← Book details Rayuwar Rayhana Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 14

Sashe 2

Rayuwar Rayhana Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

RAYHANAH A CHICAGO
Sanda suka sauka a babban filin jirgin saman Chicago ruwan sama ake yi kamar da bakin kwarya. Kalma wannan bata shiga tsakanin Ibraheem da Rayhanah ba.
Domin dai har zuwa lokacin zuciyar Rayhanah ba ta yi sanyi ba da wannan yankan kauna da Ibraheem ya yiwa karatun ta, karatun da ta sha bakar wuya a kanshi, ta kuma ciwa buri mai yawa. Rahane ta dauki wannan karatun matsayin madafar rayuwarta ta wata rana.
A kullum tana tuna maganganun Babanta ne da ya ce, ta yi kokari ta dinga tunawa a ko’ina ta tsinci kanta, ita ba kowa ba ce.... ba ‘yar kowa ba.... ba ‘yar kowan-kowa ba....face talaka ‘yar talaka. Jikar talaka. Tayi kokari ta tsaya da kafafunta. Kuma kar ta zurfafa buri.
Don haka wannan karatun shikadai ne burinta a rayuwa.
Tana da burin zuzzurfan ilimi domin cin gajiyarsa wata rana, tunda su ma su Daddyn alfarmar ilimin suke ta ci har su ma suka samu suka rabesu ana ci tare da su.
Har yau zuciyarta ta gaza sallamawa zuwa ga karbar Ibraheem matsayin mijinta balle wani matsayi na soyayya ko akasinta a gareshi gaba daya.....domin a ganinta ya fi karfinta, ta dai yi kokari ta cire Yaya Khalipha a ranta, amma ta kasa cike gurbin da Ibraheem.
Rahane ba ta gama firgita da al’amarin Ibrahim din ba sai da ya sanya mukulli ya bude wani American-Villa suka shiga har ciki da motar asibitin (Illinois) wadda ta kwaso su daga airport da chauffeur guda, mota ta alfarma da bata taba shiga irin ta ba ko a Singapore.
Gajiyar dake tare da ita ba ta hanata fara yin sallah ba sannan ne ta ji ta sakayau. Ibrahim na waje da makotansa mutanen Sri Lanka suna yi mishi barka da zuwa, kafin ya sallamesu ya shigo Rayhanah ta yi barci a falon cikin kujera da kayan jikinta ba ta nemi ko da bed-room ba.
Ya dade tsaye a kanta hannunshi cikin aljihun dogon wandon Armani dake jikinsa da bakar rigar sanyi mai kauri, a yadda ta yi kwanciyar, za ka fahimci sanyi take ji, ta cure ta dunkule jikinta cikin gyalenta wanda ba wani kauri ne da shi ba.
Kallon ta kawai yake al’amuran da suka shude shekaru goma sha biyu a baya na dawo mai filla-filla. Yarinya mai yawan jin kan mahaifi, da nuna mishi sadaukarwa. Mai hakuri da Abida, da rashin mutuncin ta. Mai son Azizah da yin biyayya ga Mami.
A saninsa Mami na son yarinyar, amma me yasa ta hana aurenta da Khalipha? Zuciyarshi ta yi saurin halarto da amsa (saboda wani baya auren matar wani). Shi mijin aure tun ranar da aka haifeka aka rubuta maka shi a allon da baya kankaruwa (Lauhul-Mahfuz).
Khalipha fari sol mai kyawun da za a likashi a goshi, me yasa yake son Rayhanah? Baka..... not so much attractive...... Ba kowane namiji ne ya san darajar mata irin Rahane ba, sai su likitoci da suka san amfanin kowacce gaba da aikin kowacce halitta ta dan Adam.
Wannan Rahanen, ya sha matukar wahala kamin ya manta da ita da al’amarinta bayan barowarsa gida.
[12/28/2019, 12:34] Takori: ‘She’s that something which goes far beyond mere or casual assumption!’ Da ya yakice yayi fata-fata da shi daga zuciyarsa a isowar sa Chicago, wato shekaru goma sha biyu a baya kada ya zamo hindrance ko obstacle ga cigaban rayuwar sa da kyakkawan kudurin da ya fito da shi daga gida.
Dadin dadawa a lokacin ya kalubalanci kansa kan damuwa da al’amarin ta da cewa tausayi ne kawai. Me take da shi da za’a so ta akan shi a lokacin banda deficiencies and inefficiencies? (Tarin nakasu).
A tsarin halitta da dabi’a (personality) irinta yake burin samu.
Abin nufi, baya son macen data cika kyau, baya son farar mace, baka yakeso ‘yar uwarsa, baya son mace mai kyale-kyale da artificial beauty, baya son wadda ta waye da yawa, baya son mai budadden ido, baya son wadda suka hada alakar jini, baya son yar masu kudi ko masu mulki duk da baya son ‘yar talakawa likis.
Ya sani ba wanda ke samun rayuwa ko abokin rayuwa 100%da burinsa. Don haka zai iya cewa ya samu Rayhanah 80% da burin da ya dade yana ciwa abokiyar rayuwar sa.
Da yake Allah ya rubuta matarshi ce ga shi ya biyoshi da ita har inda yake. Ba da yunkurin shi ba, ba da motsin sa ba, ko wani kokarin sa. Sai don kasancewar al’amarin su rubutaccen al’amari.

