← Book details Mah Noor My First Wife Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 15 OF 39

Chapter 1

Mah Noor My First Wife Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

MrsUsman400
Free book
For You Jikar kulu
BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
Zee Sardaunan
Sumayya Ahmad Aliyu, fateema Mustapha
Ga gaisuwar ku nan
masu jiran Mah-Noor.....
Gaye You enter Noorh hand, zaka fadi gaskiyar ka, indai Noorh ce jininka sai ya kare, Yan leken asiri, naga sakonku! Wattpad fans kuma haka, My Hajiya Maryam Jikar kulu
Mommy Sultan kece kike bayan Noorh kowa ya fara jin haushinta_
#My Nikkab
Yana cikin gym room, yana d'aga karfe. Sako suka fara shigo mishi. Cikin gajiya da karar wayar shi, ya d'auka yana kallon Ummina, kiranta na katsewa hadiya tana kiran shi, dauka yayi tare da cewa.
"Beb!"
"Ka duba tweeter please!"
Cikin sanyin jiki ya bude idanun shi, sanan ya bi wayar da ta kashe da idanu, kafin ya tashi zaune yana jin faduwar gaba, a hankali ya bude data. Sannan ya shiga tweeter. Sako ne suka shiga sauko mishi, cikin faduwar gaba yaga sakon Noorh. Ji yayi zuciyar shi kamar zata diro kasa, ya kurawa yar ido.
Lokacin guda yaga Aysar Haladu, wani matashin me kudi anan Yola, yana mara mata baya cikin tsannanin b'acin rai ya shiga hango wasu daga cikin mutanen da suke gaisawa sama sama, kira wayar shi akayi cikin mugun zuciya ya dauka.
"Lion! Gobara ta tashi a cikin kamfanin amma anyi nasarar kashewa."
Sake wayar yayi tare da dafe kirjin shi da yake barazanar fashewa. Jingina yayi karfen da ya d'aga, ta sauke a kansa ba dan ya tare ba, da wallahi tayi mishi lahani. Ji yayi zuciyarshi tana ci da wuta. Dan haka ya mike tare da tangadi ya bude yar medium din frig din da yake gurin ya bude tare da daukar goran ruwan sanyi ya bude bakin shi sai da ya shanye tass. Yayi wurgi da goran yana sauke wani irin gurnani.
Da zai sami wani a kusa dashi tabbas sai yayi mishi mugun duka, tashi yayi zuwa dakin shi ya budewa kan shi ruwa, haka ya jike jagwab. Sannan ya nufi inda towel
in shi yake ya dauka tare da daurawa yana goge kanshi da da daya.
Wani irin huci yake, tabbas da zai ga marubucin wancan abun sai na lahira yafi shi jin dadi, wani irin bakin ciki yake ji kamar zai kone, haka yayi ta ambaton Allah.
Har ya gama shiryawa sannan ya fito, yana fitowa yaga Nazzir ya wani firgice, bai ce kome ba, ya shiga mota aka tafi da su kamfanin, kafin su iso an kwashe kome. Sai an kananun kayan da aka barshi suna cikin wuta, lumshe idanun shi yayi domin ji yayi kamar zai sake kuka, Kamfanin nan amanar shi ce.
Mahaifin shi ya bar mishi, duk da yana da wasu masana'antu amma wannan ji ya
e kamar mahaifinsa ne a raye.
"Kuyi hacking din Acct
in Tweeter din marubucin, duk wanda yayi rubutun nan makusancin kamfanina ne, ku tafi ki nimo min wanda yayi wannan ta'addanci..."
"Lion! Jornalist!"
Juyawa yayi da fuskar shi da tayi jajjur.
"I don't care! Koma waye yazo babu abinda ya dame ni, kuje ku nimo min wanda ya lalata min suna. Idan ba haka ba, toh wallahi zaku ji a jikin ku."
Yaki magana da yan jaridu, asalima abin sai ya koma siyasa, domin wasu na cewa sharri aka mishi wasu na kuma cewa zai aikata idan aka yi dubi da yadda yake da Arziki gashi matashi wanda yake ganiyyar samartaka shi. Dole yayi abinda ya gadama.
Yana zaune a kamfanin anan yayi Sallah magarib da isha, suna zaune ana cigaba da aikin, aka turo Super visions from ministry of health, da Kuma wasu daga Shari'a committee, tare da Da'awa. Mahir ya kasa magana, a hankali aka shiga bincike sosai, binciken da ya kai har sai da aka zakulo wasu abubuwan na daban, ba abinda ake zargin ba.
Dake duk abinda yake faruwa ana dauka a live, karfe goma na dare Ummi da wasu manyan lauyoyyin daga lagos suka iso. Anan aka shiga tashin hankali tare da musayan kalamai.
