← Book details Masifaffen Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 91

Sashe 58

Masifaffen Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nazifi Suna wajen Reception ya Ciro Wayarsa yaTurama Sakina Sakon... *Alhamdulillah...An daura Aure..Yau na Tabbata Miji ga Hauwa"u...Fatan Allah ya bamu zaman lafiya.......*Ya Turamata da gayyah ya nuna mata ya zabi Jidda Fiye da ita aikuwa Tana gani Sakina ta Fara kuka Tana Fadin manganganu Tunda Ta Dawo Gida bata da kwanciyar Hankali ko wajen aikinta Bata koma ba Tun Tana Tunanin ganin Nazifi har ta Daina Ta Shiga Damuwa Sosai kullum sai kuka Bata taba Tunanin haka take son Mijinta ba sai wannan gabar Kawarta Rukky Ita Hajiya ta Kirata tazo Tana Bata baki Bayan ta karanta Sakon Nazifi Sakina na kuka Tana Zagin Nazifi da Abdullahin da Ita kanta Jiddan Rukky ta Bude Baki Tana Fadin"Wai ina ce ba wannan abokin nashi da kuke Mutumci da matarsa bane Nazifin ya auri kanwarsa..?

Sakina na kuka tace"Eh Shine...Hafsah ba.."Rukky tace"Kinji ko..? Wlh itama da Hadin Bakinta In banda Munafunci ai babu yarda za"ayi Ace Mijinki zai auri kanwar Mijinki bata sani ba in gaskiya ne ta Kiraki ta Fadamiki mana.."Cak kuka Sakina ya Dauke idanuwanta Jajir take kallon Rukky kafin kawai ta Zabura kan Dressing mirror ta lalubo wayarta Jikinta na Rawa ta lalubo Lambar Hafsah ta Kirata.

Hafsah na chan ana Hotuna da ita Taji wayarta Dake Cikin aljihun Rigar Shaddarta ta Dauki Ringing Dama Doguwar Riga Tayi mai aljihu saboda Cikinta Daya Fito,Sosai ya sakata kiba yanzu Duk yawancin kayanta sun mata kadan,Tana Daukowa ta Duba taga Sakinar Nazifi sai da Gabanta ya Fadi ammh kaucema Hayaniya sai tamatsa Gefe ta Daga Kiran,Abun ya bata mamaki Dataji Sakina na kuka tana mata mgana kan cewa Har da ita aka Taru akaci amanarta Wajen Tusama mijinta kanwar Mijinta Data rasa Mijin Aure,mganganu dai gasunan masu alama da Cin mutumci da Zagi Duk kawaicin Hafsah Sai da Ranta ya baci Jin Tana Neman Zagar mata miji sai kawai ta yanke Kiran Ta juyo ta Dawo sai ga Subai"atu Cikin mamakin gani  Chanjin Fuskar Hafsah take tambayanta Abunda ya Faru ita kuma ta gayamata wata uwar ashar Ta lailayo ta Lafta kafin Tace"Kata'i lalle nema Matarnan ta Cika yar iska yo ke kuma sai kika ce mata me..?
Hafsah tace"Me zan ce mata..?biye mata zanyi muyi ta Hayaniya..?kashe wayata nayi.."

Subai"atu ta Ciji yatsa kafin tace"Nayi Takaichin Lokacin Data Kira wayar bani na Daga ba wlh da sai ta Raina kanta..Dama tana son Mijin nata don Durun ubanta Take wulakantashi..? Ta kwantar da Hankalinta mun ma kanwarmu karatun komai Wlh sai ta Bata mamaki Shegiya kota ma Abujan ne ko Kadunan ita ta sani..."

Hafsah tace"Ohon mata..Ammah ai maganganunta ba ilimi sam..Ina ma ji Wata a kusa da ita na Tayata Allah kyauta asan Kishiya akwai zafi ammh sai ka samar ma kanka Natsuwa.."Subai"atu Tayi Tsaki Tana Fadin"Kar ma ta samar kanta...Ubanta zataji Wlh..Gata ga aikin Abuja nan Miye nata na Damuwa bashi ta Rike ba da Sai ya Rika bata Abunda Namijin Duniya Ke bama mace Shegiyar ashe Tasan Kan Abun Wlh naso kaduna Jidda zata Fara zama mije mu Baje Iskanci Da sai ta kusa Mutuwa saboda bakinciki.."Hafsah tace"Kai..Sai kuma ba chan bane..Kidai ki kama girmanki Yaya
kike ba kawar amarya ba.."

