Sashe 10
Mai Bada Magani Ko Yar Damfara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hayaniyar da ake yi ne ya janyo hankalin inna da sauri ta kalle salmanu tace '' Bashir kamar hayaniya ake yi a kofar gidan nan..,
Bashir da yake ƙwance yana fifita yace '' to iya ni ina naga kafar fita naga ko me ke faruwa ina Hadi yake ya fita yaje ya gani ko me ke faruwa..,
Inna tace '' Hadi yanzu yaushe zaka gansa yana can gurin kallon yan dambe ni tsoro nake wallahi kar wata ran a gwabje shi..,
da sauri Bishira ya tashi zaune yace '' kallon yan dambe lallai Allah ya fidda a'e daga rogo amma wallahi hmm Allah dai ya kyauta..,
Amin dai ƙoƙarin shigowa suka ga ana yi da sauri suka tashi ganin an ajiye musu hadi ya meƙe sambal salati inna ta saki tana kururuwa baba da yake bayi da sauri ya fito ganin abin da yake faruwa yace '' innna lillahi wainna ilaihir raji'un me yake faruwa a ina kuka dauko shi..,
Abokin sa ya share hawaye yace '' wallahi sai da na hana shi, shiga cikin yan dambe be ji ba ya shiga miliyan ɗaya aka saka ga duk wanda ya kada shago na laure shi ne yana shiga yayi mai duka ɗaya , ya zube ya dena numfashi...,
habawa bishira yana jin haka ya doka calle ya matsa baya yana zare idanuwa cikin subutar baki yace '' na shiga uku ni bishira me kyau ashe a gaban gawa nake nabi ina naniƙe mata salon ta cabke min ƙafafuwana na shiga uku..,
Da sauri kowa ya ɗago ya kalle sa murguɗa baki yayi yana fari yace '' to munafukai masu zuwa lahira da ƙoƙon dambu.,
ko wanne su sai ya saita kan'sa shiga da Hadi akai daki tun da bishira ya ga an shiga dashi cikin daki ya fita kofar gida unguwar tayi baki abin da ba wutar lantarki ta gumi ya zabga ya lula duniyar tunani anya kuwa ba wani abin ya aikata ba da wa'yannan masifun suke bin sa ɗazu mahaukaciya ta dake su yan zu kuma ga gawa an shiga da ita cikin dakin su hawaye ya matse da gyalen sa.
abin duniya duk ya ishe shi kamar ance ya ɗago sai ya hango wani mutumi da fararan kaya gaban sa ne ya yanke ya faɗi ya fara zare idanuwan'sa yana cikin wannan yanayi yaji an shafi ƙiyar sa ai besan lokacin da ya zub duma ihu ba.
abokin hadi yace '' bashir ni ne fa...,
da sauri ta juyo ya jike sharkar da gumi ga hawaye wani na bin wani a kuncin sa cikin faɗa yace '' Allah wa daran naka ya lalace wannan wacce irin bura uba ce ne Allah ya rufa asiri ma na nuna jarumta da karfin zuciya ban da haka da wani ne ai suma zai yi karka kuskura ka ƙara taɓani idan ba haka ba wallahi zanyi maganin ka...,
girgiza kai kawai abokin Hadi yayi yace '' bashir kenan wannan mutuwar da dan uwan mu hadi yayi ya kamata ace ta zamar mana darasi ka duba ka gani yau lafiya muka wuni kalli zuwa dare abin da Ubangiji yayi ita fa mutuwa wa'azi ce ga al'umma idan sun dauka ya zame musu jari ranar gobe kiyama ....,
Wani kallo yayi mai ya ɗauke kan'sa ganin kamar nasihar da yake mai ta fara shiga jikin sa ya ci gaba da cewa yanzu zan je na karbo lilƙafani sai kazo mu tafi tare da me awan gawa sannan ni dakai zamu kwana a cikin dakin tun da ba za'a barshi shi kaɗai ba
Kama haɓa bishira me kyau yayi yace '' kai dawa...? Uhmm ba dani ba gaɗa a lahira tun da ake mace mace a unguwar nan ka taɓa gani na a hanyar makabar ta..?,
to ai ba abin arziki ka yi ba ka dai zo muje ayi abin da ya dace mutsaya Kai da fata gurin kyautatuwar dan uwan ka ai mai sutura cikin mutunci.
