RAYHANAH MATAR IBRAHEEM!!!
Wadda ba kyale-kyale ne ke fizgar hankalin mijinta a kanta ba. Tsafta ce, da gyara. Don ko jambaki, bai taba gani a lebban Rayhanah ba, sai Avon lip Gloss.

A tsayin mintunan da Ibrahim ya diba yana bambance kamanni, halaye da dabi’un matar tasa, sai ya yardarwa kansa cewa wannan ita ce MATAR DA YA KE MAFARKI; mai kyakkyawa kuma sassaukan gayu na hankali da tunani, kuma ‘yar bokon data yiwa boko kyakkyawar fassara, though she's not wealthy but she has a great mind! Ba kamar yadda mata da yawa suka jahilci kalmomin guda biyu ba.

Turawa da larabawa da yawa kudinsu suke sanyawa suna sayen (Zaitun) don su rage hasken fatarsu. Black is beauty! And there's nothing worth respecting like naturalism!!! Fari ba shine kadai kyau ba, balle wanda akasa kudi aka sayo.
Mata da yawa sun gama amincewa cewa yin shampoo (kona gashi) da karin gashi, sanya tsadaddar suttura ta almubazzaranci ko mai zahirantar da tsiraici a wuce ana barbadawa duniya kamshi. A sanya dankwala-dankwalan ‘yan kunnaye, a lambata jambaki shine kwalliya ta wayewa da burgewa…. To ba shi bane a ra’ayin RAYHANAH RASHID TAKAI.
******

Da wannan Ibrahim ya sauke idonshi a kan Rayhanah, sai ya ga ta yi barci tana numfashi cikin nutsuwa, baccin da ba na komai bane face na wahala da azabar da ya gana mata. Shima da ya duba aika-aikar da ya yi mata sai ya ji kwalla ta ciko idanunsa.
Ya kasa sakinta, ya kasa aikata komai a kanshi ko a kanta, yana jarumtakar maida hawayensa amma sun ki hakan, sai da suka mirgina cikin gashin Rayhanah. Ya kankameta sosai.
Sauran abubuwan da yake tattaunawa cikin zuciyarsa na auratayyar da yayi a yau da Rayhanah, kuma al’amari na farko a tsayin rayuwarsa, da matsayin da hakan ya karamata a zuciyar sa, daga shi sai Ubangijinsa suka sani.
Shi da kansa ya fiddo kayan aiki da baka rasa likita da su a gida, don ya tabbata sai ya yi mata stitches, ya ji mata rauni sosai da hakan ya sa shi challenging (kalubalantar) kansa da selfishness (son kai) da rashin tausayi.
Bai san kuma ya zai yi ya yi mata ba tareda ta tashi daga barcin hutun da baya son ya rabata da shi ba. Sai ya maida ta kan sofa dake gefe ya yi mata allurar da ta karawa barcinta nauyi, sannan ne ya yi, ya gyara komai ya canza shimfidar gadon.
Ya yi wanka ya fita dining don ganin abin da Benjamin ya girka. Ya kai hannu ya bubbude dishes din yana gani; Lemon Ricotta, Pancakes with syrup, Quinoa, Poached-eggs, Sliced bacon, Sliced bread with jam. Abinda Benjamin ya shirya musu a dining kenan matsayin karin kumallo.
Yasa murya ya ce,
“Benjamin!”
Daga can kicin Benjamin ya amsa ya fito da hanzarinsa hannunsa rike da wuka da farar albasa katuwa. Ya ce,
“Jeka maza ka yo min farfesun salmon (kifi) easy chicken recipe da omelets ya isa, ina son su in ten minutes”.
Benjamin ya amsa cike da girmamawa ya koma ya fara aikin.
Minti uku ya kara akai daga mintunan da ubangidansa ya ba shi, ya jero a tray cikin ‘yan kananan bowls din karau (tangaran) zai soma jerawa a dining bayan ya kwashe wadancan maigidan nasa ya fito daga corridor din da zai sadaka da dakinsa yana sanye da farar shirt DKNY an rubuta DKNY din da ruwan kasar zare da dogon (brown jeans) ya debi wanka ya sharce gashin nan nasa da kumfar Arganavita. Shaidar sujjadarsa ta fito sosai a karshen goshinsa.
Ga mamakin Benjamin isowa ya yi gareshi da kansa ya karbi katon tray din ya sallame shi. Har sanda ya shiga bedroom din nata da abincin ba ta tashi daga nannauyan barcin da ya tsikara mata allura don ta yi ta yin shi ba.
Shima bai bi ta kan abincin ba computer ya kunna yana ci gaba da hidimar da ta kawo shi ta yanar gizo.
Ba wani abu ne ya kawo shi ba face tattara ajiyarsa da ke manyan bankunan Amurka daban-daban irin su J.P Morgan Chase, HSBC, U.S Bancorp, Morgan Stenly, Wells Fargo Don komawa gida kwata-kwata.
Gidan da yake ciki wanda mallakinsa ne kadai zai bari a Amurka ba zai sayar ba.
Jefi-jefi ya kan daga kai ya kallo Rayhanah wadda ta soma gyara kwanciya, sai ya sunkuya ya ci gaba da abin da yake yi. Yau jin kansa yake sakayau, kamar an sake haifo shi duniyar ne, new IBRHEEM! Babu nauyin komai cikin jikinsa da kwakwalwarsa har ma da zuciyarsa, sai abubuwan da zai loda musu yanzu. Duk wasu tensions sun fita.
Wanda ya tabbatarwa kansa ba komai ne ya haifar masa da wannan nutsuwar ba face rahamar dake cikin aure, da tarin lada da gafarar da Ubangiji ya sanya a cikinsa.
Daga lokacin da ka daura hannu a jikin matarka ta sunnah dukkan alhakin da ka dauka a rayuwarka na zina ko makamancin hakan Ubangiji ya juya shi zuwa abundant reward wanda shi kadai ya san adadinsa.
Juyi ta yi cikin gyara kwanciya kafin ta soma magana cikin gigin barci ne ko na allurar barci ne bai sani ba…..
“Ya Himu….. Ya Himu .... don Allah ka yi hakuri, na tuba na bi Allah na bika….Baba Dacta ka ceceni zai kasheni....!”.
Kalaman da take furtawa kenan wadanda a jiya ya hanata furtawa, sai yanzu suka samu sarari suke sakin kansu cikin magagin barci. Wadanda suka sa Ibrahim Takai, cikin wani hali mai kama da nadama, bai so al’amarin ya zo masa all of a sudden haka ba, amma ba regretting yake yi ba, tunda in a wajen Ubangiji ne baida wani laifi.
Shi Ya ce ku zowa matanku a duk lokacin da kuka so ko da suna a halin nakuda. Matanku gonakinku ne, ku zo musu a duk lokacin da kuka ga dama idan ba haila, ko nifasi suke yi ba.
Yadda bai yi tunanin cutuwarta ba sai na shi biyan bukatar shine abinda yake regretting, to shi kansa bai san yadda zai yi da kansa ba, samartakar, tashen balagar da tuzurancin ya hada duka ya saukewa Rayhanah a lokaci daya. Adadin kaunarka ga matarka, adadin karfin sha’awarka a kanta.
Sai dai ya yarda ya yi laifi, dole ya yi lallashi harma da banbadanci, in ma bai iya ba yanzun nan zai shiga makarantar soyayyah ya koyo. Ture laptop din ya yi, ya mike ya shige cikin bargon nata, ya mika hannu ya janyota gareshi.
Ai sai ta soma kokarin kwacewa tana rokonsa tana magiya cikin kuka, gabadaya ta gama tsorata da shi. Ko ganinsa bata son yi. Karfi yasa sosai ya riketa. Har tasoma gajiya da kokawar ta, jikinta yayi sanyi lakwas.