Subai tayi Shewa kafin Tace"Tudu Biyu nake Takawa gani Yar amarya kuma Wlh Ta wani Bangaran kawar Amarya ce.."Dariya Hafsah Tayi Tana Fadin"Shegiya..Allah ya Shiryaki."Ta wuce Subai tabi bayanta Tana Fadin"Ameen Harda mai Ciki ma.."Hafsah na Jinta tamata banza ganin haka yasa Ta Bita tana Tsokanarta Ga Hotunanta sunyi kyau ko ta Turama Yaya Abdullahi ne ko kallonta Hafsah batayi ba sanin Shakiyancin Subai yafi gaban haka.

Sai Wajen La"asar kana Abdullahi da Nazifi suka gama Sallaman mutanensu,Daganan Cikin garin Suka Dawo Suka Shiga Gidan Inna Abu,su ka gaishesu ,kannen Nazifi sai Tsiya sukaima nan ya tsaya sukayi Hotuna suna Fitowa suka Hadu da Auwal nan ya Dake sai sun Tsaya Sunyi Hoto Domin mai Hoto Guda ya Dauko nan ma Sun Bata Lokaci,Kana suka Shiga Gidan Mama suka kai gaisuwan iyaye,Duk da gidan yana Cike ne,Mama kuwa Sai Shiga take tana Fita Abdullahi yayi mata kala Hudu yace itama ta Shiga ta Fita Uwar amarya sai Nuna Nazifin ake,ana ga ango chan Mutane natama Abdullahi Allah sanya alheri,basu wani jima ba Saboda mata Sunyi yawa Suka Fito Daga Gidan,Daga nan Kofar gidan Baba Wada suka koma Inda Daga gefe suka saka Babbar Tabarma suna Zaune Shida Mijin Goggo Habiba nan suka zauna suka kara gaggaisawa Shi kuma Nazifi sai ya zame Jikinsa dashi da wani abokinsa suka Tafi Gidan da Jidda ke Zama,Suna zuwa sai ga Auwal ya Shiga Har Ciki ya Fito da Jidda ga mai Hoto ya Shiga Daukansu Da su Mariya da Sauran kawayen Amarya,sai Gabda mangariba suka baro Wajen suna zuwa sukayi alwala Suka Shiga sallah bayan sun Fito ne Suka Fara kokarin Daukan Amarya Tunda Tawagar Hajiya Sa"a sun iso tundazu Gidan Mama.

Zannira ce ta Kira Wayar yaya Abdullahi ya Dauka sukayi mgana akan Abasu Mota zasu kai Jidda chan wajen Hajiya sa"a ta mata Nasiha suyi sallama Tunda su nan kowa yayi nashi,Harta shi Abdullahin yayi mata nashi Nasihan sai yace su Dakata Sauran abokansu na Anguwa su iso da Motocin su gama dai Kimtsa ta da komai da sunzo aka Fito da ita zasu kaita gidan Inna Abu Wajen Baba wada in yagama Mata Nasihan sai su wuce Dukkansu Chan Shika garin in sun Dawo Daganan sai Dakin Auranta basai sun Daawo ba,Da haka suka Kashe wayar,Bayan sungama Mgana ne ya ja Nazifi Gefe suka Tattauna yace hakan Daya Tsara yayi,yanzu Duka Motocin zasu iso.

Yana Kokarin Maida wayarsa aljihu ne yaga Alamar Sakon akan wayarsa sai ya Dakata ya Bude kamar yadda ya Zata ne Itace Domin Tun Ranar daya Rage mata Hanya koda yaushe sai Turomasa Sakon MorningMassges,da kuma na Good nite,sai na Jummat"mubarak kuma kowani Lokaci Zata saka Sunanta a kasa,Yana ta mamakin ina ta samu Lambarsa Lokacin kansa yayi Zafi da wannan Sha"anin Shiyasa bai Taba bin takai ba yana ganin Sakom nata bai Taba dai maida mata Reply ba,yau kamar kullum ga Abunda Ta Rubuto.

_I wish you a Hearty Congratulation on This occasion...may Ur Life always  Shower you with such Happy and Succeessful Moment...Allah ya Sanya alheri...ya kuma Basu zaman lafiya Ameen....BARKAT SHEHU..._

Mirmishi yayi Yau dai na Farko ya Maida mata da Reply din Ameen Nagode Barkat.."Barkat bata Taba tsammanin Abdullahi zai maido mata amsa ba,sai kawai ta ga Sakonsa Tsalle ta Buga adaki Ta Fada kan Littafanta na makaranta Wanda ta Dauko Tana karatu Saboda sun Kusa Fara test ne a makaranta,Rungume wayarta tayi Tana jin wani Farinciki na Ratsata Bahiya ce ta Shigo Dakin Jiya Ta Dawo Weekend ganin Barkat Cikin wannan Halin yasa ta Rike baki Tana kallonta kafin tace"Anty Barkat lafiya kuwa..?Hajiya tace lafiyarki kike Ihu ke kadai..?

