← Book details Mai Bada Magani Ko Yar Damfara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 10

Sashe 7

Mai Bada Magani Ko Yar Damfara Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

basu suka bata kuɗin'ta suka tafi. ɗaukan hijabinta tayi ta goya usman abaya ta fita ba tare da ta tambaye shi ba tsaye gidan su sima ta nufa sallama tayi ta shiga sai zunduma ihu yake ana gasa mai gadon bayan sa domin ya daku iya dakuwa gaishe da iya tayi da sauri iya tace '' ashe kinji labarin tankar da ta kusan kashe salmanu.., zama tayi tace '' iya tanka kuma.., Wallahi cewa yayi babbar motar nan ce ta kade shi dawowa yayi yana wasu irin surutai marasa kan gado kalli gadon bayan sa duk a kwashe daman daga ganin wannan abu sai dai barin mota.., majiya sima ya fyece yace '' iya wacece fa zo..?, da sauri SAUDE tace '' sima murya tace baka gane ba.., yar kutumar uba ina zan gane muryar ki, ta iya bayan duk kece silar komai iya billahilazi, Iya ji nake kamar ban taɓa jin dad'i a duniya ba.. da sauri iya ta kalli SAUDE tace '' SAUDE me yake faruwa kinsan wanda ya ajiye tankar ne kome ya faru.., haba iya kalli bayan yaya salmanu sosai ki kura mai ido wannan ba wani barin mota mutum ne.. da sauri ya dago daga kwanciyar da yake yace '' to shegiya uwar bakin hali tsaka uwar munafukan duniya annabi yayi gaskiya da yace duk inda aka ga irin ku a buge shegu a huta dan uwarki zaliha a gaban ki abin ya faru..?,kuma kici gaba da cire ni daga cikin jin sin ku.., turo baki tayi ta shiga daki da sauri SAUDE tace '' sima na kasa fahimtar komai wai bayan fitowar ku daga gidana babbar mota tai barin makauniya dakai ga bakin ka tamkar na jaɓa yayi dogo.., dauke kai yayi yace '' iya dan Allah dauko min zani na yanzu salon wani ya shigo ya ganni ba kaya ni daman kirji ba kirji ba a gama gane min yan kirga dangina.., SAUDE ta tash ta miko mai iya kuwa banza tai mai ta tashi ta shiga daki ƙasa ƙasa yace '' ko da wasa naji kin fadi abin da ya faru yasin zaki sani ne sai na yi miki bura'uba domin ke na saito bane dake abin kunya ne ace an kama mu, an dake mu ke ya kamata ace ta tumurmusa saboda ke kika fara tabo ta da baki mata tofi ba da duk abin be kasan ce haka ba ke gaki uwar iya gwana ta gwanaye Allah ya rufa mana asiri daba kar mu ba yasin na so ta sauke miki muƙamuki.., kama haɓa tayi tace '' sima ni kake faɗawa haka..?, na fada miki din kanwar uwata ce ke ko ta ubana ina cewa kai ni kikai inda za'a halakar da ni.. a fusace tace '' karka sake ka faɗa min maganar banza ni nace maka kazo matar nan naga ku kuka kawo ta ina cikin kwanciyar hankali na kuka kawo min jaraba ina dakin nan har gudawa na saki ban san ma nayi kashi ba sai da nazo wanka na gani.., dariya ya sheƙa da ita yace '' to aike naki me sauki ne nida ta hadani da jinsin aljanu ke kinga yadda ta dinga zuba min sanda kai wannan bata da imani ko kaɗan..ni wank abin ba wallahi ban san ina fadi ba kawai zuwar min baki na yayi bishira me kyau yace dan annabi tanko kiyi hakuri ki barni da raina wallahi duk da banyi karatu ba nasan kawai ya faɗa ne bawai akwai shi ba , amma abin mamaki sai ta barshi ta dawo kai na shine nima na dinga dan annabi tanko kiyi hakuri SAUDE na zabtu tamkar tura ta naki ta dinga duka na tana rawa tana cewa Annabi Tanko.., saude saboda dariya har faɗuwa ƙasa tayi hade rai yayi yace '' kaji yar masara muguwa me makon ki ta yank jimama mi shine kika dariya.., cikin dariya tace '' dan annabi tanko sima kaf cikin annabawa babu tanko.., banza yayi mata tashi tayi tace '' bara na leƙa bishira naga me yake faruwa iya sai an jima.., fitowa tayi tace '' to sai an jima ki gaida mijin naki Nagode sosai wallahi kaf makotan nan nawa nasan ba wanda zai zo dubiya amma ke daga ji kin zo yar albarka.., yaushe kuwa za su zo wannan yaron da ana canza shi da tuni wallahi na canza shi tabawa yanzu har tsoran tafiya masallaci nake an dinga nuna ni da baki idan na zo wucewa a nuna ni da baki ba mutum kake ƙi ba halinsa kake ƙi..
Chapter 7 · 0% Book details