← Book details Mah Noor My First Wife Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 27 OF 39

Chapter 2

Mah Noor My First Wife Part 1 Complete Hausa Novel · about 15 min read

MrsUsman400
For You Jikar kulu
BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
*Great joy to see your enemies turn into your lovers, Great sorrow to see your loved ones turn into your enemies*
Girgiza kai yayi cikin sanyin jiki, yana kallon Dr, bai barshi ya kai karshen Maganar shi ba, yace.
"Ina da ra'ayin SOYAYYA! Bana son hada shi da wancan abun ina son na bata damar ta fahimce ni, yadda zata nime ni da kafarta bawai na nuna fin karfina akanta ba.
Shi kuma wancan d'an iskan kyale shi lokaci nake jira akan shi. Idan yazo zan bashi damar haka.'
"Amma for your health!"
"Karka damu, a da nace maka zan tawo da ita ban san wacece ita bane, sai da na binciko labarinta, na fahimci wacece ita.
Zaman jinyarta kawai ya sani kara nutsuwa da ita, bawai dan wani abu ba,
ba zance am in love ba, amma am feeling sumtins akanta yadda take rigimammiya, bata da tsoro.
Duk abinda zata yi kai tsaye take yi, wich means anyi raised
inta haka ne, so nake ta koma kasa da ni, yadda kowa na nime aurenta zata dauke ni a matsayin mijinta, idan nace zan yi abinda kake bukata, dama ta rena ni ba wani jin dadin zaman zanyi da ita ba. Shi yasa na ki kawai ka barni da ita, Insha Allah zan duba Alamarin."
Wannan ra'ayin rikau na Mahir da ban haushi yake, dan haka Dr ya kama kafar ya nad'e da bandaji, sannan ya gyara mishi, yana jin shi yana nishi, suka kuma fashe da dariya, kafin Mahir yayi wani kara irin na jin jiki.
Tana waje sai zarya yake kamar wacce ta aikata mugun abu, fitowa Dr yayi ya same ta a dame.
"Hmm! Ayi a hankali dashi domin kafar ta kwa
e, kuma ina dai kin san ba zaki kula dashi ba, na kira familyn shi"
"No-no. Zan iya kula dashi, don Allah karka bari su sani." Ta fa
a muryanta na rawa, kad'a kai yayi ya ficce daga cikin gidan, a hankali ta shiga d'akin, yana ganin ta ya dauke kan shi kamar bai ganta ba, cikin sand'a ta shigo dakin tana kallon yadda aka daure kafar,
zare medical glass din shi yayi tare da kuma dauke kai.
"Ina son ruwa zan sha magani!"
Da sauri ta juya gurin dan karamin frij da yake dakin yace.
"Bana son me sanyi."
Fita tayi, ya sake murmushi yace.
"Zaki dawo ki koma."
Tana shigowa,.ya dube ta daga sama har kasa yace mata.
"Ina kofin da zan sha ruwan?"
Juyawa tayi ta fita, can ta kuma dawowa..ya dauke kai kamar bai san da ita ba.
Haka ta bashi ruwan ya sha, kafin ya jefa VC ya kuma korawa da ruwa.
Tana tsaye kamar status, bata ko matsa ba, sai da yace mata.
"Yanzun haka zan zauna da kafa daya? Gashi Dr yace idan kafar bata warke ba za a iya yanke min shi!"
Cikin wani irin faduwar gaba ta kalle shi. Bakinta yana rawa,
Gyada mata kai yayi idnun shi kwal-kwal, akanta kamar zai yi kuka.
"Am sorry!"
"Please give me a Little hug!"
Ya mika mata hannun, buge hannun tayi cikin masifa da damuwa tana fadin.
"Ko tausayin
kanka baka ji, kana niman magana."
Fita tayi, tana nazarin me zata bashi yasha domin ance duk lokacin da mutum ya kone yana bukatar abu me sanyi dan haka ta dauko fresh milk, ta zuba a kofi ta kawo mishi, ya sha.
Har zata tafi yace mata.
"Idan zanyi fitsari ko pupu waye zai raka Ni?"
Dafe goshinta tayi tare da cewa.
"Kai kan da kunya kabi kudu yabi yamma. Ba zan zauna daki daya da balagagge ba."
