← Book details Masifaffen Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 91

Sashe 26

Masifaffen Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mariya ce tace"Haka ake ta Gulma a anguwa ana Fadin Auran kudi yayi Gashi kuma ya Auro ma kansa wacce tafi karfinsa kwanaki Mama naji suna mganar da Ya Abdullahi Da suka samu matsala ya Taba marinta ta koma Gida Babanta ya Kira Baba wada yace wlh sai yamaka ya Nazifi a kotu Baba wada yace Abun bai kai nan ba,Ya Kira ya Abdullahi yace maza ya Raka Shi Ya Nazifin suje suyi ban Hakuri wanda ya jawo Ruwa ya Dakesa Shi kadai da Mutumcinsa bazai bari Nazifi ya maidashi Mutumin banza ba.."

Salati Subai ta saka ta na mamaki kafin tayi mgana Hafsah tace"kwarai kuwa Kwanaki sunje kano..Shida Abban Amira ammh kusan Halin yayanku Wlh ko Tadin bai taba yi Dani ba.."Mariya tace"Tabdijam Wake jin Zence abakin Ya Abdullahi in banda Mama..? Ko nima Ranar bai san ina Ciki bane Ina ma Mama gyaran Daki Dana Fito muka Hada ido kinga Ruwan Harara..?Dariya suka sakamata Lokaci Daya Subai tace"Da farko Haushinsa nakeji ina mai Allah kara ammh yanzu ya koma Bani Tsausayi Wlh inda ina da Diya Budurwa sai na wanketa na bashu Naga yarda Shegiya zata kare sai taje ta Rungumi aikinta Ubanta kuma sai ya maye mata Gurbin Nazifin..'

Hafsah ta Rike baki Tana Fadin"Lalle lamarin Babba ne..Ai bata baci ba ga Muhsina sai ya Jirata in ta kara Girma muyi Tuwona maina.."Duka Subai ta Daka mata abaya Tana Dariya Mariya na Tayasu Jidda kuma daman bata Cika saka musu baki ba in suna mgana Inna Talatu kuma taji sanyin A.C mota Tuni Barci ya saceta,Mariya ce ke Tayasu Da Dariya Dayake ita akwai manyance,Bus stop suka ijiye Mariya ta Hau adaidaita ta koma Bayan sunyi Sallama nan suka Barta tana neman Abun hawa.

Suna Tafe suna Hira gwanin Sha"awa Suna gabda Shigowa Zaria Subai tace"Jidda wai yaushe ne,Bikin autar Goggo Habiba ne..? Jidda tace"Wlh na manta ammh fa an kusa kamar naji Mama suna mgana da ita datazo mata Barkan Anty Zannira Tace watan Gobe ne.."Hafsah tace"Kai Abun har yazo..kamar fa Shekara aka saka ko..?

Subai tace"Eh mana nima nayi mamaki..Komai aka sakama Lokaci sai yazo lalle kice Danja zatayi Diban baki.."Hafsah tace"Aifa..Allah dai ya kaimu.."Jiddaa tace"Kafin na Madina din wannan Asabar din Diyar mijinta na Aure fa Shiyasa ma Tace ma Mama bazata samu zuwa Kaduna ba Tadai Kira Anty Zanniran ta mata barka.."Hafsah tace"Allah sarki..yakamata kuma ama Goggo kara kowani Sha"ani Da ita da ya"yanta akeyi.."

Subai tace"Sai Ya Abdullahi ya wakilataki kije Qawata.."Hafsah tace"Wa..? Rufamin Asiri ina Lallaba yan kayana yanzu ma Baku san Abunda zan Tarar ba na Tsiya.."Ta fada tana Dariya Dayake ta basu labarin yadda ya Barta ta Taho Tunda Ranar da sukazo da Daddare Umman Sadiq ta Kirata tana Tambayanta ko ya Kirata yace tatafi sai tace gatama akaduna.

Basu iso Zaria ba sai Wajen Biyu na Rana Dayake basu yi Gudu ba Gidan Mama Tawagar Sunan ta yada Zango suka bama Mama sakonta ita kuma tayi ta Hamdalan Sun dawo lafiya daya suka baro masu wanka sukace Lafiyarsu kalau suna gaisheta Dama koda suka iso Mama tayi Danwakenta da yajinta da manja nan suka baje sukaci suka Koshi suka Dora da Ruwa kana aka Zauna zaman Hira Bayan sunyi Sallar azahar.