Sai dai har yanzu ba zai iya sakin jiki da Rahane ba, ba don komai ba sai don cewa.... bai yarda da akwai soyayyarsa a zuciyarta ko da digo daya ba, kawai dai an fi karfinta ne ita kuma ta yi biyayya......
Amma Khalipha take so, tunda har maganar aure ta shiga tsakaninsu. Allah kadai ya san irin soyayyar da suka yi kafin zancen aure ya shigo ciki.
In haka ne ta yi kadan ya mika mata dimbin soyayyar da ya tanadarwa matarsa alhalin ita ba son shi take yi ba. Sai dai ya yi mamakin yadda ya kasa sarrafa kansa a kanta the very first day of their encounter....(rana ta farko da haduwarsu) har kuma yanzu haka abin yake, amma zuciyarshi na ta karyatawa da kalubalantar hakan da gangan.
Haka ya ci gaba da tsayuwa yana kallon ta yana kissima abubuwa da yawa..... zuciyarshi na azabtar da shi a kan tunani mara tushe da makama (kishi akan abinda bai gani ba).
Motsi ta yi don ta gyara rufarta, sai ta ji alamun tsayuwar mutum a kanta, ta bude idanunta a hankali sai cikin na Yayan, idanunta sunyi kalar da ba zai iya jurewa kallon cikinsu ba tare da ya kara karyata kansa ba.
Don haka shi ya fara dauke idonsa da hanzari ya wuce bed room ya sakarwa kanshi shower. Sanda ya fito falon cikin shiri ne na bakaken suit da jibgegiyar rigar sanyi, kanshi babu hula, sumar nan ta yi luf a kanshi har sheki take na alamar ta kara ganin ‘ArganaVita’.
Nan ya taddata inda ya barta a yadda ya barta. Haushi ya tokareshi bai san cewa ita ma haushin nasa take ji ba.
Don haka yana hararar ta ita ma tana dan harararsa da karshen idanunta, ta yi kicin-kicin da fuska duk sai ta bashi dariya.
Ya girgiza kai ya ce,
“Ni kike harara ko Rayhanah?”
Ta zumburo mishi ‘yan tausasan lebbanta gaba, abinda Ibrahim baya iya jurewa gani kenan (those luscious lips) ba tareda ya karya ta kansa ba, don haka ya yi sauri ya kawar da kansa.
“Dube ki da Allah ba wanka ba sallah kina ta shirgar barci, to wallahi ba zan dau wannan ba. Nan ba Inna ba Daddy sai in yi kuli-kulin-kubra dake ba wanda zai cece ki. Mintuna ashirin na baki kafin in dawo in ganki yadda na soma ganinki, in ba haka ba, na rantse..... ni dake ne a gidan nan.......”
Ya sa kai ya fita. Ta bishi da kallo tana mamaki tana harararsa. Mamakin da take yi shine, yadda duk ta zaci al’amarin ba haka ya zo ba, ta dauki Ibrahim din tuntuni a wani mutum mai raini da wulakanci.
