Sashe 6
Mai Bada Magani Ko Yar Damfara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kofar dakin da saude take ciki mahaukaci nan , ta bugi gumi ne ya ƙara karyowa SAUDE ta kwantar da Usman ba irin addu'ar bata zo bakin ta ba tunawa tayi ai acikin daki take ta kirawo MUDAN mana da sauri ta ajiye usman ta dauko wayar ta laluban number MUDAN ta fara cikin Sa'a ta ganta danna mai kira tayi amma har ta katsai ba dauka ba ƙara kira tayi a wannan karon ya dauka kuka ta fashe dashi ta fyece majina tace '' dan girman Allah kazo ina gab da mutuwa idan har baka zo ba ka temaki rayuwata dan Allah MUDAN..., Cikin tashin hankali yace '' tun dazu na dawo daga masallaci ina ta buga kofa baki buɗe ba me ya faru..?, ƙare fyece majina tayi tace '' ka tawo da kartin maza kai ka tsaya daga soro karta kashe ka.., ita wa ya tambaya cikin sauri da zakuwar me za tace kuka ta ƙara rushewa dashi harda shashsheƙa tace '' dan Allah kazo bazan iya fadar komai ba yau ina ganin takaina.., kashe wayar yayi ya fito daga shagon sa , shiga cikin gidan su yayi ya biyo ta karamar kofa sai dai itama a kulle take dole sai da ya haura ba komawa ya gani sai mahaukaciya da take riƙe da muciya ta yiwa bishira jina jina ga sima nan ma bakin su duk ya farfashe sai hakuri da magiya suke bata jin takun tabiya ta juyo ja da baya ta fara yi gaban ta na faɗuwa. tsawa ya daka mata zama tayi jikin ta yana rawa kallar su sima yayi yace '' kuzo ku fice ko yanzu Ubangiji ya nuna muku ikon sa idan kunyi hankali ku gyara idan ba kuyi ba jikin ku ya kara faɗa muku.., da sauri suka tashi sima me kyau yace '' to oga ina ce ma hanyar fita..?, wani kallo MUDAN yayi masa bishira yace '' Allah ya gabatar ran malam yi hakuri.., dauke kai MUDAN yayi suka lallaɓa suka tashi cikin su yayi ruɗu ruɗu bib bango suka dinga yi suka fita. ganin sun fita da gudu mahaukaciyar nan ya fita cin karo tayi da wa'yanda suka kawo ta , ta dinga fisge fisge suka rike ta. MUDAN leƙowa yayi yace '' yauwa daman ku zan nema karta ɓata ba lallai ne tasan gari ba ta gama yi mata tofin tace idan kunga abu be yi sauki ba ku dawo abin sadaka kuma ku barsa.., ya faɗi haka ne domin ya rufa mata asiri tsohuwar nan tace '' mun gode Allah ya saka da alkairi dan Allah yaron nan kai mata godiya kaga sai fisge fisge take gwara mu tafi kar ta shiga cikin gidajen mutane abu ya muzanta.., cikin tausayin tsohuwar yace '' Allah ya bata lafiya ba damuwa za taji.., amin suka ce suka juya suka tafi ya koma cikin gida buta kofar dakin da take yake yi amma shiru ba alamun za'a buɗe baya son ɗaga muryar sa kar ayi zaton wani abu ke faruwa tsakanin su duk da ko da yaushe wannan halin SAUDE ne idan faɗan suna magana su kaɗai sai tai ta ɗaga murya hakan be dace ba ajiyar zuciya ya sauke yace '' SAUDE buɗe min ni ne na fitar da ita.., buɗa taga tayi ta haɗa uban gumi tace '' ka tabba MUDAN kar na fito naga ba haka ba.., kafe ta da ido yayi yace '' raina zai ɓaci ko..? tunda ai kinsan na sa ba yi miki karya. , sosa kan'ta tayi ta buɗe kofa hannu usman ya miƙo mai ɗaukan sa yayi yana shafa kan yaron ya zauna yace '' SAUDE idan na rantsai ba zan yi kaffara ba darajar wannan yaron kika ci da tuni kema ta kama ki.., zama tayi tana zunburo baki ta kauda kan'ta yace '' SAUDE kinga yanzu dai ki tashi kiyi wanka sai kiyi bacci ki huta kannan naki, yayi datti ki tsaife shi..., ɗagowa tayi ta kalle sa sai kuma ta tashi saboda yau halarcin da yayi mata duk da ko dacan din yana ƙoƙarin wajen cinta shanta ya faranta mata ita da , ɗan su. dawowa tayi tace '' babu ruwa.., daukan usman yayi yace '' zo ki karbe shi ba samu miki ruwan da zakiyi amfani dashi.., amsar sa tayi ya dauki botiki ya fita zama tayi a kan kujera yar tsuguno ta zuba ta gumi usman sai wasa yake tayi amma tayi banza dashi yau Allah ne ya auna mata arziki da tuni yanzu ruwan wanke gawar ta za'a debo. dariya ce ta subbuce mata lokacin da ta tuno ihun sima mahaukaciya na ce mai kai dan gidan sarkin aljanune tana cikin wannan tunani yace '' ga ruwan nan.., da sauri ta ɗago tace '' ungo shi..., karɓa yayi ya miƙo mata wata leda amsa tayi ta buɗe shampoo ne da shaving cream sai sabon toothbrush rufewa tayi bata ce komai ba ta wura wuta ta dora ruwan zafi tana tsifar kanta ba ƙaramar suma ce da ita ba sai dai kazanta tahana ta tayi kyau mai da dan kwalinta tayi