← Book details Mah Noor My First Wife Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 39

Chapter 1

Mah Noor My First Wife Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu
BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM
KU TAYA MU ADDU'A JIKAR KULU da A'ISHAH BAGUDU ba lafiya Ubangiji ya basu lafiya
#Dreams
Sosai yake kallonta, yana niman makusa a tare da ita, bai samu ba dan haka ya bar gidan yana biye dashi kamar bindin shi, bai ce mata kome ba, ya nufi Mansion din shi, tun ko ta kanta bai bi ba, bai kuma damu da ya mata magana ba, sai da suka isa ya kira Haroon ya gaya mishi ya sake Dolna.
Aikuwa suna shiga ya sake gidan, karen ya tawo da mugun gudu, bai damu ba yace mishi.
"Kamo min kafarta."
.wato da karen nan ya saka ta a gaba, tana ihu tana kuka tare da Rokon shi.
"Ba zaki gane ba, sai ya yanke miki kafa."
"Don Allah kayi hakuri."
Abinda take fada kenan, tare da niman ya taimaka mata, Haroon ne ya bude mata kofar,
Da kuka ta isa gidan. Jikinta yana rawa, zama yayi. Dariya yake yana tuno abinda yayi sai ya tsane mace babu kamun kai, shi yasa wani wata zai gudu Yola ko zai huta da Jarabar matan zamani.
Da ta isa gidan Ummin da gudu ta isa jikin Mahaifiyar ta, tana kuka tare da labarta musu abinda ya faru, dariya Alishbah tayi sannan tace mata.
"Ai wallahi tunda kika ga haka, gwara ki rabu dashi. Har baki ji ba ki godewa Allah da Haroon yake gidan, da baya nan haka zai shige yayi kwanciyar shi, kawai ki rabu da shi."
Ran Mahaifiyarta ya b'aci sosai, dan haka ta riko hannun ta suka bar gidan, bai shigo ba sai bayan la'asar, yana shigowa Ummi tace mishi.
"Allah ya shirya min kai. Ka hada ni da Kawata!" Ta fa
a a hankali.
Zama yayi yana kallon karatun da Dr Ibrahim Khalil yake
a sunnah tv, lumshe idanun shi yayi haka kawai yau yake jin bugun zuciyar shi tana fin na kullum.
Kwanciya yayi tare da dafe goshinsa, yana sauke ajiyar zuciya. Har barci ya dauke ta.
"Wayyo Ammih na!" Na fada da karfi bai ga fuskar ta ba, amma yana jin lokacin da matar tace mishi.
"Don Allah ka dauko min Yarinya ta, gata can Ai...."
Karar da jirgin yayi ya sanya wani abu ya buge mishi kanshi yayi da ya fad'i, kasa ita kuma matar karfe ya fasa mata kanta.
"Wayyo Allah na! Ammihhhhhhh"
A firgice ya farkaz tare da niman kwacewa zai fita da gudu,Ummi ta danne shi, tana tofa mishi Addu'a. Ita ta fara gajiya da wannan matsalar Mahir, dole zata mai dashi asibitin da ake kula da lafiyar
walwar shi, dan ya kwana biyu bai je an duba shi ba, kuma da alamun mafarkin nan yana nan tare dashi ko kuma yawan takura mishi da maganar aure ne ya sanya yake yawan jin haka oho, tunda ta samu ya sauke ajiyar zuciya, tare da daura kan shi akan cinyarta, yana lumshe idanun shi, alamar ya samu nutsiwa kenan.
Iskanci Tasleem bai ajiyeta a guri daya ba, Ni basa gaba na. Kawai abin da na sani, shine Allah ya bani sa'a na samu wata hanyar da zai kai yi wancan part din ba kome bane, dai wani riga ne da ake sakawa, dan haka nayi amfani da rigar na samu shiga bangaren, cikin ikon Allah na samu damar leko abinda suke ta hanyar nadewa a wani
aramin Camera.
Tunda na gama na fito, ban kuma komawa ba, na turawa Badar. Take shima ya tura ma'aikatar su.
Washi gari mun zo aka taramu wai Mr Nazzir zai yi magana.
Lokacin da ya fara jawabinsa. Ina sauraron shi, jin abinda ya fa
a muka kalli juna a razane.
