← Book details Masifaffen Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 91

Sashe 12

Masifaffen Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Assalamu Alaikaum my Follow pipu's Hop kuna Lafiya..? Ya kokari kuma..? Allah ya taimake mu Ameen Ina son Don Allah nayi muku wani karin Bayanine kan Wannan Littafin Dana ke kam Rubuta muku mai Suna Masifaffan Namiji..! Ina so ku Sani Dan adam Tara yake bai Cika goma ba Duk zamowarka gwani akwai inda zaka kuskusre Allah ne kadai ke iya yin Dadai kuma yayi Abun ya zama Daidai akoda yaushe Shi kadai ne baya kuskure ammh mu mutane akoda yaushe Cikin kuskure muke,Toh irin wannan Kuskuran nayi Wajen Da zan Rubuta Shekarun Abdullahi maimakon na Saka 35 sai na saka 32 kumin afuwa Shekarun Abdullahi 35,yayi Aure yana da Shekara 28 ne,Hajara Amira kenan Tana da Shekara 6, ne Yayinda Amir Usman kenan yana da Shekara 3da wasu wattani kenan,a lissafi Suna da Shekara 7 da Aure kenan Tsakaninsa da Hafsah, sai kuskure na Biyu da muka samu Shine wajen da nace Mahaifin Abdullahi ya saki Hajara ta wayar hannu,Toh an samu akasi ne,lokacin wayar Hannu bata Fito ba Shekara Talatin da wani Abu baya Sai mu barshi a Ya Tura mata sakon Sakin ne ta Tarkada har garinsu gusau,Ina Fatan awannan Bayanin nawa kun Fahimce ni..? Ina godiya Sosai Gareku,na Tabbata ba kuna Karatun littafin Janafty da baki bane kawai kuna Hadawa da Duka Zuciyarku Shiyasa kuka gano wannan kuskuran da aka samu,kuma Hakan ya Faru ne saboda karancin Lokacin da nake Dashi,in nayi Typing bana samun Lokaci da zan zauna na Maimaita har nayi Editing dinsa Ballatana in naga kuskure na gyara ammh Insha Allahu zan yi Kokarin na Dinga Bin baya ina Dubawa...Ina Matukar godiya gareku Allah ya bar zumunci Masoyan kwarai..Allah ka barmu da Masoyanmu Duniya da Lahira...Ameen ya Allah...*🙏

*Janafty..*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*

*Wattpad:JamilaUmar351*

*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..!*

*007*

  "Yadda ya Fita Daga Gidan Mama ransa bace haka yaje ma Hafsah Cikin wannan Fushin da Bacin Ran,Koda yashigo Tana Zaune afalo Su Amira suna Homewark dinsu yau batayi Girki Da Daddare ba Sauran Abincin Rana ne ya Ragu basu Cinye ba sai Sauran kazan Jiya Wanda Tunda taga megidan bai kula ba tasan bazai kula ba,Kuma koda ma Tayi abincin baya ci ballatana ma yabi ta kanta.

Kansa Tsaye ya Shigo Falon ko Takalmin kafarsa bai Cire ba,Sawun Cikinsa Dasu ya Shigo Har Tsakiyar Falon su Amira suka Tashi suka Rikesa suna masa Oyoyo,Kan Amira ya Dafa Shi kuma Amir ya Dagasa sama yana mai waasa,Hafsah Dake gefe ta mike tana Fadin"Sannu da zuwa.."Dama bata san ran zai amsa ba,kuma bai amsa ba Din yaja Ya"yansa Zuwa Ciki,Komawa tayi ta zauna kan Daya Daga Cikim Kujerun Falon Ta Zabga Tagumi kawai Domin Abun na Abdullahi ya Fara isarta.

  Chan sai gasu sun Fito da Robobin Ice cream a Hannunsu Kowa Dai dai,Dama taga ya Shiga da wata Bakar Leda,Suka zo suna  Nuna mata tace tagani susha abunsu sun zauna suna Cikin Sha sai Fada ya kaure Tsakanin Amir da Amira ta Tabamai Ice Cream dinshi Shi kuma ya Cika Fitina ya Fara Dukanta Hafsah na zaune ta Dakamai Tsawa yaki Sauraranta kawai sai tace"Amira in ya kara Dukanki ki Mareshi Tunda Bayajin mgana.."

Ita kuma Amira yana kara Dukanta ta saka Hannu ta makeshi ya kara Sakin kuka Ashe Duk Abdullahi na Ciki yana Jinsu Bai Fito ba sai da yaji Amiran ta Daki Amir din kana ya Fito da Sauri Cikin Bacin rai Har ya Sauya kaya ya saka Dogon wando baki da kuma Wata karamar Riga Fara,Kirere ya tsaya gaban Hafsah yana Fadin"Waya Dake shi..?