ta zuba ruwa a cikin botiki ta shiga bayi. zama yayi yana jiran ta , ta fito ya koma shagon sa yana wannan tunani ta fito tashi yayi yace '' ungo sa zan buɗe shago kafin lokacin karatu yayi.., amsar sa tayi tace '' ko bari ba zakai ba na shirya..?, to kawo shi maza ki shirya dan Allah SAUDE ki fadi gaskiya baki ji daɗin jikin ki ba ko ta ina iska na shigar ki..?, wallahi sai kikai kyau.., da sauri tace '' to fito fili kace min bani da kyau amma ka tsaya kwana kwana.., murmushi yayi yace '' daga magana sai ki juya min zance ki maza ki shirya ki amshe shi.., banza tai mai ta shiga daki saka kaya tayi bata fasha mai ba balle ta gyara gashin ta , ta fito tace '' bani shi.., bata shi yayi yace'' zan turo abeedah tai miki kitso.., ajiye usman tayi tana cewa a'a wallahi ba kitson da zan yi daga wanke kai sai kace sai kuma kitso karma Ka kirawo ta nace ba zatai min ba kace na tozarta nan da anjima baki zanyi akwai wanda nai wa alkwari za su zo insha'Allahu dan haka bani da lokacin yin kitso. da sauri ya juyo da har ya fara tafiya lallai wanda Allah ya shiryar shine shiryayye kasa magana yayi ya juya ya ci gaba da tafiyar sa. zama tayi akan dokin kofa tana cewa da hallacan yiwa mutane shiru kamar ba ɗazu ka sha ba shi ne yanzu kake neman rigama wallahi baza ka sha ba na gaji kuma. da sauri ta shiga daki jin wayar ta nane man dauko ɗauka tayi ta kara akunne tace '' sénatrice barka da yamma hmm da tuni an sanar miki da mutuwar mu nida su sima.., da sauri tata shi daga kwanciyar da tayi tace '' innalillahi me ya faru..?, bata labarin komai tayi ta da ɗa , da cewa Wallahi da ace MUDAN be kawo mana dauki ba da yanzu sallar gawar mu ake yi kai yau naga bala'i kina ji fa matar murɗa wuyan mutum take shikkenan an gama sai dai uwarka ta haifi wani.., Dariya sosai sénatrice take yi tace '' wayyo Allah ciki na yau kin haɗu da gamon ki me MUDAN yace nasan ya tsine min tun daga sama har ƙasa ko..?, haɗe rai SAUDE tayi tace '' yanzu ina faɗa miki damuwata kina tambayar me mijina yace miki kinsan halin sa ai bashi da hayaniya ko sunan ki be kawo a zancen nan ba kuma nima da ya cece ni bece min kala ba , wallahi kin ban mamaki dariya ma kike sai kace ba ke kika fara tallata min wannan sana'ar ba.., da hallacan rufe min baki da na tallata miki sai kuma nace dole sai kinyi talauci ke damun ki nace mu haɗa hannu da hannu tunda ke kin shiga daga ciki ni yanzu ina fara sana'ar nan kallon karuwa za'ai min, bani da aure ina sai da maganin mata kinsan halin Mutane ba'a da gadon ka ana da na maganar ka amma duk irin hallarcin da nayi miki shine kike faɗa min maganar banza bakomai yanzu yaushe sima ya dawo daga Lagos ɗin..?, shiru SAUDE tayi domin itama ba kanwar lasa bace bata son faɗa dan tana cikin talauci sai ta dinga raina mata wayo ita gwara ita daga sama take cin kudin nan ita fa yanzu mutane ma bokanniya suke ce mata shine zata faɗa mata maganar banza. senatrice ce tace '' hello hello magana fa nake kinyi shiru ko matsalar network ne.., kamar tana gaban ta , tace ina jin ki tsayawa nayi ki gama faɗan ki, sanin kan kine ko MUDAN da yake miji na bana tsayawa yayi min faɗa balle ke har kina cewa na rufe miki bakina senatrice talauci ba hauka bane ai.. Eyee kinga bana son harkar bura'ubanci kinsani sarai ba'a nuna ni da yatsa balle a faɗamin bakar magana kinga abin da kika haɗa ki turo min ta my nita ki ɗauki takardar sai ki tura min ta wayar MUDAN tunda ke ba babba ce da ke ba , bani da lokacin da zan zo karɓar. to kawai tace ta kashe wayar shiga daki tayi ta ajiye usman da yayi bacci sallama taji da sauri ta fito tace '' sannun ku da zuwa kun sha hanya..., yauwa dai matan suka ce tare da gaishe ta shinfiɗa musu tabarma tayi suka zauna shiga daki tayi ta dauko magungunan ta ta fara bayani tana cewa wannan shi ake kira da sa kishiya kuka ba boka ba malam. amma shi saboda da zafin sa bana bawa me kishiya ai zai zama da cutuwa. da sauri matar tace '' dan Allah ki bani shi wallahi ina da kishiya ta kwace komai mijin ma wata rana ina ganin kwace min shi za tayi komai ita ce wata ran ma da sunan'ta yake kira na dashi sai daga baya ya canza.., girgiza maganin tayi yayi murɗik kamar ruwan dauri dakyar yake iya juyawa tace '' ku ne yan uwanta hakane dan wallahi saboda shu'umancin'ta sa bana son bayarwa.., magiya suka fara yi mata dakyar ta