← Book details Mai Bada Magani Ko Yar Damfara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 10

Sashe 4

Mai Bada Magani Ko Yar Damfara Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Bishira ce ta cire zanin'ta da dan kwalinta tace '' sima riƙe me ai daman ita daudu riga ce yanzu sai na cire ta na ci kuttumar uban ka zuwa gida nan kuma yanzu muka fara tunda ba gurin ka muka zo ba har mu zaka nunawa bulala baka san *idan kaji ƙi gudu hakika ban ƙaraso bane ni kura uwar kare, Ni wallahi tuwon ƙaya ne maganin me haɗama ba gaba da gaba ba ni mazan suke gudu kuma ni suke tararwa a gaba Allah ba kyau ba dadin gamo dani..*
wani naushi mudassir yakai mai dafe kuncin sa yayi yana zunduma ihu tare da fita a guje ganin haka sima ya cika zanin sa da iska ko kayan wainar sa be tsaya ɗauka ba juyowa gurin saude yayi ransa a ɓace ya nunata da yatsa yace '' wallahi idan har ba zaki dinga jin magana ta ba zanyi maganin ki saude daga yau sai yau ƙarna ƙara ganin ƙafafuwan wa'yannan yan daudun a gida na..,
ganin yadda ya fusata tuni ta saita kanta fita yayi yana fita ta goya Usman a baya ta leƙa waje haɗa ido sukai da sima da bishira da kumburarran kumatu suma suna leƙowa harara ta zabga musu tace '' aikin banza wallahi kin ban mamaki ashe cika baki ne maza zo ki ɗauki kayan ki...,
ƙarasowa sukai yace '' ke wallahi bawai karfina ya fi ba gudumar da yasaka min ya bugar min fuska ce taya za'a daki mutum da guduma ace ba zai gudu ba har taurari na gani..,
dariya sima da saude sukayi sima tace '' lallai kinji jiki da hannunsa ya dake ki..,
da sauri ya juyo jin alamun tafiya yace '' maza maza bani kaya'na , na bar nan gurin kinsan zama gu ɗaya tsauysayi..,
shiga tayi ta dauko masa kayan sa dana sima tafiya sukai ta shiga cikin gidan ta zauna tana ɗaura magani tana yar wakar ta.
mudassir ne ya shigo sallama yayi kallon inda yake ba tai ba ta ci gaba da abin da take buɗe doro din ruwa yayi zai zuba yayi alwala gani yayi babu da sauri ya ɗago yace '' saude ba ruwa a cikin gidan nan..?, badai wanda na ɗebo har ya ƙare..?,
ci gaba tayi da abin da take bata kula shi ba sai da ya ƙara maimaita mata maganar da sauri ta ɗago tace '' mudan me kake nufi fito fili kace na tara mata sun maka barnar ruwa abin da ke zuciyar ka kenan wai kai dan girman Allah mudan me ya saka kake yawan saka min ido a cikin sha'anina dazu ma su kawa suka zo ka ci musu mutunci ka kora su haka ya dace..? yanzu kuma ka buge da cewa ruwan da ka ɗebo har ya ƙare..,
Kasa magana yayi domin abin nan na saude sai addu'a yawa wata me iskokai.
daukan butarsa yayi ya fita ci gaba tayi da hada maganin ta duniyar ta shar bata da wata damuwa jin alamun kamar ana jan mutum yana turjewa ta miƙe ta leƙa soro tace '' sima bishira lafiya naga kuna ta bin bango wannan mahaukaciyar ina kuka samo ta..?,
jaka sima ya saɓa a hammata ya yarfe hannun sa yace'' wallahi kinga a hanyar kukar iya na gano wa'yannan mutane wai gidan saude me maganin aljanu suke nema..nace faɗuwa ta zo dai-dai da zama nasan gida shine na danni kirjin aunty bishira muka dawo kinga idan anyi *Équilibre* kin bamu namu rabon..,
gaban tane ya wani yau take ganin jarabar rayuwa ya za tayi da wannan mahaukaciyar sai zare ido take tana galla mata harara ja da baya tayi tace '' bisimallah ku shigo kubi ta a hankali har ta shigo Allah ya saka ma sauran aljanun sun makale a kofar gida da baza ta taɓa iya shigowa gidan nan ba ..,
Wallahi malama haka muke ta fama dattijuwar ta faɗa tana share kwalla da ya'yan ta maza biyu.