Hafsah ta Dago ta kalleshi kafin tace"Dukan Amira yake yi na Hanashi yakiji ni kuma nace in ya kara Tabata ta Dakeshi.."Tsayawa kawai yayi yana mata wani Irin kallo wanda sai da Hafsah ta sadda kanta kasa Tana wasa da Zoben Hannunta,Bai mata mgana ba illah Amir Daya Dauka yana Lallashinsa kafin ya kalli Amira yana Fadin"Mamana karki kara Dukansa kinji ko..?.

Kai ta Gyadamai Cikin Taushin Murya yace"Komai zai miki kar ki yarda wani ya kara cewa ki Dakesa ki Dakesa Kinji ko..? Kaninki ne kece Babba Watarana sai Labari.."yafada yana Hararan Hafsah wacce Tasan da ita yake Bata tankamai ba yaja hannun Amira Zuwa Ciki suka Barta nan da kallo ta Bisu tana Sauke ajiyar Zuciya.

Ranar dai su Amira wajen Abdullahi suka kwana ita kadai ta kwana Cikin Daki Abun yana Damunta ammh bata da yadda zatayi Tunda Ko zatayi mganan Duniyan nan Abdullahi baya Tankamata gashi ita kuma Bata da Dabi"ar Gayama wani Sirrin Mijinta balle ta gayama wani ko Zai bata Shawara,Subai'a ma ta Kirata tana Tambayanta Komai Lafiya ita da Abdullahi sai kawai tace mata komai ya wuce saboda bata Cika son Fadin wani Abu Daya Dangancin Auranta ba.

*****

Cikin wannan zaman Doya da Manjan Tsakanin Abdullahi da Hafsah wanda tayi iya yinta Domin Taga komai ya Daidaita ammh Abu ya gagara,sai kawai ta Zubama Sarautar Allah ido ta barma Allah komai.

Yau Takama Jumma"a ce,Bayan su Amira sun Dawo makaranta Mai mashin dinsu ya sake kwasansu zuwa Gidan Mama tare da kayansu da kuma Uniform din Haddarsu ta asabar da Lahadi Tunda chan Abdullahi ya sakasu Ranar jumma"a suke Tafiya chan Gidan Mama sai Lahadi kuma da Daddare Abdullahi ke zuwa ya Dawo Dasu.

Tun Bayan Tafiyarsu Gidan yayi ma Hafsah Shuru sai kawai ta Tsiri wankin kayan yaran da kuma nata,Sai Gabda mangariba ta gama tana gamawa ta Fada wanka Jikinta yayi mata wani Nauyi,bayan ta gama wanka sai ta Dauro alwala ta Fito ta Shafa mai ta saka Riga da Sikat na wani Boyel wanda Abdullahi ya Dinkamatashi Lokacin da zasu kaduna Zanniratu ta Haihu,Akamata Dinkin Buba,kayan sun mata kyau alokacin Haka Abdullahi ya Dinga yaba kyan Datayi Shiyasa ta sakasu yau zata jawo Ra"ayinsa Batayi kwalliya ba ta bari sai ta Idar da sallah Tukunnah.

Ta Shinfida Sallayar ta Tada sallar Raka"ar Farko Taji wayarta Dake Falo ta Dauki Ringing,Tana sallah Tana ji ana ta Kiran Wayar nata Haka Kurum taji gabanta ya Fadi Dakyar ta salallame sallar ta Fito Falo da Sauri Saman Daya Daga Cikin kujerun Falon ta ijiye wayar Dazu da sukayi mgana da Umman Sadiq Daga gusau,Da sauri ta Dauka Ganin Ammi ce ta Kirata Har sau Biyar yasa Jikinta Haka Kurum ya Fara rawa Ballatana ma Tun Dazu take Kiran layin Daddy bata Shiga Daga Baya kuma sai Taji wayar tana kashe Ta kuma Kira Ammi Har sau Hudu bata Dauka ba Tun Lokacin Jikinta ya bata ba lafiya.

Kiran tabi baya sai da wayar ta kusa katse kanta kana Ammi ta Daga Kiran Cikin Sanyin Murya tace"Autana ina kika Shiga kika bar wayarki ina ta Kiranki Shuru..? Yadda Hafsah taji Muryan Ammi yasa Kafarta ta Fara rawa Da sauri ta nemi gefen Kujera ta zauna Tana Fadin"Ammi kin kirani ina sallah ne..? Lafiya naji muryanki wani iri..? Ina Daddy nayi ta Kiran wayarsa Tana kashe kema na Kiraki baki Daga ba? Wani Abu ya Faru ne..?

