← Book details Mai Bada Magani Ko Yar Damfara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 10

Sashe 8

Mai Bada Magani Ko Yar Damfara Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Copy is not allowed 🗣️

Hakkina ne mallakina ne kubar min kayana ban yadda ayi amfani dashi ba ta ko wacce siga.

https://youtu.be/WoCX8WbJOuU

If you know that you're not going to talk to me about my novel or something that concerns me, please don't talk to me at all. I don't like what you're doing
following me around persistently and talking to me about things that don't concern me.

Episode 5

Dayar sima ya iya tashi ya ja zanin sa kirji ya soke a hammata yace
''Dan ƙari maƙari baffa yanzu abin da ya same ni ne be dame ka ba kenan wallahi da ace wani yaji wannan maganar gwara ayi min duka da icce haba wannan wacce irin magana ce a tunani na kai ne mutum na farko da zaka fara shiga wani hali da idan aka ce bani da lafiya..,
zama baffa yayi yace '' saboda gaka kanin mahaifina ko yarinya yi tafiyar ki karki kara hurɗa da irin wa'yannan mutanen wallahi wata ran idan baki wasa ba hmmm kashe miki aure za suyi...,
Innalillahi wainna ilaihir raji'un iya kina ji ko sheɗanu muka zama kenan dan annabin Muhammad sallahu alaihi Wasallama ki saka baki iya.
To SAUDE tace tayi musu sallama iya tace '' gaskiya a bin da kake baya dacewa ai hannun ka baya rubewa ka yanke kayar..,
Tabawa sauna kuma ake kai hannu a yanke wannan dai yaron nabar miki shi halak malak..
ya faɗa yana tashi daga zaman da yayi zama tabawa tayi tace '' kaga ko salmanu ka nutsu ka dinga bin duniya a sannu..,
to iya zan dinga tafiyar sanɗa shikkenan magana ai ta kare nabi maganar ki..
takaici ne ya hata magana

