← Book details Mai Bada Magani Ko Yar Damfara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 10

Sashe 9

Mai Bada Magani Ko Yar Damfara Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Hmmmm T boy maza faɗamin ina jin ka idan baka da abin faɗa to wallahi ni zan yi tafiya ta aunty safiya bata san na fito ba ga dare yana yi..
T boy yace '' to dai a gurguje wannan sana'a ba wata bace illa mu saidawa mutum kaya amma fake bawai masu kyau ba daga sama sai mu saka masu kyau kina hurda da masu kuɗi zan iya hada miki game idan kika ci ribar taki ce..,
wani irin kallo ta dinga yi mai me cike da anya kuwa kana da hankali yana gamawa tace '' Allah ya tsari gatari da saran ciyawa ba dani ba gaɗa a lahira ko da wasa idan ta ɓaci ka nuna ka sanni sai naci abu takazar ubanka wallahi..,
dariya yayi yace '' matsoraciya wa yace miki ana shiga dawa dan karya..,
ubanka ne ta faɗa tana tashi daga gurin daukan guda ɗaya tayi tace '' na chanza wayata da man ta mutu..,
be hanata dauka ba yace '' duk randa na gama tara abin duniya sai na zo muyi aure..,
dariya tayi tace '' wa ni hhhh T boy la fara samin matsala a kwakwalwar ka...,

Copy is not allowed
Hakkina ne mallakina ne kubar min kayana ban yadda ayi amfani dashi ba ta ko wacce siga
https://youtu.be/qKsLgKJdsdA
If you know that you're not going to talk to me about my novel or something that concerns me, please don't talk to me at all. I don't like what you're doing
following me around persistently and talking to me about things that don't concern me.

Episode 6

Wallahi ki dena dariya kar abu ya tabbata kizo kina dana dani.
bata ko kalle sa ba ta fara tafiya cikin sauri tsoron ta ɗaya kar ta hadu da wani idon sanin ta shiga uku zargin mutane ya tabbata sosai take sauri gaban ta na faɗuwa har ta fita titi mai babur ta tsara ta kwatanta mai inda zai kai ta , sukai ciniki ta hau.
fara tafiya su kayi wayar ta tayi ringing ganin aunty ce me kiran ta ja ƙaramin tsaki tace '' sai kace wata yarinya duk inda za ka ana kafama maka sharaɗi to yasin na kusan fyace kowa ma huta haba wannan a bin da me yayi kama ƙin ɗagawa tayi ita kuma aunty bata dena kiran ta ba.
har suka isa gida tana kiran ta kuɗi ta zaro ta miƙa mai da sauri ya kalle ta yace '' nawa mukai dake zaki bani wannan kuɗin...,
wani kallo sénatrice tayi mai tace '' babu da ya'yanta zan baka ban da tsabar cuta kamar ban san garin nan ba kace min kaza , zan bayar na bayar gani jikar me kudi ko..? to wallahi nayi maka ma da mutunci idan ka raina bani ina da bukatar su..,
da sauri ya dauko zai sharara mata mari wani dan daba da yake zaune yake chakewa yace '' kana taɓa ta wallahi sai na murmurma maka wuƙa a ciki na sarkafo ya'yan hanjin ka..,
kaga barshi ya dake ni daga nan BJ CLUB ya dauko ni shine wai saboda gashi jikan dan fashi zan ba shi dubu biyu ni kuma wallahi bana son tsayuwa ta a gurin sai nace muje ba wai na amince ba, kasan tsayuwa a gurin nan ba dad'i wallahi..,
senatrice kyale sa so yake jikin sa yayi tsami
amsar kudin yayi yace '' wallahi dana san ke yar iska ce da ban dauki ki ba ...,
sannu dan guguwa.
dan daban nan yace '' kai dalla ware ko nai maka billan yarabawa..,
hawa mashin din'sa yayi ya burga yayi gaba yana mata Allah ya isa,
Hajiya senatrice ya zaki tafi baki bani na hawa gajimare ba..
dan daban nan ya faɗa yana kallon ta.
har zata shiga gidan su sai ta dakata ta juyo tace '' biyo ni ka kwata wato tsaya min da kayi kanka ka tsaya wa..,
komawa yayi ya zauna kwafa tayi ta shiga cikin gidan da sauri aunty ta tashi tace '' lubabatu ina kika je cikin daren nan lubabatu kiji tsoran Allah ki duba martabar gidan mu karki zubar mana da mutunci..,
senatrice mayafin ta ta cire ta kunshe kuɗin da ta karɓa tace
"Aunty safiya nifa ba abin da kike tunani bane kema ke kinsan da irin yawan nan nake kya ganin a haka dan haka duk me zargina shi da Allah wallahi..,
Jikin aunty safiya ne yayi sanyi ta bi lubabatu da kallo har ta shiga daki zama tayi tana sakin ajiyar zuciya me nauyi
Kenza da take zaune ta tashi ta shiga dakin su tun da aunty ta dawo ai shikkenan sa yi bacci da mun shari.
Wannan kenan

ZINDER
Chapter 9 · 0% Book details