← Book details Masifaffen Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 91

Sashe 11

Masifaffen Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abdullahi yace"Subhanallah Mari..? Gaskiya baka kyauta ba bai kamata ka Daga Hannu ka Mari matarka ba komai ta maka kuwa abokina.."Nazifi ya saki Tsaki kafin yace"Yo In ma Bugu ne ta kama Bani Bugunta..Yarinya ta maidani kamar wani yaron Gidansu Saboda mene..? Ita ke Aurena ko ni ke Auranta..?

Abdullahi yace"Duk wannan bai Taso ba...kowa ya sani kai ne Shugabanta,ammh bazan Fasa Fada maka baka kyauta ba Babu kyau kuma ba Mazantaka Bane,Namiji ya Daga Hannu ya mari  matarsa gaskiya ba Dacewa bane.."Nazifi yace"Wlh ni kuma In dai mace zata kawomin Rainin da Sakina ta kawomin yau sai na Bigeta bama Marinta ba.."Abdullahi yace"Koma dai menene Hakuri ake Mutumina Mata sai a Hankali kowa ka karkace su Domin su Gyara Kara Bankare suke Abun ne sai Hakuri kawai.."Yafada Batare Daya Damu ya Tambayi Nazifin meya faru ba.

Nazifi ya gyara zama yayi yana Fadin"Ina gayamaka Mutumina Shekaranjiya naje Abuja Tunda naga wajen Sati uku Rabonmu da Juna,Ita batazo ba Nima Fushi nayi naki zuwa,Daga baya kuma sai nahuce na Bita Chan Mun kwana lafiya lau sai Jiya da Safe kawai naga tana Shiri Dana Tambayeta sai take Fadamin wai Wata Seminar zata lagos Kuma zatayi wajen kwana Hudu,Abun Takaichin ma ba Neman izinina take ba gayamin take don na Tambaya karim ma Abun Haushin ma atafiyar ita kadai ce mace Duka Uku wasu  gardawan Maza ne wadanda ba Muharramanta ba,Don na mata Mgana Shine ta tasomin Daga karshe Ni kuma nace na Hana Tafiya,Shine fa ta Faramin Borinta Data saba na kuma ce Wlh bazata jeba,kasan Saboda Raini yarinyar sai kawai taci kwalata Tana Fadin na Bata makullin Gidan Dana Dauka na rufe Kofar Falon saboda karta Fita ina gayamaka Mutumina,Sakina Hardamin Gorin gida da Dukiya,Ni kuma Raina ya baci na Tsinketa da mari na Tureta Gefe na Fito na Barta aranar na kamo Hanyar zaria Bansa yadda ta kare ba.."

Abdullahi Da yayi Sagale yana kallon Nazifi ya saki Nunfashi yana Fadin"Tabdijam...Abu kam baiyi Dadi ba ammh agaskiya Abokina saken kane Tun Farko Sakina ta Rainaka Kana Bani wannan labarin acikin Raina ina Tunanin in nine Wlh mace taci kwalata ina Fada tana Fada yadda na Tsani Raini da sa"in sa Wlh sai na Barta kwance Duk ko  ina Daukan Namiji mai Dukan mace Sakarai.."Nazifi yace"Hmm Nima na yarda da Haka Shiyasa nake baka Shawaran kar kayi saken danayi abaya Nima Daga saken ne Komai ya kwacemin shiyasa nake gayama kowani Namiji ya zama Jajirtattace kuma Masifaffe agidansa Hakanne kadai zai sa ya samu lafiya ya kuma sa mace ta Dinga Shakarsa.."Abdullahi yace"Da wannan don wannan kuma ka Fadi gaskiya..Toh yanzu ina ita Sakinar..? Tatafi lagos din ne..?

Nazifi ya Tabe baki yana Fadin"Ohon mata..Tun jiya ina Hanyar Zaria naga Kiran Tsohonta naki Dagawa nasan ta Kirashi ta gayamai karya da gaskiya Shi kuma mai ya' ya ya kirani zai Rainamin wayau naki Daga Kiran,yau kuma Tun Safe Baba ya kirani yace nazo yana nemana Ina zuwa sai yake Min Fada wai Baban sakina ya Kirashi yana ta Fada yana ikirarin sai yamakani kotu na Dakarmai yarinyar har sai da ta Suma..."Abdullahi ya Zaro ido Lokaci Daya yana Fadin"Innalillahi kaji wani Sharri.."

