← Book details Karshen Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 20

Sashe 9

Karshen Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_____________ A tsaye take tana safa da MARWA a dakinta kayan da sageer ya siya musu ne a gaban ta meyasa? Meyasa ita ba ta da sa"a? Umayma Basu Kai su arziqi ba Amma tafita sa'a a rayuwa meyasa komi ita ke fara Fara samu?
Kallon farko da tayiwa sageer taji tana son shi Amma azuwan shi gunsu yace umayma yake so me hakan ke nufi?
Cike da tafasar zuciya tafara maganganu "Idan na haqura da wani abun to wlh wannan Karan bazan hakura da sageer ba kiyi hakuri umayma sageer da ni yadace "
Zama tai tana saqe saqe a zuciyar ta zuwa can Kuma naga
Ta tashi toilet ta shiga,

*************************Cikin farin ciki tashiga gidan su mahaifiyar ta na daki sai kishiyar mamanta dake falo Bata amsa sallamar ba ko kallon inda umayma take Bata yi ba ta juya kanta taci gaba da abinda take
"Aunty sannu" batajira cewar ta ba Dan tasan dama ba"amsawa zatayi ba ta nufi dakin umman ta tsaye ta iske ta gaban sif tana jera kaya
Sallama tayi ta amsa sannu ta mata sannan ta karbi aikin taci gaba da yi
Fira suke sai da suka Gama jera kayan sannan ta jawo ledan ta tura gaban umman kallon ta tayi alamar neman qarin bayani tun haduwar su da sageer har kawo sun gida da yayi sai da ta fad"a mata
Ajiyar zuciya ta sauke sanna tace
"Lokaci yayi umayma idan kina ganin ya kwanta Miki banason doguwar soyayyar Nan ki tura shi gun abban ku yafara neman izini tukun bazan so ki gaggawa ba Amma ki nutsu ki fahimci manufar shi"
Sannan daga yanzun kada ki Kuma karbar abin hannun shi kada ki Kuma shiga motar shi kinji ni?"
Cikin sauri tace "naji umma Kuma inshallah zanyi yanda kikace"
"To Allah ya Miki albarka
Tashi kije
Zan nuna wa abban ku kayan idan ya dawo"
"To umma baran yi wanka"
"Ok ki sauko mushiga kitchen"

Ba gida ya nufa ba Dan dama ba al'adarshi bace kwana a gida Kai tsaye gidansu wata budurwar shi Azeza ya nufa " ko da tafito sun Dade suna soyayyar su ta Shan minti acikin motar kafin yaja motar suka qara gaba sai da sukaje gidan su ta qofar shi dake baya suka shiga " karshe ma Azeeza a gidan ta kwana "Sai da safe ya sallameta ta qara gaba shikuma ya koma bacci Dan Bai samu bacci ba adaren jia"l

Baban umayma Koda ya dawo umman ta ta nuna mishi kayan yace Akira mishi umaymar bayan tazo kamar yanda tayiwa mahaifiyar ta bayani haka ta mishi shima ya yarda da ya Kuma gasgata abinda tace albarka yasa mata sannan yace idan ya Kuma zuwa ta turo mishi shi cikin girmama wa tace "to" fita tayi bayan ya sallameta"
Basu taba kayan ba Abba yace abarsu har sai yaron yazo yaga yanayin tarbiyar shi tukun inyaji zai iya bashi yarshi

Wayar ta akashe take shiyasa Bata da tabbacin yakira ta ko Bai Kira ba
Baccin ta Tasha har zuwa sanda akai kiran sallar asuba

*****************

A bangaren fateemah kuwa Bata samu rintsawa ba a Daren ta rasa samun mafita' a yanda take ji daga haduwar su da sageer zuwa yanzun idan har Bata mallake shi ba to wlh mutuwa zatai Dan wani nauyi taji zuciyar ta ta mata Dan ko sallar asuba Bata samu Yi ba Kuma akan kunnen ta akai kiran
Karfe 8 ta sauko suka karya ita da familyn ta Babu walwala tare da ita hasalima wani fitinannen ciwon Kai ke damun ta
Kowa ya tambayeta sai tace kanta ke ciwo Bata samu bacci ba jia sabida karatu ta kwana yi
. Sannu kowa ya mata sannan maman ta tace ta koma ta kwanta kafin lokacin da zasu shiga lecture yayi" Bata Musa ba ta tashi ta koma dakin shigar ta kenan taji ringing din wayar ta
Tsaki taja bayan taga sunan umayma" a screen din Bata daga ba Dan zuwa yanzun tsanar Umayma ce fall ranta ta umaymar " mafita kawaii take nema domin tana da tabbacin
Zuwan qarshen qawancen su yayi

*********************
*Alh* bilya bello shine cikakken sunan shi matar shi d"aya *haj* yahanazu auren soyayya sukayi haifafun cikin garin katsina ne su duka Kuma anan suke zaune yaransu uku
Abdul"ahad *Tahseenah* sai auta Azeema"
Alh bilya bello Mahaifanshi duka suna da Rai " mutum ne shi a fuska kyakkyawa Amma azuci bashi da kyawu ko kad"an cikakken d"an qungiyar asiri ne

Haj yahanazu ita mahaifin ta yarasu a gun mahaifiyar ta tashi cikin tsanani da wahala Dan talakawa ne na gasken gaske futuk shahararrun fakirai ne na bugawa a babban bangon jaridar duniya.........