Cikin Hiran ne Subai ke Fadin"Mama Ashe haka Matar Ya Nazifin nan take mara Mutumci..?Mama tace"Ho ke Subai"atu ina kika ganta kuma..? Nan mariya ke gayama Mama Yadda akayi Mama tayi Dariya Tana Fadin"Hoho..Subai kina nan da Halinki..Ina Ruwanki da Rashin Kirkinta Tunda Mijinta yaji kuma yagani.."Subai tace"Mama bawan Allah ya koma Abun Tsausayi.."Hafsah tace"Don Allah mu ki kyalemu da wannan mganar in baza ki iya gani ki kyale ba ki barshi.."Hararanta Subai tayi Daganan bata kara Mgana ba ammh haka Kurum take jin Haushin Sakina acikin Ranta.

Sai Da sukayi La"asar kana Kowa tayi Shirin komawa Gida kafin su Tafi sai Da Mama ta saka Suka Shiga Gidan Inna Abu ita da Subai suka kaimata Sakon Naman Sunanta da Turmin zanin Sakon Zannira ta karba tana ta Godiya ta sakamusu albarka suna gidan ma sai ga Baba ya Shigo nan Inna Abu ke gwadamai  Shima yayi ta Godiya yana saka musu albarka kana suka musu Sallama suka Fito Direban Mijin Subai Shi ya Fara kai Hafsah Gida kana ya wuce da ita Dama ta karbi key hannun Mama Tunda nan Abdullahi ke Barin key din Guda Daya Dayan kuma Dama yana Hannunshi ne.

Tana Komawa Gida ta Zage ta Fara Gyaran Gidan ganin Duk yayi Kura ta Share Tsakar Gida da Kitchen ta Share ganin yadda Abdullahi ya Birkita mata shi kawai Wajen Dafa Ruwan lipton,Ruwan zafi ma cikin Kittle yake sakawa,Dakin barcinsu kuwa Taga Abu kaya duk ya watsar Sai da ta gyara haka Tailet Ya watsar da Soso nan Sabulu chan komai dai ya Batashi Bayan ta Share ko"ina ta gyara sai ta koma Zaman gyara kayan Abdullahi na Cikin Wardrope wadanda kila wajen Daukan kayan da zai sakane Duk ya Birkita goggun Ciki ga kuma Kayanta da nashi wanda aka Dawo Dasu Daga wanki da Guga nan ya Turasu waje Daya Tana Gyarawa Tana mita acikin Ranta sai Gabda da mangariba ta gama gyaran kayan kana ta Fito Zuwa Kitchen ta Duba Fridge dinta taga Tana da Sauran Nama da Nikakken kayan Miya kawai sai ta Dora Musu Jallop din Shinkafa,Acikin ranta kuma tana Addu'an Allah yasa wannan karon Abdullahi ya siya mata gas Tuni Take nacin ya siya mata yaki wai saboda yara bata da Hankali wata Rana Sanda zasu je kusa ma bata sani ba Tunda Taji haka ta Hakura damai magiya.

Ta idar da Sallar mangariba kenan ta Kira Ammi ta Shaidamata Ta dawo Ammi tace"An dawo lafiya..Su Amira dai Kila sai Friday zasu dawo..Taji Dadin kiwon Tsohon Mijina ta nace taki Tafiya.."Hafsah na Dariya tace"Kai Ammi kodai ke kikaga Sabon Miji kika makalemai kina ma Daddy jan Aji Shi kuma ya kama Sabuwar amaryansa..?

Ammi tace"Wa..? Wannan ai ba megida bane Tunda baya Cefene.."Hafsah ta saka Dariya Ammi na Tayata tana jin Hayaniyarsu Amira Hafsah tace"Ammi kina ganin ba Matsala..? Kada fa Hayaniyarsu Amira ta Saka jinin Daddy ya kara Hawa..?Ammi tace"Ko daya karki damu ai shi Hayaniyar yaran yake so Tunda yanzu duk baku kusa dashi..Baki ga yadda yake sakewa dasu ba suma Sunfi son zama Dakinsa indai yana Gidan.."Hafsah tace"Shikenan Ammi..Ki gaida Daddyn zan kirasa.."Ammi tace"Shikenan.."Daga haka suka yanke Kiran Juna Hafsah na Mirmishi Sanin Diramar Ammi da Daddy kan Son Yaran da suka Haifa ita da Anty Hadiza,Koda Ammi tace sai Ranar Friday su Amira zasu dawo bata damu ba sanin Direba ke kaisu makaranta kuma Suna da kayansu chan Gidan Ammi kamar yadda suke dashi Agidan Mama Tunda suna yawan zuwa wasu kayan adawo dasu wasu kuma abarsu chan.

