← Book details Mai Bada Magani Ko Yar Damfara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 10

Sashe 2

Mai Bada Magani Ko Yar Damfara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sénateur ta faɗa tana murguda bakin ta.
Allah ya kyauta yanzu sai yaushe zaki dawo.
cewar saude
kallon rufin dakin saude tayi duk azara wani gurin ya tsake tace '' kinga saude ki rufawa kanki a siri ki dena zaunawa a dakin nan kar fa wata ran ayi ruwa ƙasa tayi miki rubuti kisha uban duka...,
kallon gurin tayi tace '' abban usman yace min kuɗi yake jira su shigo mai zai gyara mana yana riga da ya samo kasa kawai kudin aiki zai bawa masu aiki su fara...,
hangame baki tayi tace ''bazai saka muku plafond...ba yanzu fa shi ake yayi kai amma *MUDAN* naga lokacin da zai waye kullum duniya ci gaba take amma shi yadda kika san an tusa kansa a cikin bakar leda..,
hmmm kya faɗa kullum bashi da aiki sai Allah ya wore min zanyi idan baka tashi ka nema ba ta ina zaka samu kina ga abokinsa shazali ga uban gidan da ya gina a maradi gari guda ne har da wannan abar ta zamani douche 🚿 ya saka musu...,
sai dai ki hakuri da irin taki kaddarar shi yasaka sai na zaɓa na darje tukunna zan yi aure yasin ina dalili haka kurum da kuruciyar ka , kaje inda zaka koma tsohuwa wani wanda be kula ba sai yace gwaggo ina huni nan kuwa besan talauci ne ya kashe maka jiki...
rausayar da kai saude tayi kawar tata na ƙara bata sha'awa tace...'' muje na raka ki...,
Sénateur (senator) gaba tayi ba tare da tace komai na saude na binta a baya dakyar ta iya tsallaka katuwar kwatar dake soron gidan tana yatsuna fuska ranta duk ba dad'i domin sénateur ba dai tsafta ba suna fita MUDAN na zauna da Kur'ani a hannunsa shagon nan ba mutum ko ɗaya to kayan shagon ma nawa yake ƙatuwar motar da ta kawo sénateur ce me rai da numfashi ta matso inda take da sauri *Chauffeur* (driver) ya fito jikinsa na rawa ya buɗe mata baki saude ta buɗe tana jinjina kai kallon MUDAN tayi ranta yayi baki kyakkyawa ne domin kusa buzune amma kyawunsa be amfana mata komai ba a nata ganin idan dai mutum da kuɗin sa to ko bakar leda ne fari ne ita bata san wacce kaddara ce ta waɗa mata ba ta kasa tan tan ce me ake nema a gidan aure ta aure MUDAN dafa kanta tayi da lokaci ɗaya ya sara mata shiga cikin gidan tayi tana jan karamin tsaki.
duk a binda ke faruwa be sani ba saboda hankalin sa yana kan karatun da yake sallama aka yi mai ajiye Kur'anin yayi ya amsa sallamar yace '' Alhaji Mamman yau kai ne a gari..?,
zama Mamman yayi a kan teburin MUDAN yace '' abin naka har da zolaya wanne alhaji kuma ana zauna qalau ga kunnan manyan alhazawa..,
murmushi MUDAN yayi yace '' masha Allahu mun godewa Allah. amma dai kai kasan yanka ta kake ya hanyar..?,
hanya alhamdulilah ina yaro na Usman
Mamman ya faɗa yana duban MUDAN
Wallahi yana cikin gida be dade da gama rigima ba na kulle shagon na kai shi gida to ba jimawa yayi bacci.
Allah sarki, Allah ya albarkaci rayuwar sa
amin ya Allah ina iyalin naka da fatan dai kowa yana lafiya
Wallahi suna lafiya qalau, yar hira suka taɓa sannan yayi mai sallama ya tafi kulle shagon yayi ya shiga cikin gida ko sallamar da yayi bata amsa ba ta zauna ta kwashe cinyoyi tana kallon tulin maganin da sénateur ta kawo mata ta tafi duniyar tunani domin kuwa sai lissafi take tare da faɗar yadda za a yi amfani da su domin kar ta manta wanda bata faɗa mata ba ta ajiye shi a gefe guda. shiga cikin dakin yayi ya zauna saude ba mummuna bace kazan tar da take ita ta munan ta , ta domin kallo daya zakai mata kasa ta a sahun kyawawa ajin farko Allah yayi mata diri yar kanwar mahaifiyar sa ce mahaifinsa buzune gidan su babban gida ne irin gidan nan na gado dakin wannan yana kallon na wannan, basu da arziki domin sana'ar gidan su malinta sanin kowa ne idan malami ba zai fita ya nema ba to lallai yana tare da babu, sai azumi suke mun dan wani abu na kuzo a gani idan ba lokacin azumi ba lokacin fidda zakka bayan haka ba abin da suke samu to wannan hali ya taka rawar gani gurin gada musu talauci wasu daga cikin ya'yan gidan ne suke fita cirani zariya, Sokoto, musamman ma kano domin kusan cibiyar kasuwanci ce....