saude kan'ta ya kara fasuwa tace '' karki damu inna zanci uban su dan durin uwar ku ba zaku cika ta ba kai me katon kai har hararata kake ko...? to maza cika ta ko na kona ƙona ka..,
sami da bishira da suka choge a baya suna liƙowa suka hada ido suka jinjina kai wani ikon Allah sai ga mahaukaciya ta shigo cikin gidan da sauri suka shigo tace '' sima maza rufe min kofa bishira rufe min kofar bayi karsu samu damar shigowa..,
da sauri sima ya rataye mayafin sa ya tafi zai rufo kofa sai ga MUDAN nan ya shigo da sauri ya matsa yana sosa sumar sa da ta sha relaxer ratsa shi MUDAN yayi ya wuce ransa duk a ɓace dattijuwar matar nan tace '' ina wuni..,
da sauri MUDAN ya tsuguna yace '' ina wuni inna mun wuni lafiya..,
Lafiya qalau dan nan gaisawa sukai da sauran yaran nata da sauri SAUDE ta bi bayan sa domin kar ya kwance mata zani a kasuwa me makon ya shiga daki sai ya fita bin bayan sa tayi suka tafi soro cikin matsanancin ɓacin rai yace '' SAUDE har yanzu she zan dena nanata miki magana ɗaya ne..?,
turo daurin ta gaba tayi tana sosa kitson ta da ta haɗe ko tsaga ba'a gani tace '' sai ranar da ka dena yi min hassada a cikin gidan nan bansan ina ka dosa ba ..,
Kekai bansan ina kika dosa ba wa'yannan yan daudun da kika ƙara gayyato su me na fada miki ɗazu..?,
kauda kan'ta tayi tace '' na manta tuni nake buƙata..,
ɗaga hannu yayi zai zabga mata mari sai kuma ya damke yan yatsun sa ya dunkule su gu ɗaya juyawa yayi ya fita ba tare da yace komai ba,
saita kan'ta tayi tana gyara daurin zanin ta , ta shigo tace '' inna sannu na barku kuna ta jira..ko..?,
Dattijuwar tsohuwar nan tace '' wallahi bakomai a haka ma kina kokari abu ba mutum ɗaya ba , ba mutum biyu ba ..,
zama tayi tace '' to ya za nayi harkar temako ce tun da mahaifina ya mutu ya barmin wannan harkar ta temako yanzu ma wallahi wani me lalurar aljanu aka kawo min daga Cameroon to na gaji yamma ta kawo kai nace su dawo sai gobe...,
Allah sarki sannu yar nan shi ya saka naji muryoyi kala kala kamar na faɗa.
gyara zama saude tayi kan'ta ya fasu tace '' yauwa idan da kin gan sa sai kin tausa ya mai wallahi kinga yadda yake rubos abin aba'a cewa komai..,
Allah dai ya yemake mu yasa ka mun zo a Sa'a
Cewar dattijuwar matar nan
SAUDE tace '' amin ya Allah aikin mu tamkar yankan wuka ne yanzu dai me yake damun ta..,
guri su sima da bishira suka samu suka zauna suna jiran suji me za'a ce domin har ga Allah sun fara jin tsoron SAUDE.
wani namiji wanda yake riƙe da mahaukaciyar da take ta fisge fisge yace '' wallahi tun da taje ɗiban ruwa a rafi shikkenan fa aljanu suka fyaɗe ta bamu kara sanin inda kan'ta yake ba duk wani guri munje sai aka yi mana kwatance wajen ki duk wanda ta daka da hannun ta sai ya sami karaya idan kuwa ta damfara mutum da ƙasa to wallahi shikkenan sai dai wani ba shi ba a garin mu, mutane da yawa sun mutu ta dalilin ta har cin mutum take ta gwaguyo naman sa...tas tabar ƙashi.
wani irin gumi ne ya fara karyowa SAUDE ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba gashi duk ta saka an rufe kofa wani irin yawu ta hadiye me kauri ta fara kifta idanuwa yawa wanda tayiwa sarki karya ci gaba zai yi da bayanin sa jikin SAUDE a sanyaye ta daga mai hannu domin zancen da yake yi ba ƙaramin saka ta cikin rudani yake ba kai ya gyaɗa su sima kuwa ta kurewa sukai guri ɗaya kamar kace ket su gudu.
bagaye tayi ta dauki buta wacce MUDAN ya shigo da ita ta zuba ruwa a hannun ta ta fara motsa bakin ta nan kuwa ba abin da take faɗi in banda innalillahi wainna ilaihir raji'un tana kasa da idanuwanta domin wannan mahaukaciyar ita take kallo tana cure hannu guri ɗaya tsoran ta ɗaya karta cinye mata naman kwakwalwar ta gwara idan karaya ce da sauki akan mutuwa wani ihu ta saki da sauri sima ya tashi yace '' kai ina wallahi bazan iya zama ba kai Bashir idan zaka tashi mu tafi ka tashi yawa wa'yanda aka ɗaure mun zauna hantar ciki na daddatsawa..,
kifta musu ido SAUDE ta fara domin idan suka tafi tana cikin wani irin mawuyacin hali bishira yace '' Bashir gatsal ka mai dani namiji.. billahilazi ba inda zani sai naga kwal uwar daka zama daram yana me nakuɗa ko dan na cusawa wancan mutumin takaici..,
Idan kai baka guma mai takaici ba to wallahi zama a gurin nan zai guma maka takaici zaka hadu da dana sani na har bada idan ma ka rayu kenan cewar sima..