Wannan kenan

Bayan fitar SAUDE gidan su bishira ta shiga sallama tayi mahaifinsa da yake zaune yana mai fifita yace '' a'a sannu da zuwa ashe haka abu ya faru..?,
zama tayi tace '' baba ina wuni..,
lafiya qalau alhamdulilah ya kuma tsauysayi.
hmmm baba alhamdulilah mun tsallake Rijiya da baya.
Cewar SAUDE.
tashi baba yayi yace '' ɗazu na gama yi mai faɗa ya za'a yi kaga mutane rike da mahaukaciya kace ka san guri ai ba zaka ce ka sani ba.
SAUDE tace '' baba wallahi duk su suka ja min wannan fitinar Allah ya rufa asiri yana nan a dakin da nake akwai waya na buga mai yazo ya tafi da ita da wallahi yanzu wani zancen ake yi ba wannan ba tsaf matar nan zata ci uban mu kana ji fa har cin mutum take..,
Baba yace '' innalillahi wainna ilaihir raji'un mayya dai suka kawo miki..,
Hmmm wallahi kuwa mayya kai dai Allah ya saka mu dace
Amin ya Allah yace tashi tayi tace '' baba bata nan ne..?,
Bishira yace '' ta tafi unguwa.,
cikin jimama tace '' sai ta dawo ta tarar da tashin hankali..,
Wallahi kuwa ya faɗa yana cije lips din sa domin sauran kaɗan ya zunduma ihu bayan sa wani irin ciwo yake mai.
Hadi ne ya shigo yace '' Allah ya saka wannan ce sanadiyar shiriyar ka...,
na shiga uku daman ba a shirye nake ba SAUDE a yaya kike gani na dan Allah karki boye min..
Bishira me kyau ya faɗa yana yarfe hannuwansa tare da lankwasa murya kai kace mace ce tayi maganar nan
Hadi yace '' dan Allah karki boye mai ki faɗa mai gaskiya abin da yake aikatawa haramun ne ko ba haramun bane..?,
Kaga Hadi bana son neman fitina zo ka bar gurin nan tun Kafin ranka ya ɓaci duk wani abu kai kake fara assasashi..,
baba ya faɗa yana nuna mai hanya ita dai SAUDE sallama tayi musu ta , tawo gida tana zuwa kofar gida wani kallo MUDAN yayi mata da ya saka hantar cikin ta kaɗawa dauke kai tayi ransa a ɓace yace '' karki sake ki shiga cikin gidan nan..,
daidai lokacin usman ya fara kuka jijjigashi ta fara yi rintsai idanuwan'sa yayi da suka kaɗa sukai ja baya so tun yanzu su gadarwa da dan'su matsala baya so ace koya ya fara fuskantar wane hali suke ciki da SAUDE bayan mahaifiyar da ta sani amma da tuni ya dade da sawwake mata Allah ya sani ya gaji da halin ta , tashi yayi ya rufo shagon sa ya shiga cikin gidan bin bayan sa tayi zuciyar ta na lugu dan uku uku yanzu yace ta tafi gidan su ya za tayi tafa shiga uku ke nan da wanne ido zata kalli mahaifan ta kullum nasihar su a gare ta tabi mijinta sauda kafa.
tsayuwa tayi tana fiƙi fiki da ido yawa an jiƙa ɓera a cikin ruwa zama yayi akan kujerar da dazu ya tashi yace '' wallahi kina gab da kaini bango ke ko tausayin yaron nan bakya ji kuma duk ranar dana sallame ki wallahi sai kin dire min ɗana..,
da sauri ta ɗago shima kallon ta yake yi yaci gaba da cewa eh abin da kunnuwanki suka jiye miki shi na fada ki ci gaba da kaini bango har muje batakin ƙarshe sannan yanzun nan abeeda zata zo ki tsaya tayi miki kitso..,
zama tayi bata ce komai ba , ta kunto usman da yake ta kuka zip din rigar'ta ta zuge ta fara bashi mama yana sha shiru yayi yana yan wasannin ta duk maganar da MUDAN yake yi ko tari ta kasa yi tsoron ta ɗaya tayi magana yace ta tafi gidan su wallahi ba inda za ta ai danta namiji ne dan haka zaman dan'ta za tayi ba inda za ta tana wannan tunanin ne ta ɗago suka haɗa ido gaban tane ya fadi domin ko kallon ta MUDAN yayi tana iya karantar yanayin da yake ciki jan hijabinta tayi ta rufe kirjinta ta maida kan'ta ƙasa sallamar abeeda taji da sauri ta dago tana amsawa gaishe da su tayi SAUDE ta amsa tana kau da kan'ta daga kallon MUDAN.
zame dankwalinta tayi tace '' kafin ya farka zo ki fara yi min..,
Abeeda ta leƙa usman da ya fara bacci sakin maman ta yayi ya ɗago tare da yin dariya dariya abeeda tayi tace '' kinga ashe ba bacci zai yi ba...,
SAUDE tace '' aikuwa dakyar ya barmu ayi min kitson nan..,
to sai na goya shi, daukan sa tayi ta goya shi sannan ta fara taje danƙararran gashin SAUDE duk uwar ta zar da ake mai tsilin gashi ki ɗaya be zuba ba saboda tauri da rashin gyara.
tashi yayi ya fita abeeda zama tayi ta yarfa mata kitso me kyau bayan ta gama tayi mata godiya ta tafi da usman gyara gidan ta fara yi sannan ta ɗora girki zama tayi tana lissafin kudin da zata turawa sénatrice ta my nita bayan ta gama ta saka hijabinta ta fito yana zaune shi kadai a kofar shagon sa yana karatun Alkur'ani ta dade a tsaye akansa sannan tace '' zan tafi can shagon ne zan turawa sénatrice kuɗi bata da lokacin da zata zo ta karɓa kuma bukatar su take..,