"Da alamu akwai yan leken asiri, sun shigo cikin gidan nan.
Toh ba wani abu bane da zaran kuma kama su, toh zamu mika su ga jami'an tsaron, dan haka kowa ya shiga hankalin shi, kuma ku nutsu kuyi abinda ya kawo ku, matukar muka kama wani toh bamu bazamu yi kuka da kan mu ba, amma shi yayi kuka da abinda zai faru.
Karku damu ba barazana bane, tunatar wa ne."
Daga haka ya wuce abinshi idanun shi a kaina, takowa yayi tare da tsayawa a gabana, sannan ya kuma fita, yana shiga office din shi ya turo aka kirani,
bina da ido mutane suka yi..ban damu ba. Na isa Office din su.
"Mr Mahir Hamoud Boualem! Zai iso next. Zan baki aiki idan kina son na rabu da wancan halittar, zan hada miki wani abu, kuma naji labarin duk abinda yake
faru dake a gidan ku. Zan iya koran su a gidan ki.. amma nima sai kinyi min wani aiki guda daya.
Amma sai Mahir yazo kan yazo anan zan nuna miki abin da. Nake bukata"
"Ni bautar
asa nazo yi, baka isa ka sani abinda banyi niyya ba, And idan ka gadama karka rabu da halittar da kake fada munafukin banza kawai." Na gaya mishi haka cikin tsiwa da masifa, sannan na bar Office din, ina lura da dab ranin hankali yana ta janyo min abubuwan da zai Hadani da Tasleem, kamar yadda yake bukata haka yake samun ta mahaukaciya bata san cutarta yake ba.
Tun daga lokacin da aka gaya mana Mr Mahir zai zo, kullum cikin gyara mishi office din shi ake, tare da ware min inda zan zauns, sai kuma yadda suke gudanar da gyaran Office din, yadda ake kyalkyale office din shi ya fara bani haushi, mutum sai kace wanda yafi kowa. Ina jin wasu mala'ikata mata da suka san shi, sai cewa suke.
"Wallahi idan Mr Mahir ne gwara na ajiye aikin, ina dalili mutum yazo ya ishe kowa da masifa, wancan shekarar sai da na kusan ajiye aikin,
Domin a gaban wanda zan aura ya wulakanta ni, ya janyo saura kiris a fasa aurena, dakyar na samu muka dai-daita"
Ina jin wata tana tambayarta, me ya faru.
"Wai kawai dan naje kusa dashi na dauki hoto, tare da cewa ya bani Number wayar shi."
Juyawa nayi tare da watsa mata ruwan hannun na, ina dariya.
"Ko kunya baki ji ba, kina gayawa mutane kece kika nemi ya baki Number shi, toh a sunanki me? Ke sakatariya ce a ma'aikatan nan, amma kece kika fada soyayyar wani kato.
Nifa babu wanda ya isa nace ya burge ni, domin kishin tsiya ne dani,shi yasa bana son soyayya da namiji me kule kulen yan mata, ni mijin da zan aura. Ba zan tab'a cewa ina son shi ba,sabida kar yayi amfani da wannan tunanin ya cutar dani.
Ina mamakin Yadda ku mata baku da wani jan aji, kawai namiji na zuwa, sai a fada mishi kamar wani ya
i, toh taya ba zasu yaudare ku ba, ko zuwa yayi da gaske yana sonki, dole ki kame kanki balle kuma yazo da fuskar shirme, baku san wani abu daya ba, ranar da na fara zuwa dariya kuka min saboda hijab.
Har ana gaya muku cewa, munafukai ne ke saka hijab, toh baku san wani abu ba, hijab kariya ce ga ya mace, dan haka ne ba munafuka bace, kuma hijab dina kariya ce a gare ni, dan haka ku Cigaba da watsi da kimar ku, ana cin mutuncin ku a banza."
Mikewa nayi na bar gurin, yau har muka dawo, gidan ina ganin yadda Tasleem take ta rawan kai, Ashe mutumin zai zo cin abinci ne, ni kuma munyi Badar zai zo mu tattauna akan abinda na samu.
Muna cikin hira, a motar shi ina nuna mishi abinda yake faruwa, tare da cewa.