Ta juya tayi ta fitarta,
tunda ta koma d'akinta ta kasa sukuni, bata minti talatin zata zo duba shi, dan renin hankali yana kwance kamar me barci idanun shi biyu.
Ganin har karfe biyu saura tazo duba shi, har dai dai inda yake kwance..tazo duba fuskar shi, kawai ya fincikota. Tare da matse ta a jikin shi.
"Don Allah sake ni!"
"Shiii! Just sleep!"
Ya fa
a mata a hankali,
haushi ya bata ta kai mishi cizo, shi kuma ya sake mata wani irin nishi a kunnenta sai da tsigar jikin ta ya mike tayi shiru, tare da jin wani irin kasala ya saukar mata once, murmushi jin dadi yayi tare da gyara mata kwanciya, kasa barci tayi..yana jin bugun zuciyar ta..har zuwa lokacin da barci yayi gaba dashi. A hankali ta juya yana kallon shi. Idan ta tuna lokacin da yake bata wahala sai taji ranta ya b'aci, a hankali ta zame daga gadon. Tayi ficcewar ta.
Yana jin haka , ya sake murmushi, yana jin dadin yadda take kokarin kame kanta, da wata yarinyar ce tuni ta sake jiki dashi amma ita ta kasa sakin jiki dashi. A hankali ya cigaba da barci.
....itama a d'akinta kasa barci tayi sakamakon kamshin turaren shi da ya rike mata kaya, haka tayi ta juyi, har kusan karfe uku,kafin barci me nauyi ya dauke ta.
Da asubar farko, ta tashi ta gyara jikinta, sannan ta dauko kitchen
in ta ha
a abin karyawa tsaf, ta kai falon sama, ta jera mishi sannan ta koma d'akinta ta kwanta, bata kuma farkawa ba, sai karfe goma..tana jin kamar ana sa'in'sa, a hankali ta tashi zata fito. Taji Muryan Mahir yana fa
"Ina ruwanka da rayuwata? Na tab'a bin rayuwar ka? Har kai ka isa ka nima min abokiyar rayuwa? Dat's my Opinions ba wani ne ya isa ya nima min mace da karfin cin tuwo ba. Ko ce aka akayi Ni Womeniser ne?"
"Mahir kana boye wani abu a cikin gidan nan naka?koma meye We shall see, aure kuma kasaka a ranka zaka yi shi domin kuwa Zoolfa itace mafarkin Hajiya."
Wani wawan shak'a ya kai mishi tare da wullo shi waje, aikuwa take mara mutunci, ya cigaba da gaya mishi magana har da kiran shi dan luwadi, wannan kalmar ta dame shi ainun domin ko bayan tafiyar Nazzir, tsakanin shi da Allah yaji ciwon abun dan haka yaga Noorh sanye da wata doguwar rigar English wear, kawai yana tashi ya nufe ta.
A hankali take ja da baya, yana kuma Binta har suka isa bangon falon, kafin ya zuba mata idanu, dauke kanta tayi daga kallon shi.
"Wai ni d'an luwadi ne?"
"Wallahi ban san kome ba a wannan rayuwar don Allah ka barni na tafi gurin dangina!"
"Idan na barki zaki dawo gare Ni?'
"Cab'ijam, me zanyi maka me zan karu da kai Ni dai ka barni na tafi gurin dangina."
"Ba zaki tafi ba, sai kin gaya min zaki dawo gare Ni!"
"Wallahi gwara na mutu da a dawo gare ka, akan me?"
"Me nayi miki? Meye laifinta? Meye laifi" yana tambayar a haukace, wani irin aazabebben tsoron shi ya kamata,
dan haka a takure ta kalle shi.
"Don Allah ka rabu dani, meye nayi maka da ba zaka hakura ka yafe min ba."
Fisgota yayi tare da jefata kirjin shi yana me saka kanta a kafad'arshi, zaro idanu waje tayi. Kwalla na cika mata su, kokari take ta kwace daga jikin shi, ya matsa ta sosai.
Kukan da take ne
asa
asa, yayi masifar tasiri a kan shi, kasa saketa yayi yana niman yaga fuskarta, d'ago kanta yayi tare da zuba mata ido,
"Baki jin kome a kaina Noorh?" Yayi mata tambayar cikin damuwa.
"Ni bana jin kome?"
"Da gaske?"
"Kana tamtama ne?"