Nazifi yace"Wlh..ai ya saba dama yarda da mganar ya"yansa...Ita zata kara  mganar shi kuma ya hau kai mana Nadai ma Baba Bayani Daga karshe yayi tamin Fada kadai san Halinsa.."Abdullahi yace"Kai Abu dai bai yi Dadi ba sam..Allah dai ya kyauta kai Mata Duk haka suke in kayi sake Shikenan Nima Tun Jiya ko mgana bana ma Hafsah saboda ta gama Batamin rai wlh.'"Nazifi yace"Ahaf..Ai na gayamaka Wlh in baka zama Masifan kanka da Gidanka ba Sai kafini zama Abun Tsausayi meya Faru ne Hala..? Abdullahi ya sauke Numfashi da kamar Bazai gayamai ba sai kuma ya fadamai Kadan Daga Cikin Abunda ya Faru Nazifi ya karkace kai kafin yace"Wlh kamin daidai...gwara ka mata haka ai da gangane tasan ai kace mata ta koma Gidan Mama akan Lokaci Salon Raini ne kawai sai an yi mgana su kwashe sukai Gida iyayensu su mara musu Baya Allah dama Gida ka aikata Kila achan tafi gane Kuranta.."Abdullahi yayi ma Nazifi wani kallo kafin yace"Kawai sai na aikata Gida saboda wannan karamin laifin..? Ina fa som matata bawai bana sonta bane kuma Itama tana sona tana kuma min biyayyah daidai gwargwado da kuma Gudun Bacin rai kawai na yarda Kuskure aka samu zan Hora ta kawai da irin Horona ammh ba mganar Turata Gida Mutumina Haba dai Iyayenta ba irin iyayen sakina bane suna da Dattako sosai ba zan iya wani Abun da zan Tozarta musu ya' ba gaskiya.."

Nazifi yace "Ai Shikenan Tunda kace Haka gani nayi Turasu gidan yafi Firgitasu da kuma su Dawo Cikin Hayyacinsu lokaci Daya.."Abdullahi yace'Naki din..? Kai Gida ka Tura sakina Duk da Irin Dibar albarkar Datake maka.? Nazifi yace"Ban taba Tura ta ba ammh zan Turata kwananan wlh.."Abdullahi ya saki Dariya kafin yace"Dan Rainin Hankali...Oh Shine ni kuma da matata bata taba Maidamin mgana sai na Turata gida ko..? Anki din toh.."Sai Nazifi ya maida mganar Dariya Sun Dade suna Hira kafin Nazifi yamai sallama ya tafi.

Da yammah da Abdullahi ya taso Daga wajen aiki Gidan Mama ya wuce yaci Tuwo Dawa miyar kubewa chan yayi sallar mangariba da  Isha'i,Har kuma Lokacin Jidda bata Dawo ba Ran Abdullahi ya baci ya Shiga Fada Sosai Mama tana Bashi Hakuri kafin tace"Wlh yayansu na Kira Hauwa"u da kaina Nace mata kace ta Dawo gida sai kanwar uwar ta karbi wayar ta Rokeni na Bari gobe da safe zata Turota yanzu Dare yayi ne kaji yadda mukayi da ita Na dauka Tun safe zata Turota ammh har yanzu Shuru bata Dawo ba.."

