← Book details Rayuwar Rayhana Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 14

Sashe 10

Rayuwar Rayhana Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayhanah na durkushe tana regaining consciousness. Ta rasa a duniya take ko a lahira. Ibrahim ya kara da cewa,
“Idan don lasisin da na baki na soyayyata a gareki ne yasa za ki wulakanta min UWA, to kin yi kadan Rayhanah! Son ya ci uwatar! Soyayyar ta ci abu kazan.....ubanta. Ki gaida mutanen TAKAI”.
Ya raba ta gefenta ya wuce rungume da ‘yarsa, wadda har zuwa lokacin ba ta daina tsala ihu ba.
Wata Nurse ce dake bangaren Nursery, wai ita Regina ta karbi jaririyar daga hannunsa ta sanya mata kan feeding bottle a bakinta (nipple), sai ta yi shiru. Ta mika masa ita tana tambaya.
“Where is her Mum?”
Sai ya wuceta zuwa motarsa bai bata amsa ba.
Ya bude motar ya shiga ya zauna ya bude tawul din ya rufeta sosai ya kwantar da ita a kusurwar kujerar baya, ya dinga jan motar a hankali kamar mai tafiya akan kwai kada ya jijjigata.
In ka kalle su shi da jaririyar sai sunyi bala’in baka tausayi. Idanun shi sun kada sunyi jawur amma ba hawaye yake ba. Bakin ciki ne da fushi mai tsanani, yana mamakin halayen mata.
Kai ka so su, ka kaunace su da zuciyarka daya, ka so nasu har fiye da yadda kake son naka, amma ba za su saka maka da komai ba sai raini ga mahaifiyarka, wadda itace silar komai na zamowarka in existence har kayi girma da balagar da suka samu suka aura suke mora, ba don komai ba sai don saboda sun sameka a hannu.
To Allah wadaran soyayya! Shi ya sanya bai taba yiwa kansa sha’awar auren soyayya ba da farko saboda gudun irin wannan fiffikar.
Ga wadda yake murna da halayenta, dabi’unta da ginin da suka soma yiwa rayuwarsu, ta nuna masa itama bata da bambanci da sauran mata.
Har ya iso gida tunanin da yake ta yi kenan.

*****
[12/30/2019, 20:24] Takori: Sanda Rayhanah ta samu dawowa hayyacinta daga gigitattun marin Ibrahim sai ta mike tsaye hajijiya na dibarta. Dai-dai lokacin likitanta da Nurse suka shigo, cikin mamakin abinda ya kawo ta bakin kofa haka ko hutawa ba ta gama yi ba.
Haka suka sata gaba da lallami da ban baki har ta hakura ta koma gadonta ta kwanta. Suka ci gaba da abin da ya kawo su, suka bata magungunanta ta sha suka sanyata ruwan zafi suna ci gaba da kula da ita, kulawa ta musamman albarkacin Dr. Ibraheem.
Likitan ya tambayi babyn, tana kuka ta ce Babanta ya tafi da ita. Cikin mamaki suka ce
“Ina?”
Ta ce, “Ba ta sani ba”.
Sai kuka.
A take Dr. Aziz, Musulmin Lebanon ya kira wayar Dr. Ibraheem, magana suka yi mai kama da jayayya. A karshe ta tsinci maganar Dr. Aziz inda yake cewa.
“Wannan Issue dinku ne kai da iyalinka babu ruwan baiwar Allah, kada ka kwareta ka kawo ta uwarta ta shayar da ita ko in kai maganar kotu wallahi”.
A wajen Bature yaro ya fi komai muhimmanci, kuma gwamnati na da ikon raba Da da iyayensa idan irin haka ta faru, ko in an ga za su cutar da rayuwar yaron musamman kasar Amurka da Ingila.

Ba ta dai ji me Ibrahim din ya ce ba, Dr. Aziz ya ci gaba da bincikar lafiyarta. Ya yi rubuce-rubuce cikin file dinta, sannan ya iso gabanta a hankali ya ce,
“Ko mene ne ya hadaki da Dr. Ibrahim ki kwantar da kai ki amshi laifin, ki karbi jaririyarki ki shayar da ita kin ji? Babu abin da take bukata a halin yanzu sai ke da dumin jikinki, idan fa har kina son soyayyar uwa da Da ta kasance tsakaninku, kar ki bari a rabaku, kin ji?”
Tana share hawaye ta daga masa kai. Ya ce ta zo ya kaita gida in ji Ibraheem.
Ba ta da zabi in ba komawa gidan ba, jiki ba karfi babu passport ina za ta je? Sai dai ita ma ta yi fushi da Ibrahim a kan marin da ya yi mata, fushi irin wanda ba ta taba yinsa a kan kowa ba, including MAMI.
Shine ya danna bell a flat dinsu, Ibraheem ya bude daga shi sai farar singilet da wandon wanka gajere, ya bata hanya ta wuce inda ta jiyo babyn nata tsala kuka. Tsikar jikinta ta tashi gaba daya ta saurara don jin daga inda kukan ke fitowa, master bed room ne.
Ba ta bi ta kan wani Ibraheem ba ta je ta sunkuto ‘yarta ta fito. Dr. Aziz na nan falo tare da Ibraheem suna ta ragargazar Turanci kamar an bude CNN. Da alama mukabala suke yi, Dr. Aziz na tausarsa.
Ta zo za ta wuce dakinta ya ce,
“Come here Rayhanah”.
Tana matukar ganin kimarsa kasancewarsa consultant na gynecology din Illinois baki daya, kuma aboki ne na jiki ga Ibrahim, domin tare suka yi karatu duk da suna fanni daban-daban.
Ya mika hannu ya ce,
“Bani ita”.
Tana share hawaye ta mika masa, Ibrahim ya yi kicin-kicin ko kallon ta ya ki yi.
Dr. Aziz ya ce,
“Durkusa ki ba shi hakuri”.
Sai ba ta yi musu ba ta durkusa din.
“Ka yi hakuri Ya Himu, bai kamata ka yi hanzarin yanke hukunci a kaina ba, ba tare da ka tambayeni dalilina ba.
Na san abinda baka sani ba. Mami ba ta sona, shi yasa Daddy yake boye mata aurenmu.
To kuma ga zuri’a ta soma taruwa ina so Mami ta sani…. ina tsoron..,. ina tsoron… kada ta ce ba za ta amshe ta a matsayin jika ba…. tunda ba ta san da aurenmu ba”.