Ammi tace"Auta irin wannan Jerin Tambayoyi wanne kike so na Fara amsa miki..? Hafsah tace"Duka Ammi..."Da Sauri kamar ta kagara taji ko lafiya ajiyar Rai Ammi ta Sauke kafin tace"Dama ba wani abu ne,Daddynku ne ba lafiya Tun Jiya Da Daddare Hawan Jininsa ya Tashi Haka muka kwana da Safe muka tafi asibiti a almadina muka Wuni yau sai yanzu muka Dawo Gida.."Da sauri Hafsah ta mike tana Fadin"Innalillahi Ammi Shine baki kirani kin gayamin ba.."Tafada Cikin matsanancin Damuwa.

Ammi tace"Shi ya Hana yace kar na Kiraku keda Hadiza Yasan ku da Rudewa yanzu hankalinku zai Tashi,Jikin da Sauki Gashi har mun Daawo Gida,lokacin muna asibitin ne ban Daga Kiranki ba Bayan mun Dawo ne na kiraki baki Daga ba sai na Kira Mijinki yanzu muka gama mgana Dashi ma.."Hafsah tace"Wayyo Daddy..Ammina ya Jikinsa..? Yaji Ssuki..? Yana iya cin Abinci..?ko barci yake ji..?

Ammi Tayi Dariya kafin tace"Kai Autana Irin wadanan Tambayoyin fa..? Ki bari in kikazo kya gani Abdullahi yacemin yana Hanyar zuwa Gida zai Daukoki ku Taho tare.."Hafsah tace"Ammi ki gaida Daddy sai munzo..Don Allah ki bashi abinci ya koshi.."Ammi tace"Ohoni Da ke da Hadiza bansan wanne yafi wani Son Daddyn nan ba itama dana Kirata Fadi take Ammi yaci abinci..? Yayi barci..? Ya jikinsa..? Ki bashi abinci karki barshi da yunwa hala kunfi son Mijina ne da kuma yadda zan kula Dashi.."?Ammi ta karishe Fada Cikin Zolaya tana Dariya ganin yadda Mahaifinsu Hafsah ke ta Dariya Shida kaninsa Alhaji Mustapha..."

Tura Baki Hafsah tayi kafin tace"Mudai mun fi Son Daddynmu.."Ammi tace"Ehe lalle Bari kizo sai Daddyn naku ya zaba ko ni ko kuma ku.."Daga haka ta yanke Kiran tana Mita Ita kadai Alhaji Hamza Dake Zaune kan Gado acikin Dakinsa zama irin na marasa Lafiya Bayansa Kaninss Alhaji mustapha ya karamai Filo,Farin Dattijo ne mai kima da Dattako Dan Kimanin Shekaru 63 aduniya Fuskarsa tana Cike ne da yalwar Fara"a da Haiba.

Cikin Muryan Ciwo yace"Banda Abunki Zinariya wazai Hada mata da ya"ya..? Kowa matssyinshi Dabam ko Mustapha..? Alhaji Mustapha na Dariya yace"Haba ina ma za"a Hada ai sai ana son mata ake son ya"yanta.."Mirmishi tayi kafin tace"Allah Baban Abdul Iyayin yaran nashi ne ya Isheni kowacce ta Isheni da Ammi Don Allah ki ba Daddy abinci ya koshi.."Tafada Tana kwaikwayon Muryansu Dariya ta kama Alhaji Mustapha da Alhaji Hamza ganin yadda Ammin tayi.

Hafsah kuwa Bayan Ammi ta kashe wayarta sai ta Sulale kan Kujera ta zauna Tsausayin Daddynta ya Isheta sai ga Hawaye Sharr sun zubomata ta Tuna Shekaranjiya da Damuwa ta mata yawa  Shi ta Kira suka Sha Hira yana ta Zoyalarta Dayake sunan Marigayiya Ayya aka samata Mahaifiyarsa Shiyasa yafi sonta daji da ita komai ya samu Mamana Shiyasa Tun tana Gida akwai Shakuwa Sosai a tsakaninsu Wani Lokacin Ammi tayi ta Fadan Irin Koda yaushe yana Tare da ita tana fadin watarana Aure Hafsah zatayi ta barshi Tunda Dukansu mata ne sai yace ba komai mijinta zai Dinga kawota ina ganinta Domin zan gayamai matarsa Ba irin Sauran mata ne bane, Autan Hamza ne kuma Uwa take garesa,In ya Fadi haka Daga Ammin har Hafsah dariya sukemai aikuwa Lokacin da Hafsah ta kawo Abdullahi sai da Alhaji Hamza ya gayamai Ya kular mai da Mamansa da kuma Autansa Hafsatu.
Chapter 12 · 0% Book details