Har zuwa karfe
aya na dare, suna cikin wannan yanayin Noorh ta kuma sake videon da ta dauka, tare da asalin yadda giyar take, da yadda ake tacce rubabben kayan marmari ana sarrafa su a gida, tare da tambarin Hamoud Boualem Drinks. Kamar zai fadi. Ummi ta riko shi.
"Kar wannan ya dame ka, ka nutsu a ranka babu wanda ya isa wuce kaddarar shi jarabtace."
Muryan shi a raunane yace.
"nagode sosai Ummina"
duk yadda aka so yayi magana ya kasa cewa kome, dan haka Manyan Jami'an gwamnati, suka saka hannu a rufe Kamfanin, komawa gefe Nazzir yayi sun jima ana magana can aka kira wani daga cikin masu binciken.
hakuri yayi ta badawa sannan ya kalli Ummi da lauyoyyin yace musu.
"karku damu ministan harkokin lafiya yayi maganar,"
Haka suka dauki kayan su, suka fita amma ta fannin addinin Musulunci, sun ce a karkare a kotu. Lumshe idanun shi yayi sannan ya mike, suka nufi gida.
Tunda suka shiga gidan shi Ummi ta zauna a kujera, daura kanshi yayi a kafad'ar ta, yana me lumshe idanun shi, sai ajiyae zuciya yake, zunzurutun b'acin rai.
Wayar shi tayi kara Ummi ta duba, taga Nazzir. Kashe wayar tayi tare da wurgawa a cikin jakarta. Yana kwance a jikin ta, har yayi barci, zamar da kanshi tayi tare da sakawa akan pillow.
Tausayi ya bata, tare da jin ta ina zata taimaka mishi, toh babu Mahir yaki aure, tana fara maganar aure zai tashi kamar me aljanun.
Dakin shi ta nufa tayi alola tare da gabatar da sallah nafilla. Tana idarwa tayi kwanciyar ta, a d'akin.
Wato Noorh da ta samu ana giya mata baya, kawai ta shiga bankad'e Abubawan da babu ruwanta, kiranta Badar yayi yace mata.
"Ki dakatar da abinda kike! Domin mutumin da kike yaka bai san kome ba, kiyi maza ki goge abinda kike daurawa, kafin zuwa lokacin da zaki yi danasanin abinda kike aikatawa "
"Kaga Don Allah ka barni nayi aikina, idan na gama shi kenan.". Dakyar ya dakatar da ita, sannan ya sakata ta goge kome, sannan suka yi sallama.
Washi gari.
Da wuri ta shirya zuwa kamfanin, tun a bakin kofar shiga ta fahimci yau abu mutunci ,.kowa zai ci Ubanshi. Tana shigowa Yana shigowa ko kallon shi bata yi.
Duk yadda Ummi taso lakwasa Mahir abin yaci tura, domin kuwa sai da tai mishi nasiha, da kuma kar taji ya kori kowa, sanan tabar Yola bayan taje gurin Yan uwan ta, suka jajjanta.
Bata ce kome ba, har suka isa airport. Nasiha take mishi gyada kai kawai ya
e. Bayan tafiyar ta, suka juyo zuwa kamfanin, tun daga bakin kofar ya fara ruwan bala'i, har ya shiga office din shi, bai yi kora ba, amma an dakatar da mutane da yawa, dama a yau Tasleem ta shirya tsaf domin tun karar Mr Mahir da marurun zuciyata, bata san abinda yake faruwa ba.
Sai dai yadda taga Noorh tana kaf kaf da kanta, tare da saka nikkab
inta ta cikin fiskarta sannan ta daura hijab a saman shi.
Sannan ta dauki hand bag dinta, suka fito Tasleem ta shige dakin Mommy, ta sami guri ta zauna, tana daukar turaren mallaka da kuma idona idonka.
Tana gamawa ta fito, a hankali tana yatsina fuska, a gurguje suka karya, tare da mik'ewa suka fita.
kowa ya gama shan jinin jikin shi, domin an dakatar da mutane arba'in, yana tsaye ya kasa magana idanun shi jajjur, suka shigo kamfanin, bai juya ba dan yasan sune zasu iso.
"Ba zaku fitar min da wanda yayi min zagon kasa ba?"
Kunshe dariya Noorh tayi, take tare da kallon shi, ganin yadda ga baki daya ya rud'e, tana hango tsoro injita, da tashin hankali. A fuskar shi a tunanin ta kenan. Amma a yanayin shi babu tsoro, tsabar bala'in da yake cin zuciyar shi ce, ya tsare su da masifa. Yadda yake musu tsawa.
Cikin niman tsokana tace.
"Mufa ba yara bane, da wani zai tasamu a gaba da ihu, ai idan mutum bai aikata abin da ake zargin shi ba, ba zai damu kan shi ba, sai ma kare kan shi da zai yi salon mugun nufinsa ne ya janyo mishi rikicin duniya."