Ba za ta taba manta labarin data ji Daddy na baiwa Inna Jumah ba a (farm-center) suna hira ne inda yake gaya mata dalilina na hada auren Rayhanah da Ibrahim shine halayen Ibrahim duk irin na Rayhanah ne wato miskilanci don haka yake da tabbacin zasu ji dadin zama da juna, yana bata labarin ranar data bude idanunta daga hatsarin da sukayi ita da Iya.
Daddy ya ce ya ba ta tea ta sha a AKTH ya yi baya ya buya ya tura Eric Epatobe wani abokin karatunsa baisan cewa Daddy na ganin sa ba.
Tana kuma iya tuna ranar da Abida ta kifa mata pampas na kashin Aziza a fuska ya zo ya gani bai ce komi ba, bai nuna komi ba, bai wa Abida koda fada ba. Sai YAYA KHALIFA ne yayi hakan.
Tun zuwanta gidansu kafin ya bar gidan, kalma wannan koda ta gaisuwa ce bata taba hadasu ba. Tun daga lokacin ta bawa Himu matsayin wani mutum mara kirki.
Don haka ne fuskar da ya karbeta da ita a Singapore ta bata mamaki kwarai, ta kuma sanyata cikin shakku, akan tunaninta na baya a kansa.
A ranar da ya ganta matsayin matarshi a ranar ya hada jikinsa da nata, ya yi mata sumba mai tsayawa a zuci, ba tare da ta yi wani abu don ta ja hankalinsa ba. Ba za ka taba yin hakan ga macen da kake kyankyami ko baka so ba.
Wannan ya nuna cewa Ibrahim ya karbeta a matsayin mata ba don kyale-kyalenta ko wani abu special data ke da shi ba.
Wannan tunanin da ta yi yanzun, sai ta ji haushin nasa da take ji na rabata da Informatics yana decreasing a hankali cikin zuciyarta. Zuciyarta ta ci gaba da yin sanyi, jikinta ya yi la’asar.
Ta samu kanta da mikewa don cika umarninsa. Ba don tsoron kuli-kulin kubrar da yace zai yi da ita ba.
A’ah, sai don wani kima da daraja har ma da martaba da ya kara a idaniyarta. Yanzu ma taunar gefen gyalenta take cike da tunani da bege mai yawa dake mamayar ta.

Duka kofofin guda hudu dake cikin babban falo a rufe suke da mukulli, sai daki daya wanda ya fito daga cikinsa kenan, kuma can ta ga kayanta a kan gadon dakin.
Cikin nauyin ido da nauyin zuciya Rayhanah ta daga ido tana karewa cikin dakin Ibrahim kallo. Daki ne sosai irin na manyan proffessionals din Amurka, babu tarkace ko kankani.
Komai yana ma’adanarsa, na’urori da yawa bata san na menene ba duk da sunfi kama da computer ta san ba duka ne computer ba, sassanyan kamshi ke tashi na room fresh din rasp-berry.
Dakin da dumi yake sosai, na’urar dumama daki na aiki. Tun ganin ta dashi a Singapore taji tana so ta san menene sirrin gayun Ibraheem? Don ita dai a kafatanin rayuwarta bata taba ganin mutum irinsa ba (mind blower!).
Ashe amsarta tana toilet da ta rage kayan jikinta ta shiga don yin wanka.
Chapter 2 · 0% Book details