← Book details Rayuwar Rayhana Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 14

Sashe 11

Rayuwar Rayhana Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Har kuma zuwa inda yau ke motsi, daga Daddy har ita babu wanda ya yarda koda cikin raha ko subutar baki ya gayamasa dalilin fasa auren Rayha da Khalipha. Saidai su ce
“Allah bai yi ba!”.
Eh, gaskiya ne komai sai Allah ya yarda, amma babu abinda ke faruwa a duniya babu dalili.
Sai ya ji jikinshi ya yi sanyi, mai daki shi ya san inda yake masa yoyo. Zuciyar Rayhanah mai kyau ce, ba za ta fadi sharri ko batanci haka kawai a kan kowa ba, balle a kan uwar da ta haife shi.
Tukunna ma, shi shekarunsa nawa baya tare da su? Ya san irin rayuwar da suka yi cikin tsayin shekarun ne?
Da wannan tunanin ya mika hannu ya rungumo matarsa, ya kwantar da kai a kafadunta, zuciyarshi cike da nadamar saurin kai hannunshi ga lafiyar jikin wadda ta ba shi farin cikin rayuwar da bai taba tsintar kansa a ciki ba. A kuma ranar da ta ba shi farin cikin ko hutawa ba ta yi ba.
Jinta gaba daya jikin Ibrahim kamshin jikinsa na ratsata sai ta idasa narkewa, hawayen suka kara shimfidowa a kan kundukukinta.
“Ki yafe ni Rayhanah, kin yafe min Rayhanah?”
Ta daga kai….
“A’a, wannan bai gamsar dani ba, bude bakinki ki gaya mini….”
Ya fada a lokacin da ya dago habarta. Sai ya soma dauke hawayen da harshensa. Runtse ido ta yi, amma jin Ibrahim na neman zafafa al’amarin sai ta kwace.
“Malam yi a hankali, dinkin likita ce”.
Ibrahim yasa dariya ya sake kamo ta.
“Ba sai a sake dinkewa ba???”

Ya fada da muryar da ta gaya mishi hakan shekaru biyu a baya. A take ta tuno da first night dinsu. Ta juya masa keya cikin jin kunya tana jijjiga babyn.
Ibrahim ya sake binta ya ce,
“Ko kwaryar ba masaka tsinke ne inda za a sake soka allurar?”
‘Yar ta aje cikin ‘yar katifarta, ta dau filo ta danne shi tana bugu. Sai ya hantsilota ya koma samanta ya mamayeta yadda ko motsi ba za ta iya ba. Cikin dariya da shaukin bege mai yawa ya ce,
“Wallahi ki bini a hankali, in ba haka ba wannan dinkin farkashi zan yi yanzu”.
Ganin ya soma zarce Zaria ta soma lallashi, wanda ba ta san yaushe ta iya ba, har da su dadin baki, kirari da bambadanci.
“Haba dan Ibro na…. angon Rayhanah Baban Asma’u….. dan gaban goshin Baba Dacta.....likitan likitocin kodar Rayhanah......” Ibrahim dariya yayi yace
“har kin tunomin da Ado, oh su Rahane da yanzu fa anada ‘ya’ya goma” ta shaka tayi fus, kamar alkubus. A ranta tace “yanzunnan zan rama”.
“Ai dai duk da kaki bani shayin da Baba Dacta yace ka bani, ka turo inyamuri ya bani, kuma arzikin kalma ko ta sannu ce ban taba samu ba, na ganka kana mazari kana tsuma kana gwada ‘yar kashi da Adon don yana kokarin shimfidar ni.....”
Inda abin da ya tsana a tayar ko a tuna masa a duniya to wannan zancen ne. Ai kuwa a take ya koma serious. Fuskarsa tayi kicin-kicin kamar ba shi yake rahar da yake yi yanzun ba.
“Rayhanah zamu bata, uwar Asma’u zamu bata……”
“Na tuba….. na bi Allah na bika Baban Asma’u. I’m in nostalgia (ina cikin begen gida)”.
“Nima gidan nake so Rayhanah, amma bari Mamina ta yi dan kwari zuwa watanni biyar haka”.
Har cikin ranta ta gamsu da hakan.
******