Comment
Share
08038541511
[1/16, 11:09 AM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA*
_kalubalenku Iyaye_

*na*
*Zahrabukar*

*Exquisite WRITTERS FORUM*

*_16_*

_________Waye Alh wada?
shine Wanda yake lalata rayuwar yara maza nutsattse ne a da mai sanaar siyar da fruit tarihin nutsuwar shi yafara ne watarana
""""""""Wata Daria aka kwashe dashi d"aya ya matso gun shi yace "Wada wada wada Berry ya kagani ? Tabbas yau ranar sa'ar muce ba banza ba qungiya ta bamu shawarar zuwa park din Nan Ashe sun San zasu turo Mana Kai?"
Dayan yasake kyalkyale wa da Wata kafurar Dariya yace
"Nayi mamakin dama da akace muzo Park mu aikata wanan abin zamuga Mai zai faru to gashi ta Tabbata"

Kallonsu yake a razane suwaye? Mekuma suke nufi me suke nema wajensa? Tunaninshi ne ya katse sanda yaji an dafa shi
Daya ne acikin su yace mishi "ka Gane ni?" Girgiza Kai yayi yace "nine Wanda muka had"u dakai shekaru uku da suka wuce Kana siyar da fruit na siya na barmaka canjina in baka manta ba a lokacin ai na maka wata magana ko?"

_abinda ya faru 3years ago_

Tafe yake yana tura Baron kayan fruit din duk ya gaji ya had`a uwar zufa ga yunwa ga ba ciniki
Yana cikin tafiya wata mota tai parking mutum daya ne aciki ya tsaidashi ya siyi fruit din bayan yabashi kudin kallon yatsun hannun shi yayi take meeting din qungiyar su ya fad"o mishi na jia kowa an bashi zabin abinda ake buqata so shi nashi ana buqatar yakawo mutum Mai yatsu shida a hannu yashigo dashi qungiya so ganin hannun Wada berry
har ya tafi sai Kuma yadawo
Zuge glass din motar yayi yace mishi yana da magana dashi

Kallon shi yayi yakuma kallon motar kafin yace "to inaji zaka fito ne?"
"Why not?" na cikin motar yabashi amsa Yana kokarin fitowa daga motar
"Baran fito"
Wuri suka samu suka d'an keb'e sannan mutumin yace meye "sunan ka?"
Kallon shi yayi irin meye had"Inka da sunana" ?
Kuma tambayr shi yayi sannan yace "sunana wada Amma anfi kirana da wada Berry"
"Ok tom wanan itace sanaar ka? Gyada
Kai yayi yace "kwarai domin akan ta ka ganni ai"
murmushi mutumin yayi yace 'hkne but kamar da wahala acikin ta me zai Hana ka canja wata?"
Kallon shi yakuma yi yace "ko?" Gyada mishi Kai yayi yace "kwarai ga sana'o' Nan birjik sai wacce ka zaba?"
A takaice yabashi amsa
"Nafi buqatar wannan din ai"

Dariya yayi yace "acewarka ba? Amma kowa ya ganka yasan kana cikin wahala well why not in taimake ka?"
Kallon shi yayi sannan yace
"If u need fa Amma ba tilas"
_Amsa yabashi da cewa "wannan ba sana"a bace knn_
_Wai tsaya malam_
_mece matsalarka da nine nine kadai Mai buqatar_
_taimakon ka? Ina akwai mabuqata a gari so kaje ka Basu ni Ina da madogara ya tura Baron shi yayi gaba"_
binshi yayi yace
_"ok tunda bakka buqata ga wanan kaje ka qara jari"_
_Bai jira cewar shi ba ya aje mishi bunch na 1k guda d"aya ya koma inda ya ajje motar shi yashiga _ da sauri yabishi ya Mai da mishi sai dai kafin ya iskeshi har ya tada motan yayi ribos yace ko badade zan waiwaye ka bawai na tafi kenan ba ka jirani_

Ya Dade agun Yana juya kudin Yana juya maganar mutumin cikin farinciki yau gashi da dubu dari tashi ta kanshi dama duk basarwa ce yake yaso mutumin yayi ta lallabashi sannan sai ya fad"a mishi eh Yana buqatar taimakon" Bai wani matsa ma kanshi ba yayi sadaka da yamutsattsun kayan fruit din ya samu abinci ya siya
A ranar Bai koma inda yake kwana ba sai da ya qarar da kudin Tass
Ya qara jari yasiyo suturu da takalma" da sauran abubuwa dai
Kullum Kuma sai ya tuna da mutumin yaci gaba da Sana arshi har zuwa yanzun "
_*wannan shine abinda yafaru a ranar*_

ce mishi yayi "ka tuna? Ka ganeni yanzun ko?
Gyada mishi Kai yayi yace "eh natuna ka Amma a ranar da na ganka a mutumin qwarai na ganka Amma ynxun naga kishiyar haka
Bansan meye dalilin ka na bibiyar rayuwa'ta ba ko zan iya sani? Amma kafin Nan muje waje"
Wqni kallo mutumin ya watsa mishi sannan yace "amma kana hauka ko?
In ba hauka ba yaushe zan ga samu Inga rashi? Kaga kofar Nan a rufe ko to wllhi tallahi muddin baka bani hadin Kai ba ko? To sai wani ba Kai ba zaifi ma kyau ka nutsu Muyi Mai fishehemu
Ka qaru nima inqaru"

ta Dade Tana tafka da warwara dagaske sageer ya mata sannan da ita yadace bada Wata banzar bazara umaima ba Tabbas wannan Karon sai dai ai uwar watsi wallahi bazaiyi ba bazata sabu ba
dole ne tayi ma kanta wannan yakin sunkurun ita kadai dole zata nemi maryam Ashe kawance da yan duniya ma Yana da rana? Yau ce ranar kawance da maryam dole zata rakata wajen bokanta wallahi ko ran mutum ne Zata bayar Dan ta mallaki sageer,
cikin hanzari da yarda da shawaran zuciya takira maryam suka Gama kulle kullensu a washe gari suka nufi gun bokan '
Chapter 9 · 0% Book details