"Ina zargin bai san meke faruwa ba, domin kuwa har yanzun yana makale min. Kuma da yasan nice nake bibiyar abinda yake maybe da ya saka an kore ni!"
"Nima shi yasa na sake rai na, amma ya kamata ki nutsu dan Mr Mahir yana zuwa, abinda zaki yi yana dayawa, amma dole ki shiga jikin shi shima."
"Ni fa bazan iya mu'amala da wani namijin ba, kai ma sabida na yarda da kai ne, nake taimakonka. Amma bana jin zan iya wannan aikin, kowa so yake yayi amfani da ni, me yasa sai ni?"
Shiru yayi yana kallon bayan motar shi sakamakon hancin motar Mr Nazzir.
"Dama wannan gayen zai zo gidan nan ne yau?"
"Eh nima dawowa na daga aiki naga Mother In-law din shi tana ta shirya table bari naje na musu Iskanci." Ta fa
a a hankali.
Kafin ya mata magana har ta fita. Lokacin da Nazzir ya fito cikin motar itama ta iso inda yake, bata kalle shi ba, ta wuce abinta, tana zuwa cikin gidan,ba tare da tacewa kowa kome ba, ta nufi table din, ta dauki wani katon filet ta dibe abin da ranta keso, tana lashe yatsunta, sannan ta wuce ta daidai saukowar Tasleem.
Ganin yadda tsabar mugunta, ta bata ko ina, sannan tayi ficewarta, ta nufi motar Badar, shi kan Nazzir dariya ta bashi.
Tana tafiya tana murmushin mugunta, tana isa motar ta bude tare da mikawa Badar, tace.
"Kayan abincin da suka shirya wancan banza na dauko maka, maza ci rabonka ne."
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Ai ba zan iya cinye ba,"
"Toh ni kan nayi nan, zanje niman rigima."
Tunda na barshi ya girgiza kai, na shiga cikin gidan, na shiga zabga musu iskanci, na hana kowa sakat. Dan kaina na bar falon bawai dan sun roke ni ba. Ganin yadda Tasleem take zubda kwalla. Sai jikina yayi sanyi na kyale su.
Dan na fahimci amadadin. Yaji haushina sai ma jin dadin da ya
---
A hankali naga jikin Tasleem ya soma sanyi. Karshe dai ta sauko. Nima kuma muka dai daita, har iyayen ta suna jin dadin haka, ban tab'a jin na mata wani abu ba. Shirin da muke ya kuma samun kyakkyawan sakamako, dan har a kamfanin kowa yasan mun shirya. Dan haka Sir Nazzir ya dai na kokarin shiga tsakanin mu.
Yana zaune a gefe, Haroon yana ta ha
a Mishi kayan shi, idanun shi na kan wayar shi. Tare da nunawa Haroon kayan da zai zuba mishi, kama daga suit zuwa jamfa har zuwa kaftanis din shi yana gamawa ya kira Number Ummi ya gaya mata, yau zai bar garin zai nufi Yola.
Fada tayi mishi tare da gaya mishi amma ai zasu tafi asibiti shine zai gudu.
"Ummi mafarki ne ba ciwo bane, Insha Allah zan dawo muje ba zan wuce sati Uku ba,"
Ya fa
a tare da dafe goshin sa, bayan fitar Haroon da kayan ya tashi sanye da farin jeans sai rigar black, ya daura wani top a saman shi, idanun shi manne da sunglass, ya fito a hankali yana murmushi, mota ya shiga yana kallon kayan aikin shi, kama daga wayar shi, Tap din shi zuwa laptop din shi, lumshe idanunshi yayi,
yana kuma tuno mafarkin shi na jiya.
Fuskarta sanye da rufe, ta mika mishi hannu. Zai riko kenan, wani abu ya tawo da karfi kamar jirgin kasa ya shiga tsakanin su, sai muryan ta da yake ji tana dariya. Anan ya bude idanun shi...
Zaku na samun Posting a ranaku biyu ne, Monday da Alhamis. Bayan nan zaku min Uzuri, gaskiya. Idan kuma bayi yi ba toh sai sabon shekara Insha Allah, sai na cigaba da baku kullum...
https://my.w.tt/oCPVBn764bb
MAH~NOOR
My First Wife
Chapter 10 · 0% Book details