Bishira cire mayafinsa yayi ya daure a kugusa yace '' amma wallahi sama'ila sai yau na fahimci ba kada hankali ina mace ina ni ina kwana da gawa bama ta mace ba ta namiji kuma dakai a daki ɗaya ko dan dazu ka taba ni ban wanka ka da mari ba shine yanzu kake kawo min maganar banza to ahir ɗin ka wallahi karka kuskura ka kara yi min irin wannan kalamin jeka ka nemo dan uwanka namiji ku kwana tare da shi wai baba ma amfanin me yake a cikin gidan nan ai shi ya kamata a ce ya kwanta da wannan gawar,
Sima da yake salllamowa yaji Bishira me kyau ya zagi yana wannan mayani sai ya shiga karkashin benchin dake jikin gidan su ya riko ƙafafuwan'su shi da Sama'ila ya maƙe murya yace '' yanzu kuna matsayin yan uwana amma kuke gudana to wallahi tare za mu tafi..,
gumi ne ya shiga yanko musu ta ko ina wannan shi ake kira da tashin hankali ba'a saka maka rana.
ganin sun kasa ko da motsi sai sima yace '' au ni zaku mayar mara aikin yi ko ina magana kun yi shiru ga shege yana magana.,
da sauri Bishira Yace '' dan girman Allah dan uwana kai min aikin gafara wallahi Allah baka girman ka nayi jira nake ka gama magana sai na baka amsa ko Sama'ila...?,
karya kake yau tafiya ni dakai ba fashi...
Innalillahi wainna ilaihir raji'un Allahumma sai yarasa me zai ce sai zare ido kawai yake ga yawun bakin sa da yayi kaurin ba shiru ya soma sakin futsari bakin sima ne ya subbuce yace '' kuttumar uban can kayyasa ni zaka sakar wa fitsari a hannu..?,
saboda da tsabar rudewa be gane muryar sima ba kuka ya saka Sama'ila yace '' wallahi Allah bani nayi futsari ba shi ne..,
nan suka fara gardama wannan yana wannan ne wannan ne dariya ce ta subbucewa sima da sauri suka kalli kasan benchi ai bishira me kyau be san lokacin da ya take hannun sima ba yace '' wallahi Allah ya isa ka tsakani na dakai shege dan iska..
dauke hannun sa yayi da sauri ya fito yana dariya yace '' ina kwance a gida nasha uban ribiti a gurin mahaukaciya naji ance Hadi ya mutu..,
wani kallon banza bishira yayi mai yace '' billahilazi sai na rama dani kake zance..,
kaga mai da wukar Allah ya baku hakuri sima ya faɗa yana yarfe hannu
Saboda takaici Sama'ila buge shi yayi ya fara tafiya da sauri sima yayi baya yace '' me kyau kaga ɗan hau yana neman ya taɓa min jiki na..,
Sima yanzu ba wanne a gaba na ba bansan ta ina zan fara ba gidan nan fa yana neman gagara ta shiga a cikin fa dakin mu aka ajiye gawar hadi kuma ake min wani makahon zance wai na kwana da gawa wannan ita ce kadai soyayyar da zan nuna mai
a'a wallahi karki soma tab wallahi akwai matsala.
Sima ya faɗa yana zama akan benchi..
Bishira Yace '' gane min hanya gane min hanya wallahi nima ko sama da ƙasa zata haɗe bazan shiga dakin nan ba balle aje ga kwana alfarma ɗaya zanyi gudun zagin Allahumma zan je kai gawa wannan ne kaɗai abin da zan iya yi..,
kaga tafiya ta zama guri ɗaya tsauysayi ya faɗi haka ganin Sama'ila da malam liman DA me auna gawa sun dawo hade da wani farin abu a hannun sa da alama lilƙafa ni ne...,
wani yawu me ƙauri bishira ya haɗiye yace tabbas akwai babbar matsala ga su can ina kayi yanzu..?,
a'a bishira karka soma bina wallahi inji ya biyo ka har gidan mu kasan fa gawa ita ke zama fatalwa zauna inda Allah ya ajiye ka nima yau dakin su rafi'a zan shiga tunda ai duk jinsin mu ɗaya bazan iya kwana ba a ɗakina..
cewar sima ya faɗa yana tattare zanin sa domin so yake ya fita a guje kar bishira ya biyo shi sarai yasan halin bishira badai naci ba yawa baƙin mayye..
ganin abin da sima ke ƙoƙarin yi carab Bishira ya riko zanin sa da sauri yace '' a'uzubillahi minar sheɗanir rajim tsirara zakai min kenan kana ganin maza suna ƙoƙarin doso mu wallahi tun kafin nayi maka ɓarin makauniya ka sake ni bana son ciki da hulakanci..,
wallahi ba inda zaka yau tare za mu kwana.
aikuwa zancu bura'uban ka billahilazi shemaka zanyi a nan gurin ga bakar cuta dan anyi mutuwa a gidan ku shine nima kake so na bishi wallahi ban gane da wa nake tare ba sai yanzu to ka ci Kani ko yanzu jikin ka yayi tsami..