Cikin harshen Hausa take yin maganar cikin kuka da karkarwar murya, kada Dr. Aziz ya fahimta.

“Wannan statement da kika fada wai bata son ki, kamar ya ya ba ta son ki, ban gane mata ba? Wane irin so kike so ta yi miki bayan wanda ta yi miki tun kina Rahanen ki?
Da bakina mun yi fada da Mami a kanki, da na ce ban yarda da zamanku tare da su Abida ba. Cewa ta yi ita babu ruwanta, Da na kowa ne, za ta rike ki tsakaninta da Allah.
Sannan don yanzu na ce zan sawa ‘yata sunanta ki nemi wulakanta min ita Rayhanah? Sam, ba zan dauka ba wallahi. Ki yi mana duk zabin da kika gama dama, a shirye nake da karbar duk hukuncin da kika yanke. Sunan ‘yata Asma’u, Rayhanah ki yi duk abin da za ki yi….”
Ganin cewa ba ta da hujjar da za ta kare kanta a kan wannan bayani na Ibrahim a kan mahaifiyarsa, sai ta bi shawarar Dr. Aziz wanda ke ta daga mata kai da kada mata ido alamar ta dauki laifin, sai ta kama kafarsa….
“Na yi kuskure Ya Himu, don Allah ka yi hakuri….”
Ta ci gaba da rera masa kuka mai nuna MARAICIN ta.
“Ba ni da uwa, bani da uba, bani da komai sai kai da Baba Dacta, sai ‘yar da Allah ya bamu yau din nan. Idan ka rabani da ita ka ki ni saboda kuskurena ina za ni? Ibrahim ina zan sa kaina???”.
Ta kwantar da kai a kan gwiwoyinsa tana sauke ajiyar zuciya.

Ga mamakinta sai Ibrahim ya mika hannu ya dago habarta yana share mata hawayen da ‘yan yatsunsa zara-zara guda biyu. Sai Dr. Aziz ya yi gyaran murya don su san da zamansa a falon, domin ga dukkan alamu suna bukatar fiye da hakan wajen lallashin junansu.
Rayhanah ta mike ta zauna kusa da Ibrahim, ya mika hannu ya sarkafo kugunta. Dr. Aziz ya ce,
“Kin iya breast feeding?”
Ta girgiza kai cikin jin kunya wato “A’ah”.
Sai ya hau nuna mata,
“Haka za ki rike ta, ki dago ta haka…. Ki sanya nipple din a tsakanin yatsunki biyu, sai ki sa mata a baki. Amma ki dinga yi da lura kada ki toshe mata hanci.
Idan ta sha da yawa sai ki dagata ki dora a nan…. (ya nuna mata) har sai ta yi gyatsa”.
Rayhanah ta daga kai. To ungota yi in gani. Ta karbi ‘yar, amma don kunya sai ta yi dakinta, ba za ta iya wannan rashin kunyar ta likitoci ba.
Ba Dr. Aziz kadai ba, Ibrahim ma ya yi dariya. Ya raka Dr. Aziz har motarsa ya dawo ya rufe gidan bayan ya sallami Benjamin.
A yadda ya shigo ya same su, ta takarkare tana aikata yadda Dr. Aziz ya koya mata ne, har ‘yar ta kama hungrily tana ta tsotso. Sai suka ba shi sha’awa da tausayi, duk da har lokacin bai gama warewa sosai ba.
Itama din kuma a shake take, bata huce ba daga marin barin makauniyar da yayi mata. Kawa-zucin ‘yar dama shi ya fi damun ta, tunda ga abarta a hannu, to babu laifi ko Ibraheem ya ci gaba da dukanta.
Sai ga hawaye sur-sur! Suna tittidowa. Ibrahim ya zauna a kusa da ita a hankali, ya turmutsa yatsunsa cikin kwantacciyar sumar kanshi ya lumshe ido a hankali, sannan ya bude yana kallon yadda ‘yarshi ke zukar nonon uwarta, ya tabbatar ya dau alhaki, ya san Rayhanah kuka take, amma bai yi yunkurin komai a kai ba.
Wata irin soyayya ce mai yawa ta tsakanin uba da Da ke ratsa shi. A lokaci guda kuma tausayin Rayhanah, yana tuna kalaman da ta gaya mishi dazu.
Wannan shine a doke ka a hanaka kuka. Shi kansa ya san Abida ba ta son Rayhanah, amma bai san da Mami ba.
Haka nan ya yi mamakin dalilin da yasa Daddy ya hana shi gayawa Mami aurensa da Rayhanah, in haka ne akwai ayar tambaya a tsakanin mu’amalar Rayhanah da Mami. Ya tuna cikin kalamanta tace

“nasan abinda baka sani ba!”
Chapter 10 · 0% Book details