"Me yasa baki jin kome a kaina?"
"Kawai bana son damuwa ne, kuma Ni zuciyata tana inda ya dace"
"Ok!" Ya janye daga jikin ta, yana sauke ajiyar zuciya, ya wuce dakin shi baki daya.
Bai kula ta ba ma, itama bata damu ba, ta juya zata wuce taga shigowar Haroon, suka shiga kitchen, a tare suka yi abincin ranar, sam Mahir baya cikin nutsuwar shi, dakyar ya shirya tare da barin d'akin, yana fitowa falon yaji muryan Haroon da Noorh ana ta hira.
Abin ya kona mishi, wato shine D'an iska ba zata mu'amalance shi da mutunci ba, sai wasu mutane na daban, kwafa yayi tare da barin gidan baki daya. Tunda ya isa gidan Ummi ya sameta tana shirin fita, zuba mishi ido tayi kafin tace mishi.
"Da na tura Nazzir ya kira ka shine ka ki zuwa, sannan ka buge da cin mutuncin shi."
Shafa kanshi yayi tare da kallonta, sannan ya
dashi.
"Kiyi hakuri!"
Duk sai taji babu dad'i, ta kuma shi cikin kulawa tace mishi.
"Me yasa baka son ana zuba gidanka ko akwai abinda kake b'oyewa ne?"
A firgice ya kalle ta, can kuma ya wani boye razanar shi..
"Ni kuma? A'a kawai."
"Idan na kuma jin kana hana mutane shiga gidanka zan je naga abinda kake b'oyewa."
"Toh Ummi, babu kome ma a gidan."
Yadda yayi maganar sai da jikinta yayi sanyi, bata son fara zargin shi, domin kamar ta bashi kofar aikata abinda bai yi a baya ba.
Shiga gurin Hajiya yayi itama ta kare mishi zagi, sannan ta kuma gaya mishi cewa an tsayar da maganar shi da Zoolfah, cikin b'acin rai yace mata..
"Wallahi kika Kuskura kika makala min ita, sai na saketa ana daura auren."
Kura mishi ido tayi, kuma tunda ya fadi haka. Babu shakka zai aikata, dan haka ta sauko cikin lallashi tace mishi.
"Toh ranka shi dad'e, wacece zab'inka." Share ta yayi tare da lumshe idanun shi, yana hango Noorh, yadda suke ta dariya da Nishadi tare da Haroon, take shaidanin zuciar shi ta shiga kawo mishi hari ba mamaki suna can suna aikata masha'a. Bu
e jajjayen Idanun shi yayi tare da mik'ewa zubur ya bar gidan.
Da gudu ya figi motar shi,koda ya shigo gidan ya sami Haroon na wanke mishi wata motar shi, duk sai yaji babu dad'i amma kishin da yake cikin shi ya hana shi sukuni, shiga cikin gidan yayi ya same ta, tana saka turaren wuta.
Buge hannun ta yayi tare da zuba mata ido.
"Meye kika dauke ni ne?"
"Kaga Mahir bana son damuwa! Don Allah ka bar ni magana, an ce kama kowa damanme ne irin ka da zai saka kan shi a irin matsalarka. Don Allah ka kyale ni."
Tana fadar hakan ta tsuguna tana kwashe turaren wutan.
"Waye meye nayi miki ne da zafi haka?"
Mikewa tayi, zata wuce ya kai hannun shi k'ugunta, d'agowa tayi cikin mamaki, tare da kallon cikin idanun shi, a hankali turaren stick din suka zube daga hannun ta, kawai wani Kaddararren al'amari da ta tuna kwanakin baya, ya dawo mata cikin idanunta, kallon juna suke cike da mamaki, shi kan shi yana tune da wannan yanayin da ya zauna a cikin brain din shi, hannun shi ya kai zai tab'a fuskarta tayi maza ta rike hannun. Bakinta na rawa take kallon shi a hankali.
"Don Allah ka kyale ni, ka bar ni na samu lafiya."
"Ba zan iya ba, i'm in luv."
"Da wa?" Ta tambaya kirjinta na bugawa..
"Da wata me kama dake shekaru goma sha biyu da suka gabata."
Ture shi tayi zata juya da gudu,
ya riko hannunta, tare da fisgota kirjin shi, yana me rike ta da dukka hannu bibbiyu..