be kalle ta ba yace '' ɗazu ni kika tambaya kika fita...?, kuma me nace miki ba ce miki nayi na karki shiga cikin gidan nan shi ne kika shiga..,
hijabinta ta saka tana goge idanuwan'ta cikin muryar kuka tace '' wallahi ba inda zani ni dakai mutu karaba me kake nufi dani ne da kace karna shiga cikin gidan ka na tafi namu gidan ko me..?,
ganin hankalin mutane zai fara yowa kansu ya ƙara rufe shagon sa ya shiga cikin gidan bin sa tayi tana cewa to wallahi ko ka sake ni ba inda zani zaman ɗana zanyi kuma naga shegiyar da ka auro ka kawo ta cikin gidan nan wallahi Allah sai na yanka ta sai da ka gama dani ka mai dank bazzawara kace min ga zance ga magana komai duk yabi ya saki..,
Dariya ce ta kusan subbuce mai amma sai ya danne yace '' oh Allah ba kina haɗa mai da tsohuwa yarinya ba wel come back virginal to sai ki haɗawa kanki hakkina nawa kike tauyewa a cikin gidan nan , wallahi nagaji maganar sai da maganin nan na hanaki ƙin ƙi hanuwa bansan ya zanyi da ke ba wallahi idan ba mu rabu ba to zan kara aure gudun saɓawa mahaliccina..,
da sauri ta cire hijabin ta tace '' anzo gurin daman tun jiya abin da kake nama kenan daman duk wani take taken ka kallon ka kawai nake yi yasin ba zaka sani a cikin tashin hankali ba , naje na ƙara yin wani cikin na shiga uku dan dai ba a jikin ka yake ba shi ya saka kake faɗar haka..,
tsura mata ido yayi ashe duk guje gujen da take yi saboda karta ƙara daukan ciki ne tab lallai tana da aiki yace '' au baka bada wannan maganin ne ? Ko dai damfara kuke yi bawai bada magani kuke ba duk wata me bada maganin gaskiya ba maganin da bata bayar wa balle wannan abin..,
zama tayi tana cewa aini ba yar iska nace da kake wannan maganar ka bari sai na fara tara yan iska sai na fara siyar da irin maganin nan..
ja da baya tayi ganin yana neman cimmata ta shiga daki a guje gaban ta yana faɗuwa
dariya yayi ya koma waje zama yayu akan benchi ba tare da ya bude shagon sa ba ya kunna Radio.
Wannan kenan..
Iya tsaruwa club din ta tsaru yan mata da samari sai tashewa ake yi masu shan shisha na sha a hankali taja ɗaya daga cikin kujerun da aka jeru a gurin ta zauna cire glasses din'ta tayi ta ajiye a gefe sannan ta cire facemask din'ta tace '' kai sauri ka faɗa min abin da zaka faɗa min bani da lokaci..,
dariya yayi yace '' uwar son kudi daga jin maganar kudu har kin dauko kafafuwa kin tawo idan da ace wani tarko na kafa miki fa...?,
murmushi tayi na gefen baki tace '' saidai ya kama ka kai kaɗai ban dani karka manta nidin wace da kuma kake cewa uwar son kudi kai da baka so ka zubar dashi a ƙasa.,
Dariya yayi yace '' lubabatu sheɗaniya..,
haɗe rai tayi tace '' kaga idan ka kirani ne nan domin ka ci min mutunci sai naji bayani na zo kuma banga wani abu ba kuma wallahi har kudin motar da na biya sai ka biya ni kudina..,
buɗe waya jaka yayi ya zaro bandir bandir na saifa ya ajiye a kan table zaro ido tayi tana kallon gefe da gefen ta tace '' T boy ina ka samu wa'yannan makudan kuɗaɗen..? wacce sana'a haka , ka fara..?,
kardai kaima ka fara tsafi ne , na shiga uku shikkenan kaima ka ɓata wallahi duk son abin duniya ta bana so na ganni na aikata irin wannan aiki dan Allah ka faɗamin ina ka samo wannan kuɗin..,
dariya yayi yace '' ko ɗaya ba abin da kike zargi na fara ba harkar alkairi ce idan har za kiyi to fa gida da mota sai dai ki bayar badai a baki ba..,
zaro manyan idanuwanta tayi tace '' t boy Ka fara bani tsoro fa lamarin ka akwai sarkakiya a cikin sa anya kuwa to me ka fara ka faɗamin gaskiya ni ba zan shiga abin da ba'a feɗe min biri har hutsiyar sa ba idan abin da nake tunani ne wallahi gwara na mutu cikin talauci ba zan saka kaina a wahala ba karshe ance rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ta me kaya lah laj barni a siye da siyarwa ta da nake yi arziki na Allah ne..,
Dariya yayi ya busa shisha yace '' matso raciya ke wallahi son kudin ki na banza ne..,
hmmm ina jinka faɗa min kuma ka bani kaso na , nabar nan gurin kafin na hadu da idon sani na shiga uku a dinga yawo dani kwararo kwaro ana cewa ga sénatrice can zama karuwa...
ke fa hallacan sun dade basu faɗa ba su daman mutane ana iya musu kawai idan zaki yi sabgar ki kiyi sabgar ki...
Chapter 8 · 0% Book details