Cikin fusata ya juya tare da janyo hijab
inta yayi hanyar waje da ita, rashin sani yafi dare duhu. Watsar da ita yayi akan idanun Yan jarida. Da suka zo wurin domin niman abinda zai ce da kalubalantar shi da ake.
"Kar na kuma ganinki a cikin kamfanin nan." Ya fa
"Wannan kuma matsalar kace sai dai ka sani ka kuma dagula kome, ashe cin zarafin mata da kake gaskiya ne."
Cikin makirci ta mike tana kuka, tare da tunkarar shi, ana kuma dauka a hoto, haka ya kuma tureta, kamar da gaske.
Security ne suka zo suka fita da ita, ai kuwa yan jaridu, suka shiga tambayar ta, ta shiga basu amsa.
"Wallahi ban san me nayi mishi ba, kawai ya shiga wulakantani, sannan yau ma ya nime ni ne, naki shine yake tozartani a cikin jama'arsa tare da koro ni."
Wannan muryan nata da tayi sanadiyar janyo mishi mugun asarar me girma a wannan kamfanin, a cikin kasa da awa biyu, masu hannun jari sama da mutane 70, suka zo janye hannun jarinsu. Juya musu baya yayi tare da kallon waje, kunna mishi tv aka yi, yana jin muryan ta ya juya da sauri, yana kallonta, tare da bawa babbar yar jaridan nan amsa cikin nutsuwa wato Mimiqueens. Tace mata.
"Toh Malama A'isha Omar Jimeta, shin akwai abinda ya tab'a had'a ku da shi?"
"Eh toh gaskiya zan iya cewa,ya sha bani azaba a cikin office din shi sannan kuma Dan uwan shi Sir Nazzir ya sani, domin ya mishi magana yaki!"
"Toh wai da gaske ya tab'a niman yayi miki fyade." Kasa tayi da kanta, tasan karya haramun ne, amma ta nan take ji zata cutar da Mahir yaji yadda take ji.
"Ya tab'a, domin Office din shi da akwai dakin da yake aikata hakan da yan mata irina."
"Shin ya samu nasara akanki."
"A'ah!"
"Toh anan muke kira da Malaman musulinci da kuma hukumar kare hakkin dan Adam da kuma na kare mata da kananun yara, su shiga domin karewa A'isha Omar Jimeta, dalibar jarida, sannan ina tayaki murna sakamakon daukar ki da gidan tv Gaskiya tafi kobo, ta dauke ki. Zamu kuma kare mutuncin ki."
Cikin rawan jiki ya cincibo tv daga wall ya buga da kasa, cikin bala'in b'acin rai.
"Meye mata? Meye nayiwa mutane suke son ganin bayana?" Duk wani abu sai da ya farfasa, ya shiga tashin hankali, tare da
jin wani irin bakin ciki, duk yadda kake da taurin zuciya, idan kaga Mahir Hamoud Boualem CEO ya zama wani irin mutum lokaci guda depression yana niman kai shi kasa.
Dole aka nimo Dr din shi,da taimakon alluran da aka mishi ya sami barci.
"Noorh! Ki boye wannan hujjojin, suna bina zasu kashe ni,na tura abinda kika bani kafin ki fitar da naki, sannan yanzun zan shiga gidana,yadda muke zaton abun ba haka bane, na kiraki da privet Number ne domin kar su kamaki, ni kuma na kawo su gidana ne domin kafa hujja, Noorh Sir Mahir..."
Karar harbi taji ta sake wayar da sauri jikinta na rawa, cikin tashin hankali, take kallon wayar, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, tana kallon wayar jin yana magana ta kuma saka wayar a kunnen ta.
"Noorh! Kanina yana Asibiti yana shan magani, mata na kuma tana Ghana na turata da yarinyata, ga kuma karamin ciki, don Allah ki taimaka min akwai sako, zata bawa gidan jaridar ku domin Sir Mahir Hamoud Boualem.."
Sake bude mishi wuta aka yi, tare da bankawa gidan wuta. Kashe wayar tayi, cikin minti talatin tana zaune a Office din su aka kunna tv.
"A yau ne muka samu labarin wanda ya fasa irin badakalar da ake a masana'antar Hamoud Boualem Company, ya mutu. Sakamakon gobara mutuwar dai ta girgiza zukatar jama'a, Mr Badar Dan jarida ne da yake aikin sirri da kamfanin tacce labarai na
asar nan NAN, kafin mutuwar shi yayi aiki da CNN, sannan yayi aiki da DW, kafin ta dawo yake aiki da kamfanin tacce labarai na NAN,
matashin dan shekaru talatin da tara, ya rasa rayuwar shi ta dalilin da ba a sani ba."
Kayan aikinta ta dauka, a yau ta shirya fuskarta MAHIR Hamoud Boualem, tare da cire Hijab
inta da kuma Nikkab....
Na wetin go hapun?
https://my.w.tt/ylGexVK5jcb
MAH~NOOR
My First Wife
Chapter 15 · 0% Book details