"Noorh! Kaman."
"Kaga Don Allah ka rabu dani mana, duk ka nace sai ka lalata min rayuwa, meye nayi maka da zafi da ba zaka bar ni ba? Meye na tsare maka da ba zaka barni na rayu cikin salama ba? Don Allah karka takura min ka kyale ni."
Yadda tayi maganar cikin kuka da fada sai da ya kashe mishi jiki baki daya, a hankali ya sake ta, tare da juyawa ya bar gidan.
Tunda ya fita take kuka, tare da takaicin ajiye ta da yayi a gidan babu wani kwakwaran dalili, haka ta zauna tayi kuka har ta gaji. Karshe a falon ta kwanta barci ya dauke ta..
Kwana biyu kafin Ramadan, rashin jituwar su tayi yawa, dan Noorh tana son barin gidan, bai kula ta ba, kuma bai kuma mata magana ba, asalima daina kula tayi baya tab'a dawowa, sai tayi barci karshe ma da yaga zuciyar shi tana yawan kawo mishi gulmar ta da Haroon, kawai ya san yadda ya raba zaman su, guri guda. Inda ya bawa Haroon aiki a Office din shi, kawai ya huta da zargin shi.
Suna zaune su uku, sun saka shi a tsakiyar su, duk sai ya basu tausayi, d'aya su Brst Usman Kamfut yace mishi.
"Amma Dr ya baka shawara nima ina bayan shi, idan ba haka ba, kuwa zaka jima kana ganinta babu yadda kayi da ita."
Mikewa yayi zai tashi yace musu.
"Ina da Opinions akan yarinyar amma bana jin zan iya amfani da karfina dan na nime Yardan ta, kawai zan cigaba da binta har ta amince."
"Allah ya wadaran naka ya lalace, jakin dawa ya ga na gida. Toh wallahi ka kyaleta tabar gidan ka, domin zaman ku a guri daya zaka iya durawa yar mutane ciki ka bar ta da tashin hankali."
Zama yayi sannan ya kalle su, kafin yace musu.
"Yarinyar da ta gama, raba kanta ga wasu bata yi cikin ba, sai ni ne zanyi cikin, kawai ku tayani addu'a, amma wancan tsohuwar zata b'allo min August."
"Wallahi idan ka yarda yanzun mu tafi muyi maganar da ita, dan kasan dole."
"Kai kyale ni, zanyi magana da ita amma bata wannan sigar ba."
"Kana nufin baka son ayi."
"Kai Dr bana son shirme, kawai ku manta da batun, amma zan shawo kanta."
"Yaushe kenan? Sai yaushe zaka shawo kanta, kasan iya adadin kusancin da kuke kara samun juna."
"Na sani mana, kawai bana son amfanin da karfin da nake dashi ne akanta."
"Toh me kake ganin ya dace kayi mata."
"Zan gaya muku?"
"Hmm! Baka da idea dan iska!"
"Toh alhudaduda."
"Bana son Iskanci, kai ba atab'a karewa da kai lafiya ba, dan banza wanda so ya cilla shi."
"Zan danna maka ashari'a."
"Sorry Bobo!" Da sauri ya d'ago kan shi, yana kallon Tamarah, wata mayyar yarinyar da take masifar son shi, amma baya sonta, duk fadin Lagos ita ke kiran shi Bobo.
Mikewa tayi tare da, tana taku kirjinta yana wani girgiza, cikin wani daukar hankali. Dauke kai yayi tare da mik'ewa zai bar gurin tasha gaban shi tare da kaiwa Big Bom d'inshi wani irin cafka ya buge hannun ta, tare da mur
e dayan.
" Ina da wacce tafiki haduwa sama da kasa, idan son ganin su naka nasan yadda zan yi da ita nake da kika gama bawa wasu mazan damar yin amfani da ke ba." Ya ture ta tare da barin club
in, wato idan kaga club
in ba zaka tab'a cewa a Lagos yake ba, kudin shiga club
in kawai abin jinjinawa ne, balle ko ruwa zasu sha a zaune yake da gindin shi.
Mahir yana shiga ne domin yasha soda, bayan nan baya kuma bin kome a gurin.kuma mafi akasari shida Aminan shi sun zab'i gurin ne domin tattaunawan sirri, shi yasa suke shiga gurin.