Mudassir su hudu ne a gurin malam iliyasu me ishiriniya akwai sulemanu sai mudassir sai kuma jimmala da hadizatou dukkan su , suna da aure mahaifiyar su laure itace matar iliyasu me ishiriniya ta farko Allah yayi mai auri saki dan haka yana da ya'ya sosai sai dan uwansan malam salihu shi kuma matar sa daya da ya'ya bakwai dukkan su suna zaune a cikin gidan har da kakanin su haɗin zuminci akai da saude da MUDAN to daman ance matar mutum kabarin sa baya ra'ayin'ta haka dai ya aure ta rabon yaron dake tsakanin su , babban abin da ke damunsa da ita kazanta ga taurin kai tamkar jinjirin jaki...
idan ta saka kanta a gabas to fa ba wanda ya isa ya dawo dashi yamma duk da wannan matsatsi da suke ciki MUDAN yayi ilimin boko da na addini idan mahaifinsa baya nan yana koyar da mata sa da mahaifinsa ya ga haka sai aka raba karatun shi ya koyar shima ya koyar..

dagowa tayi suka haɗa ido murguda mai baki... tayi tace '' malam lafiya wallahi Allah idan ma dawowa kayi ka ƙara to wanda kayi cikin dare ma ya isa haba aita abu ɗaya nifa da nasan haka lamarin nan yake yasin da ban yarda da auren nan ba...ni Allah ya gani bazan iya da wannan bakar jarabar ba.,
kauda kansa yayi bema nuna mata ya san me take fadi ba MUDAN akwai hakuri da juriya kafin ka gane kamilar fuskarsa me take nufi to lallai zaka kwala yace '' kin dora sanwar rana ne..?,
a'a yau aiki yayi min yawa Alkur'ani ba zan iya ba ka nemowa kanka abin da zaka ci..
tashi yayi be ce komai ba ya fita wata yar durkusasshiyar kofa ya shiga sai gashi ta sada shi da ɓangaren iyayen sa be tsaya ko ina ba ya wuce dakin mahaifiyar sa bayan sallamar da yayi musu wanda yake tsakar gidan ya amsa zama yayi tare da gaishe ta , tana zaune tana cin kwaɗon rama ajiyewa tayi a gefe ta amsa gaisuwar sa tare da yi mai bisimillah
kawaici irin na mudassir kawar da kai yayi yace '' alhamdulilah..,
bawai dan ba zai iya ci ba a'a shi be kawo musu ba sai ya ɗauke musu... yaci,
ci gaba da ci tayi ganin yayi shiru ta ajiye robar hannunta ta sanshi sarai da mugun zurfin ciki tace '' lafiya MUDAN me ya faru kardai wannan mahaukaciyar yarinyar ce ka dena saka damuwar ta a ranka kana zaune mahaukatan kawayen ta zasu koya mata hankali...,
murmushi yayi yace '' a'a mamma ba ita bace kawai dai nayi shiru ne..,
hmmm Allah ya kyauta
ta fadi haka tana ji manta lamarin saude da kullum baya raguwa sai karuwa cikin sauri ta dago tace '' ashe daman saude ta zama bokanniya ba mu da labari kai wannan jarabar son kudi ta saude ta kai inda takai yanzu abin da ta tsira sai ta dinga tattara yaran matan unguwar nan tana musu huduba tare da basu magunguna da yake su jakai ne idan kura tana maganin zawo tayi wa kanta mana shi ne suke biye mata..wai dai jummai tace har manya zuwa suke tana basi ararrabi da bagaruwa tana cewa maganin matsi wai kuma maganin yi yake jummala da yake yar gidan tace, tace har dorawa take kadawa ta basu susha wallahi ina jiye mata randa hukumar kula da lafiya za tayi dirar mikiya a cikin gidan ku
ajiyar zuciya ya sauke yace '' mamma wallahi na rasa yadda zanyi da ita dazu ma sai da mukai wannan maganar dan haka kawai na zuba mata ido har lokacin da zata ga ishara abin tsoran shine ranar nan har mahaukaciya aka kawo mata karfa wata ran aljanu su nannade ta..,
ni wallahi da zasu nan nade shegiya ta yi hankali daba haka ba
mamma ta faɗa ranta a ɓace
shiru *MUDAN* yayi domin yasan ranta ne ya ɓaci ya saka ta fadi haka.
tashi yayi yace '' sai anjima mamma..,
to Allah ya kiyaye hanya
amin ya Allah.. ya faɗa yana fita kai tsaye cikin gidan sa ya shiga ransa ne ya ɓaci ganin taron mata ko wacce tana ganin sa ta fara tsinke kai tare da gaishe shi amsawa yayi ƙasa ƙasa ko a kwalar rigar saude kallon matar gaban ta tayi tace '' kinga wannan hmmm shi ake kira da ƙare mana wallahi ko baki kika nuna mai kika ce fari ne to ya zama fari can ciki zaki tura kinsan idan kika kama miji ta gurin shinfida kiga komai..,
ke dan manzo matar ta faɗa tana washe baki
gyara zama saude tayi tace '' daga garin nan maleshiya aka kawo min kinsan turawa ba dai iya riƙe miji ba to wannan shine sirrin nasu.,
to yanzu nawa ne kuɗin sa
Kar kata daurin kanta tayi tace '' *Cinq mille* ...,
Chapter 2 · 0% Book details