Sashe 1
Rayuwar Rayhana Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read
[12/27/2019, 17:59] Takori: RAYUWAR RAYHANAH 4
Duk da rashin barcin da ta samu jiya a tsayin daren baki dayansa, hakan bai hanata yin wanka karfe bakwai na safe ba, ta yi sallah ta kintsa, ta zo wajen saka kaya ta rasa wadanda ya dace ta saka. Sai ta tuna da maganar Inna jiya cewa ta yi kwalliyarta da atamfa.
Idanunta duk sun tasa sunyi ja cike da nauyin barci, domin dai shi ba a cin bashinsa a zauna lafiya.
A ranar ma test za ta yi, amma ko Alifun ba ta karanta ba, inda Allah ya taimaketa ma practical test ce (gwaji na aikace).
Karfe goma na safe suka gama ta nufo gida. Daga informatics institute zuwa gidansu babu nisa da kafarta take takowa kullum. Atamfa ce exclusive fara tas a jikinta mai ratsin shudi da ruwan goro, ta yafa mayafi ruwan goro mai girma da ka ganta ka ga cikakkiyar Nigerian.
Ganin motar su ya tabbatar mata sun shigo gidan. Sai ta rage sauri cike da jin nauyin, da wace fuska za ta dubi Daddy a yau, Ibrahim da ya haifa yana aiwatar da wadannan al’amura masu tsaurin fada a gareta? Wato sumbatar ko’ina a tareda ita? Wannan babban tashin hankaline a gareta.
Ba Daddy kadai ba, shi kansa Ibraheem din ba ta jin za ta iya hada ido da shi. Don haka take tafiya sannu-sannu, kafafunta babu kwari. Da ta iso kofar shiga gidan, sai ta kasa danna bell ta yi zamanta a kan wani ginannen verse din fulawa dake bakin kofar shiga falon nata, tana tauna gefen mayafinta da fararen hakoranta.
Wajen mintina ashirin da zamanta kofar ta bude. Inna ta fito da katuwar jakar kayanta za ta sanya a mota.
Gaban Rayhanah ya yi mugun faduwa, kar dai Ibrahim da gaske yake rabata zai yi da Singapore? After one year and a half of dedication, struggle and endeavor?
Inna ta ankara da ita a zaune ta yi salati ta yi sallallami.
“Yanzu daman kin dawo tun dazu kika zauna a nan? Rahane yaushe za ki bar kauyancin ki? Ko ni tsohuwa ba zan yiwa mijina abin da kikewa Ibraheemu ba. To kai Ibrahim fito ka dauke ta ka shiga da ita gidan.... tunda bazata iya shiga ba.”
Ai da jin haka ta zabura ta mike ta danna kai falon, idanunta basu sauka a ko’ina ba sai cikin lumsassun idon Ibraheem, wanda ke nutse cikin kushin, kafafunshi mike a kan tebirin glass mai garai-garai dake tsakiyar falon. Yana sanye da wasu shudayen Tommy hilfiger, masu ratsin ruwan toka da ruwan tokar safa a kafafunsa.
Kallon ta ya yi na minti biyu, sai ya mai da kansa a jaridar dake hannunsa. Sai ta shige bayan labule wai tana gaida Baba Dacta shi ba ma ya jiyowa sosai.
Yasa dariya ga dukkan alamu yau cikin matsanancin nishadi yake, da tabbataccen kwanciyar hankali, ya ce,
“An Rahanen Inna yau sai Chicago, Inna sai TAKAI!”
Ai ba ta san lokacin da ta fito daga labulen ba ta zazzaro ido. Ya girgiza kai yana dariya.
“Ni dai Ibraheem ka warware wannan firraqun da ka yi min da ‘yata, tunda ka zo ban ga hakorinta ba sai razana cikin fararen idanunta. Zo nan Rayhanah, daure ki zo kada ki sa in yi fushi da zuwan Ibraheem.....’’
Ta lallabo da rarrafe ta zauna gefen kujerar da yake zaune. Ya ce,
“Yaushe za ki kare test kuma yaushe zaku fara exams?”
A hankali ta ce,
“Mun gama test..... 1st April zamu fara exams ”.
Ya ce, “Masha Allahu, mu zamu wuce gida Inna za ta Takai da Albasu ta ga dangi sannan ta dawo gidanku (Farm Center) kafin ku dawo.
Za ku wuce Chicago, Ibrahim ya gama kammale-kammalen sa ya dawo gida baki daya.
Kafin nan za a san yadda za a yi a kan karatun ki, ai za ki raka shi ko?”