“Ka taba kashe abin da ka fi so a duniya RAYHANAH???”

Yadda ya yi maganar cikin sanyi, tarin so da kauna da kulawa, sai ta daina kokawar kwatar kan nata.
“Rayhanah idan ka kashe shi kai da wa za ka zauna? Wajen wa za ka je ka sauke son nashi da ya yi maka babakare a zuciya?
Ina rokon Allah ya kasheni ya barki, ki yiwa ‘ya’yana tarbiyya irin taki.
Madallah….. da shigowarki cikin rayuwata….. Maadallah... da Uba irin Babanki Dr. MANSUR. Mai so na da ALHERI..... da dimbin kauna mai yawa agareni. INA SONKI RAYHANAH! INA SONKI RAYHAH!! RAYHANAH I so much love you!!!.”
[12/29/2019, 19:10] Takori: Sai ta daga kai a hankali don ganin daga bakin da wadannan zakakan kalmomin ke fitowa, da babu wanda ya taba gaya mata kwatankwacinsu a zaki da gardi? Tana tababar ya zamo cewa daga bakin Ya Himu ne…. wanda in ya ganta bai iya cin abinci.
Fuskar da ta gani cikin hasken safiyar da ya keto fararen curtains din dakin barcin, ya fi gaban a kirashi Ya Himu.
Cikakken likitan Koda ne Dr. Ibrahim Mansur Balarabe Sardauna, mai matsayin (Nephrology Consultant) a babban asibitin Illinois, ba dan matashin dalibin nan mai girman kai da kwalisa a AKTH da gidan Dacta Mansur ba.
Wannan fuskarsa cike take da gargasa lallausa, da tarin hankalin da shekaru suka taimaka wajen karuwarsa. Idan aka kira shi Dr. Ibrahim Mansur Takai, zai fi dacewa da shi fiye da a kira shi Ya Himu.
Chapter 6 · 0% Book details