Auwal na Zaune yana cin Tuwo yace"Mama bafa zata dawo ba wlh..Dama Yarinyar nan batajin mgana ta samu sake chan bamai gwabamata Dama ai bazata Dawo ba Wawiyar yarinya kawai.."Mariya na zaune tace"Kai ya Auwal kai fa Dan Zugi ne.."Da maficin gabansa ya Jefeta yana Fadin"Kimin Shuru wlh ko nayi kasa Kasa Dake yanzu nan.."Baki ta Tura tana kunkuni Dakatawa Yayi da Cin Abincin yana Fadin''Ammh Mama kina kallonta ko..? Wlh in ta kuskura ta Zageni saina mata Dukan Tsiyan sai ta manta Sunanta karyan Iskanci take ai Duk sune su Jidda marasa kunya.."Mama tace"Kai kuma dan Zafin Rai ba..ke Mariya kar in kara jin Bakinki anan wajem.."Tashi tayi Fuu ta Shige Uwar Dakin Mama Tana Kunkuni Auwal ya Rakata da Harara Abdullahi na Zaune yana Laluban Lambar wayar Mariya wacce Jiddan ta ari wayar Tatafi da ita, Daga ganinsa Ransa a Bace yake ya Hade Girar sama Data kasa Fuskarnan ba Fara"a ko kadan ko Ta kansu Auwal bai bi ba.

Ana Cikin hakane sai ga sallaman Jidda Ta Shigo Dakin Mama da Ledan kaya Riki Riki,Tana sanye da Doguwar Rigar atamfa mai launin ja Harda mayafinta karami ta Sagaloshi ta Wuyanta ta Shigo da Fara"arta tana Fadin"Mama mama..Anty Mariya na Da..."Mganarta ta makalene ganin Abdullahi zaune kusa da Mama sun Hada Ido Hudu Dashi kawai sai Jikinta ya kama Rawa sanin Hali Kauda kanta tayi Gefe daya tana kallon Auwal dake auna mata Harara Mama ta Kalleta tana Fadin"Jidda sai yanzu..? Na dauka tun safe innar taki zata Turoki Ga yayanku nan Tun jiya yake Fada rashin Dawowarki Wlh.."

Jidda Ta Bude baki tana Fadin"Allah mama zan taho Anty Lariyace tace na Tsaya zan karbi sa..."!Ki koma Inda kika Fito sai su Rikeki achan.."Mganar Abdullahi ta katseta wanda ya Fada Cikim kaushi da Fushi Lokaci Daya yana mikewa.

Jin Haka yasa Jidda ta sadda kai kasa Tana Fadin"Don Allah ya Abdullahi kayi Hakuri bazan kara ba.."Wani tsawa ya Dakamata yana Fadin"Yimin Shuru..In kika kara mgana anan wajen sai nazo na Tattaki mara kunya..Tun jiya da kika Fita Daga Gidanan sai yanzu kike Dawowa kuma Saboda Rashin kunya da wani Ficicicin mayafin wanda Dashi da Babu Duk Daya Don kaniyarki Shi kika saba sakawa anan..? Nace shi kika saba sakawa anan gidan..?

Ya karishe Fada Cikin Tsawa Da Sauri Taja baya kafin tace"A"a yaya..Bazan kara ba..'Tafada kamar tayi kuka yatsa ya Nuna ta Dashi kafin yace"Wannan ne na karshe da zan kara zuwa Gidan ace min wai kin tafi wani yawon wofi mara amfani in ma Fitan ta kama Dole akirani awaya a sanar dani in na amince aje in ban amince ba kowacce ta zauna agida bana son Shashanci banza da Yawo mara amfani kinji ko baki ji ba..? Da kai ta amsa kafin tace"Naji yaya.."Bai tsaya wata mgana ba kawai ya Wuce ta gabanta taja baya da Sauri sai da ya saka Takalminsa kana yace"Mama na tafi sai Allah ya kaimu.."

Mama tace"Allah taahemu lafiya ka gaida Hafsah da Megidana.."Bai amsa ba ya Fice Daga Gidan Cikin Fushi Auwal Dake zaune ya Saki Dariyar da Dama yake Riketa Tun dazu Jidda da Hawaye suka kawomata ta kalleshi kafin ta kalli Mama tana Fadin"Mama kinganshi ko..? ta karishe fada kamar zatayi kuka Mama tace"ina Ruwanki kuma Dashi..Kyalesa Hauwa"u na yakinan manta da wannan Babban gwabon.."Tafada tana yafito da Hannu Auwal kuwa sai kara tsintsira Dariya yake mariya na Ciki tana jindu Taki Fitowa Gudun kada Ahada da ita acikin Ranta kuwa Fadi take Anty Hafsah na Hakuri Wlh.
Chapter 11 · 0% Book details