Sai Lokacin Ta Dawo Cikin Hayyacinta Ta Bude Lumsassun Idanuwanta akan Bahiya kafin ta yunkura Ta mike ko kallon Bahiya batayi ba ta Dauki Wayarta Ta Tura kofar Tailet ta Shiga ta Rufo Kofar Batare da tabama Bahiya amsa tambayanta ba ganin haka yasa ta Tabe baki ta Fice Sanin ko Zata Shekara Tsaye Barkat bazata bata amsan Tambayanta Datayi mata ba...Barkat kuwa Kofar Tailet ta Jingina Dashi Tana ta Murnanta Lokaci Daya tana Fadin"Alhamdulillah.."Dama Abakin Hajiya taji Zencen Auran kanwarsa Da Nazifin Lokacin da ya Salisu yazo da safe yana Fadamata Daurin Auran na 11 na safe ne,shiyasa ta Turamai sakon Allah sanya alheri.

Su Goggo Habiba da Umman Sadiq da Inna Talatu sai Ammi suka kai Jidda Nasiha wajen Baba wada,Yayi mata Nasiha Sosai Shida Mijin Goggo Habiba,Daganan gidan Mama suka maidata tayi mata Sallama suka Rumgume juna suna ta Kuka Dakyar aka Bambare Jidda tana kuka aka Fita da ita Lokacin Sauran abokan sun iso da Motocin,Abdullahi shi ya amshi key din Motar Nazifi yace zai Dauki Jidda da kansa ya kaita Dakin Auranta Saboda haka Motar aka Sakata Daga ita sai Ammi sai Umman Sadiq da Goggo Habiba Dangin Hajiya sa"a Dama da Motocinsu suka zo Sauran Motocin kuma Kawayen Amarya su Rumana su Mariya suka Shisshiga Subai"atu kuwa da Hafsah Motar wani Ishaq suka Shiga Dayake Duk yan anguwa ne Zannira kuma Wata mota ta samu ita Dasu Jamila,Motoci a kallah sun kai goma Dayake anyi Abun da Tsari ne,ba Tururuwa kowa ya samu Harda kannen Nazifi Sun samu Shiga.

Gidan Hajiya Sa"a suka Fara Zuwa Abdullahi kadai ya Shiga da Mota,sai Danginta da Shigo da Tasu,Ciki yau ne karo na Farko Daya Taba zuwa Gidan,yana Cikin mota yace Su Goggo Su Fita da ita Don Allah Minti goma su Fito Haka kuwa akayi Basu wani Jima ba yan Nasiha ne da Sallama Dama kuma ta mata,suka Fito da ita,Abdullahin ma Tana kiran Umman Sadiq ta waya yana cewa su Fito

Tafiya zuwa gidan Amarya Tawagar ta kara yawa Tunda Har dasu Lariya Suna Zuwa kofar gidan Jidda ana Kiran Sallar Isha"i,Abdullahi da kanshi ya Rike Hannun Jidda har kan gadon Auranta,ya zaunar da ita ya Dafa kanta yayi mata addu"an Zaman lafiya Daganan ya Fice Su Ammi kadai ya Jira su da ya Dauko ya maidasu da kanshi Chan yaga su Hafsah da Subai"atu sun Fito Daga Mota Abunda Ya bashi mamaki ganin Hafsah Da gyale Ransa ya Baci Kamar ya Fito ya mata mgana sai kuma ya faasa Domin Rabonsa da ganinta Tun Shekaranjiya Banda ta Rainasa ta san Bayason mayafi Shine ta saka ga Cikinta ya Fito,ko kafin ma ya Fito sun Shige Gidan kawai sai yayi kwafa yace Zasu gamu,Su Umman sadiq ganin Dakunan kawai sukayi suka saka albarka suka Fito Abdullahi ya maidasu Daganan Ammi ya Dauka ya maidata gida Anty Hadiza Tun dazu tatafi Saboda Su Abdulwaseen suna ta Rigima bai Shiga ba ya Juya Ammi nata mai godiya.
Chapter 58 · 0% Book details