Idanunta narai-narai da hawaye ba tareda kwana ba ko sakayawa kai tsaye ta ce,
“A’ah”.
Hatta Inna ranta bai yi mata dadi ba da amsar Rayhanah, balle Ibraheem. Shi kuwa Dr. murmushi ya,
“Why?” (Me yasa).
Ba ta kalli inda Ibraheem din yake ba wanda ta tabbata idonshi na kanta, kunnensa na sauraron amsar da za ta bada.
A sanyaya tace.
“Na fi son na kammala karatun gaba daya mu koma gida kwata-kwata, ina son karatun Daddy, kuma na sha wahala a kansa, sannan na ci karfinsa”.
Inna ta yi tsagal cikin takaici ta ce,
“Amma ke kadai za ki zauna ko, ki auri karatu? Wallahi ba zan zauna ba, na gaji da zama cikin jajayen kunnen nan da basu san Allah basu san Annabi ba, ko kiran sallah babu, sai dai a duba agogo. Ban da wuyanki ya fara kauri yau Babanki ne zai yi umarni ki ce masa a’ah?”
Ran Inna Juma ya baci sosai, sai fada take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Babu wanda ya ce uffan sai da Rahanen ta fara kuka.
Daddy ya ce,
“Inna yi hakuri, tana da ‘yar gaskiyarta.......”
“Ina wata gaskiya a nan? Boko ya fi aure? To ba dani ba, kinga tafiyata, wallahi ko kwana daya ba zan kara a garin nan ba”.
Ta kinkimi sauran kayan ta yi waje. Ibrahim ya mike ya ajiye jaridar a kujerar, ya shiga bed room din Rahanen ya bude cupboard ya soma diban wasu daga cikin kayanta.
Karfe daya na rana za su tashi zuwa Chicago a ‘American Airlines’ daga ‘Changi Airport,’ yayin da Inna da Baba Dacta za su wuce gida Nigeria.
Daddy ke lallshinta ba da fada ba,
“Ki gane Rayhanatu aure yana gaba da komai, wannan karatun ma da kike yi ai na debe kewa ne kawai saboda rashin sanin ranar da Allah zai kawo mijinki.
Don haka bai ma da amfani yanzu, ko da can da nake yin kan gaban kaina a kanki, a bisa rashin mijinki ne.
To ga shi ya zo, ragamar al’amuran rayuwarki ta fita daga hannuna tana gareshi, shi ya ce zai tafi dake ba zai barki a nan ba, don ba shi da abin yi a nan, bai ma taba zuwa ba. Rahane ke kinga dacewar ke kina wata kasa mijinki yana wata kasa babu wani kwakkwaran dalili?”
Ta girgiza kai tana share hawaye jikinta ya soma sanyi. Ya cigaba.
“To kin gani. Wani hanin ga Allah baiwa ne, da kanshi in kin kwantar da hankalinki zai nema miki makaranta a duk inda kuke, Ibraheem is a nice person.... Allah ba kwarzanta shi nake yi ba. Wata rana ke da kanki za ki gaya min hakan, lokacin da zai sunkuya yana yi muku ‘doki-sukutum’ ke da yaran ku!”.
Ta boye fuskarta cikin gyalenta tana dariya. Dai-dai lokacin da ya fito yana tura dirkekiyar troller dinta, kaya da yawa ya barsu duk da amfaninsu sabida ba zai iya kwasar duka ba sai wadanda suka zama dole.
Haka ya wuce su bai san me sukewa dariya ba. A ransa yana fadin
“Daddy ke dada sangarta yarinyar nan”.
Karfe sha daya da rabi dai-dai na safe suka kullo gidan. Landlord din ya karbi mukallansa da basu kudinsu da suka ragu a hannunsa, da yake na shekara biyu cif Daddyn ya biya, yau kuma shekara daya da watanni biyu kenan, amma Daddy ya ce ba zai karba ba ya bar masa.
Zuwa sha biyu da rabi suna kan layin screening. Karfe daya dai-dai jirgin ‘American-Airways’ ya soma tafiya a kan kwaltarshi. Yana wani irin kartar kasa. Rahane na share hawaye tana kallon dogayen gine-ginen kasar Singapore da suka soma kankancewa yanzun a idonta, a sabili da daidaito da jirgin ya soma a kan gajimare duk da bai keta hazo ba, tana fadi cikin ranta,
“Bye-bye Singapore...... Bye-bye Informatics!!!”.
Karfe biyu na cika suma su Daddy KLM ya lodosu zuwa Nigeria bayan yayi transit dasu a India.
*****