yaƙe SAUDE tayi ganin kar suga ba tai wani abu ba karkata buta tayi ta dan motsa bakin ta ta tofa yawu a ciki sannan ta watsa wa mahaukaciyar nan wani girgiza tayi sai kuma ta kame kam.. tace '' inna ko zaku shiga daga ciki ko kuma kubi wacce siririyar kofar ku fita sai ku kullo zanyi aiki ne..,
cikin sauri suka cika ta suka fita domin suma cikin su ya duri ruwa ita kuwa SAUDE tayi haka ne domin ta samu ta kubuta itama guduwa za tayi shaf ta manta da batun usman da yake bacci a bayan ta takan ta kawai take yi gadai mahaukaciyar nan tun da ta kame bata ƙara wani motsi ba saita ta tabbatar sun fita tace '' bishira muyi takan mu yau ka kawo min jaraba har cikin gida na..,
ai karawar ta ke da wuya mahaukaciya ta miƙe taka zuba uwar miƙa taku ɗaya tayi gidan sai da ya amsa kan SAUDE ne ya shiga juyawa bishira kuwa da sima ihu suka saka da ruruwa ganin mahaukaciyar na yowa kan'su
Curewa sukai gurin ɗaya yayin da sima yake kokarin kwacewa daga rikon da bishira yayi mai ganin za ayi babu ya ga tsara mai cizo cikin fitar hayyaci bishira yace '' wayyo Allah shikkenan yawa ta kare wallahi ta cije ni..,
ba ƙaramin tashin hankali SAUDE taji ba da wannan zance jikin ta ya soma rawa ga mahaukaciya sai za gaye su take ba damar guduwa share kwalla tayi tace '' Allah ya shigo da MUDAN ya ceci rayuwa ta yau ina ganin ta kaina..,
sima da ta fyece majina yace '' kike gani ko muke gani annabi yace imanin ɗayan ku ba zai cika ba har sai ya sowa kansa a binda yake sowa dan uwan sa amma shi ne da yake , ke yar kwal ubace kike fadar haka..,
za kuyi shiru ko sai na tura kanku cikin masai.
cewar mahaukaciyar nan
tsit sukai tamkar ruwa ya cinye su sima ya kama baƙin sa yana zare idanuwan'sa ba irin addu'ar da be ba ji sukai ana girgiza kofa wani sanyi ne ya shige zuciyar su dan ganin me ceton su yazo da sauri wannan mahaukaciyar ta doka tsalle ta fita a guje tana cille da robobin maganin SAUDE kafa me naci ban baki ba daki SAUDE ta shiga a guje sima ya tafi madafa yana zare idanuwan'sa da wata ƙatuwar tukunya wacce akai bikin kanwar mijin SAUDE suka ajiye anan basu dauka ba ita ya shiga ya rufe kansa da murfin tukunyar domin a ganin sa ba me iya gani shi.
bishira suka bari a tsakar gida yana fyece majina tare da ihu domin ba wajen boya ko ina sun rufe.
ɓare baki yayi yana cewa ya MUDAN ya MUDAN kazo ka cece rayuwa ta wannan mutanen makiya, Allah ne la'anannu in banda tsinancewa mutana tare da ku, ku gudu ku barni..
Sima da yake cikin tukunya yaji irin ihun da bishira me kyau ya zage yana yi mahaukaciya na dura ashar sai yaji cikin sa ya kulle saboda tsabar dariya da ta ciyo shi ya zage ya koma gardi sak.
kofar madafa mahaukaciyar nan ta ja , ta tsaya saboda jin kusur kusur shiga tayi ta dauki zabgegiyar muciya ta buɗe murfin tukunya ta soma raɗawa sima bare baki yayi yana gurza ihu tare da tara hannu a ka hannu ta saka a baki tace '' dan ubanka yi shiru..,
bakin sa a fashe fa majina da hawaye sai zuba suke ya kama bakin sa yana gyada kai..,
shikkenan yasan irin tasa kaddarar kenan Allah ya fitar dashi ashe a fili yake fadi da karfi wata dariya ta sheƙe da ita tace '' dan ubanka ba kai ne jikan mirze dan gidan aljani bindu..,
ai besan lokacin da wage baki ba ya saki kuka tace '' wallahi sunan babana yunusa sani baban gida ko sau daya bamu hada dangi da aljanu ba..,
rufe min baki makaryaci yau za kuci uban ku har na cikin daki bazan kyale ba sai na bawa aljanu jinin ku sun shanye..tas yan iska
SAUDE jin hakan ke da wuya ta ɗora hannu aka tana sakin siririn kuka yau tana ganin ta kan'ta usman ne ya tashi sanin halin yaron yana da ihu sosai idan ya tashe ba'a bashi a abinci ba dan haka tayi sauri ta sauko shi ta ciro mama ta bashi yana sha tana kuka tana riƙon Ubangiji ko dan wannan shayar da yaron da take Allah ya kawo musu dauki cikin gaggawa kafin aljanun su zo..,
Chapter 4 · 0% Book details