WELCOME TO THE WORLD ASMA’U IBRAHEEM MANSUR

Rubutun da za ka fara cin karo da shi kenan a kasan tangamemen hoton da za ka fara cin karo da shi da zarar ka shigo falon nasu, mai kama da fadar wani gwamnan a Nigeria.
Uwar da Uban ne cikin ‘Native Hausa Attire (shadda da Atamfa) shi dinkin Mohammed na shudiyar shadda sheraton da hula Damanga shudiya mai duhu, sun sa buleliyar ‘yar tasu a tsakaninsu kowa ya rungumo bari daya, wadda ta washe ta yi haske ta zama kamar ‘yar Sudanese, dukkansu bakinsu a washe, fararen hakoransu a warwaje kamar masu tallan colgate. Itama ‘yar bakinta kamar ya tsage da dariya, cleft da beauty point din Mami da Ibrahim duk sun lotsa.
Hoto ne wanda Ibrahim ya turawa Baba Dacta copy dinsa cikin wayarsa, ta hanyar BlackBerry Messenger. A lokacin yana kan hanyar komawa gida daga wajen aiki.
Ya ji shigowar hoton amma bai bude ba, sai da ya shiga get Mal. Dahiru ya rufe ya adana motar a rumfar adana motocinsu.
Ya dauko kwat dinsa da bakar jakarsa tukunna ya bude. Sai da ya jingina da motar kada kafafunshi su kada shi. Kwallar farin ciki ta tsiyayo daga idanun Dr. Mansur. Ya tsura musu ido dukkansu ukun kamar ya hadiyesu don kauna.

Wannan rana yake jira, ya maidawa Asma’u martanin bakin cikin da ta kunsa masa shekaru uku da suka wuce. Ai bai shiga gidan ba, mota ya koma duk da gajiyar dake jikinsa ya sake fitowa ya nufi Arewa Studio dake Tarauni ya basu suyi mishi window size guda biyar zai dawo gobe ya amsa, bayan ya biyasu.
Wani abin mamaki a washegari bayan ya karbo hoton sai ya dasa a falonsu, daya a bed-room dinsa, daya a dakin su Abida, a lokacin duk basa nan. Jawahir tana Hurghada, Mimtaz ta sake haihuwar da namiji again. Mami na office, Abida da Aziza suna makaranta.
Bayan ya kakkafa enlargements din ya yi tafiyarsa office dinsa da nasa copy din da zai sa a office dinsa, zuciyarsa kal kamar madara. Duk inda ya gitta cikin ward din su an san Dr. Takai yau yana cikin farin ciki. Sai raha yake yi da likitocin da ke karkashinsa da marasa lafiyansa.
Dr. Kofar Mata ya kasa shiru ya ce, “Wai Dr. Mansur hala amarya ka yiwa Dr. Ma’u?”
Bakin Dr. Mansur har kunne ya ce, “Eh, kamar ka sani kuwa wallahi Dr. K/Mata, gata”.
Ya mika masa hoton da ya yi saving a fuskar wayarsa.
“Zo muje office ka ga amaryar tawa sosai”.
Ai kuwa ya mike ya bishi office ya nuna masa tangamemen hoton. Dr. K/Mata kamar yau bai ci abinci ba, haka ya bude baki yana ta kallon hoton.
Ya ce,
“Wannan kamar Ibraheem, ‘yar kamar Asma’u, matar ce ban sani ba”.
Murmushi ya yi ya ce,
“Ita ma ‘yata ce, ni nake rikon ta”.
Dr. K/Mata ya ce, “Masha Allahu, Allah ya albarkaci little Asma’u ya rayata cikin tafarkin Islama, amma ban san sanda Ibraheem ya yi aure ba”.
“Auren ne ya zo a kurace, amma abu wajen shekara uku”.
Haka suka yi ta zancen Ibrahim da iyalinsa, suka manta da patients dinsu.

A take Daddy ya turawa Hakimi da Haj. Karima da Inna Juma, wadda ba ta yarda ta zauna a Farm Center ita kadai ba, tana gidan Hakimi, can aka ba ta daki take zaune. A take kuwa suka hau kiran wayar Dacta suna neman karin bayani, baki har kunne Daddyn ke amsa musu.
Tafi-tafi zance ya yadu cikin gidan Hakimi da wajensa Ibrahim matarshi ta haihu, ‘ya kamar Asma’u. Wannan kadai ya isheta aya, idan fa har tana da hankalin tsinkayen hakan kenan.
Abida da Aziza ne suka fara dawowa gidan a gajiye tubis, suka baje a falo suka kure A.C. Kamar an ce da Aziza daga kanki ta yi arba da tangamemen hoton, ta hau zubawa Abida duka a cinya.
“Yaya Abida….. Yaya Abida ....sister…. Sister kin ga… kin ga”.
Abida ta juyo a fusace domin har ta samu barcin gajiya ya sureta Aziza ta katse mata. Tana niyyar mangare Azizah sai ta ji tana fadin.
“Kamar Ya Himu da RAYHANAH da ‘Cute Baby!”.
Abida ta daga ido ta kalli side din. Ai da sauri suka mike dukkaninsu suka runtuma ga hoton suna kallo sosai. Iyakar rikicewa da firgita Abida ta yi.
A take ta ja waya ta kira Mami.
“Mami ki taho gida maza – maza yanzu ki ga wani abin mamaki”.
“Mene ne?”
Ta fada da dan karfi.
“Ke dai ki taho Mami za ki sha mamaki, idan fa har baki suma ba”.
Ta kashe wayar ta kyale Mami.
Chapter 11 · 0% Book details