Koda Abdullahi ya Dawo ya Iske Hafsah ta gama Komai Har wanka Tayi ta Saka kaya Cikin Wasu Ubansu Riga da wando yan kanti wadanda suka kamata Sosai suka Fitar mata da Surar Jiki gefe daya kuma Tama kanta Barin Turare Duk inda ta gifta sai Tashin kamshi kawai take,kanta kuma wani Karamin Vail din gyale ta Daura,koda ya Shigo Gidan yaga Hafsah ta Dawo bai yi Mamaki ba Tunda ya Biya Gidan Mama ya ga Sakon Zanniran kuma Maman ta gayamai Sun Dawo Tun dazu Subain ma da Hafsah tare suka Fita.

Koda ya Shigo Hafsah Tana Sallar Isha"i Saboda haka kawai sai ya wuce Cikin Bedroom Karamar Jakarsa ya ijiye da key din Mashin Dinsa,kana ya Shiga Toilet ya iske ta sakamai Ruwan zafi a kittlle kawai sai ya juye yayi wanka Dashi ya Fito Kenan Daga wanka yana Sanye da Bakin Wando sai karamin Towel yana Goge Jikinsa Dashi sai ga Hafsah ta Shigo kallo Daya yayi mata ya kauda kansa kawai ya karisa gaban madubi ya Dauki mai ya Fara Shafawa.

Da kallo Hafsah ta Bisa sanin Hali yasa kawai ta karisa garesa ta Rumgumesa ta Baya Lokaci Daya ta Zuro Hannuwanta saman Cikinsa wanda Dukkansu sai da Jikinsu ya amsa Cikin kissa ta kwantar da kanta saman Bayansa Sanin tayi Laifi sai ta ke kokarin amfani da Hanyar da tasan Zata sauko da Fushinsa Da wuri.

Yana Jinta ya mata Banza sai ma Kokarin Rabata da Jikinsa yake yi Jin Haka yasa ta kara makaleshi Lokaci Daya ta Shagwabe Murya tana Fadin"Abdullahina Kana ganina na Dawo Shi ko mgana ko..? Tafada Lokaci Daya tana amfani da Hannunta Duka Biyu Tana Shafa kwantattacen gashin Daya kwanta saman Kirjinsa,Wanda sanadiyar haka Tsikar Jikan Abdullahi ta Fara tashi Ganin tana neman Birkitamai lissafi yasa yayi Sauri  Juyowa Lokaci Daya yana saka Hannu ya Raba Hafsah da Jikinsa Kallonsa take Cikin manyan Idanuwanta Shima sai ya sakarmata ido kawai yana kallonta ammh Fuskarsa ba Fara"a ko kadan

Ganin Haka yasa Jikin Hafsah sai yayi sanyi Duk Confident din Datazo dashi sai ta nemeshi ta Rasa,Sai kawai ta sadda kanta kasa tana wasa da Zoben Hannunta Cikin sanyin Murya tace"Sannu da zuwa ka Shigo ina Sallah.."

Yana kokarin Rabata ya wuce yake Fadin"Uhm...Na Shigo kina Sallah.."Daga haka bai kara komai ba ya Bude wardrope yana neman Jallabiyan da zai saka bata Dandara ba ta kara Binsa ta saka Hannun kenan zata Rikosa yayi saurin kaucewa yana kallonta Lokaci Daya yana Fadin.."Ina Kika ijiyemin Jallabiyoyina..? Yafada yana kallon Gefe Saboda Shigar datayi Domin wanke Laifinta ya kusa yin Tasiri a tare da shi.

Batare Da tayi mgana ba ta matsa gefensa ganin haka yasa Shima ya matsa hade da Juyamata Baya,Mamaki ya kara kama Hafsah aranta tace Abun Babba ne,Jallabiyansa ta Daukomai mai Ruwan toka tana Fadin"Gata ko na chanzo maka wata ne..?

Bai mata mgana ba illah ido Daya Zubamata lokaci Daya yana mika mata Hannunsa tagane Abunda yake Nufi ta mikamai Jallabiyan ta koma gefe tana kallonsa Bai sakata ba ya maidata ya Dauko Baka ganin haka yasa ta Girgiza kai ta Fice kawai Zuwa Kitchen ta Hado ma Abdullahi Dinner dinsa Zuwa Tsakiyar Cafet din Dake Cikin Falon.
Chapter 26 · 0% Book details