Lokacin da ya dawo gida, ya same ta a kitchen, dan yasan tunda ya hana Haroon shigowa gidan, shi yake zuwa musu da abinci, yana shiga ya samu ta gama jollop din rice wanda ya sha, kifi da kayan kamshi, har da kayan kamshi dangin cinnomi da mashroon powder, sai kanshi gidan ya
e, cikin gadara da iko ya isa gaban abincin ta sauke ya saka wata yar bowl ya debi abincin sannan ya kwashe kome na kai duk abinda zata ci dashi ya juye, domin sai yanzun ta fahimci ashe bata cin abincin da yake kawo masu, dan haka ya juye har da salat din ya fita abinshi, ko kallo bai ishata, sauran ta kwashe da kanzon tafto.
Tass ya cinye abincin, ya juya yana kallon yadda take cin nata,kamar ba zata ci ba, gyaran murya yayi tare da cewa.
"Yau zaki bar gidan nan!"
Da wani irin sauri ta d'ago kanta, cike da farin ciki.
"Amma kina da inda zaki zauna ne? Kinsan Lagos ba kamar Yola bane, akwai gang na yan iska, masu lalata yan mata."
Cikin rashin wayo tace mishi.
"Toh ai kai ne zaka mai dani Yola sai ka basu hakuri."
"Ni kuma? Toh duniya zargina suke na kashe ki, har yanzun case din ake, sannan kuma dole ki bar gidan nan domin Aysar Haladu da Manager suna niman ki, zasu kashe ki, shin kin shirya haduwa dasu?"
"Toh Don Allah kai ba zaka iya taimaka min bane?" Ta fa
i haka cikin rashin sanin abin yi.
"Tab! Bazan iya taimaka miki ba, domin gaskiya nima iyayena suna son na koma can cikin gidan na zauna dasu!"
"Don Allah,Mr Mahir ka taimaka min don Allah."
"Ke babu taimakon da zan miki,akwai kartin maza a wajen garin zasu iya ruined pride dinki su baki gurin kwana, amma Ni ba zan iya ba, maza ki gama ci,ki bar min gidana."
Kuka ne yazo mata tana rokon shi amma kememe, ya ki kulata karshe tace mishi.
"Don Allah ka rufa min asiri, na zauna na tsawon wata daya After Ramadan zan tafi ko ina ma"
"Ke baliga, Ni baligi anya baki hango abinda zai faru ba? Baki tunanin zan iya far miki."
"Ai nasan kai mutumin kirki ne, don Allah idan da hali ka
auke ni, aiki a kamfanin ka."
"Ta nan kika biyo?"
"Please wallahi zan na biyan kudin haya da albashin da zaka bani!"
"Wa zaki biya kudin hayan?"
Ya tambaye ta idnun shi a bu
"Kai mana, kai zan biya wallahi bani da kowa kasani ai, kai ne garkuwa na, please kayi hakuri na zauna a cikin gidan nan, domin nan ne matsirana."
"Tab' bazan yarda ba, kin manta yadda kika yi ta kafta min rashin mutunci ne? Ko kin manta tijarar da kika min ne!"
A rud'e ta mike tare da zuwa gaban shi ta zuba gwiwar ta a kasa tace mishi.
"Don Allah kayi hakuri kome ma kace nayi zanyi kawai ka barni na tara kudin jirgin da zai kai ni gurin Family na, kaji."
Tausayi ta bashi, amma bai sanya ya hakura ba, duk da yana da burin shi, amma haka yayi ta bata wahala, tana kuka kafin yace mata.
"Ina da sharadi da kuma abinda zaki min sai na kyale ki! Su Ummi zasu tafi Umrah dukkansu, dan haka."
Ya mike tsaye, tare da giya hannun shi a bayan shi, yace.
"Zaki zauna na tsawon wata guda amma ba zaki zauna a yadda muke ba, dole zaki amince...
Eyyeeeee toh wallahi Kuyi Vote da Comments, kuma kuyi share din shi ko kuma Alqur'an naja bargona nayi ta jan ragona
Lemme see wich can wuta bal-bal-bal zai tashi
#Team Mahir
#Team Noorh
[1/23, 11:09 AM] Addah Ramlat MANGA: https://my.w.tt/GmD0CxtiNcb
MAH~NOOR
My First Wife
Chapter 27 · 0% Book details