← Book details Karshen Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 20

Sashe 15

Karshen Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hmm "nadai jika
Inda ace ita wannan ta haihu ta ajje mun d'an jika ko Yar jika ai da ko Kai ba kaje ba nasan jikana ya je in ganshi
To wallahi da sakel asan abin yi ganan wad'anda akai auren ku tare yanzun wasu ma yara biyu garesu wasu nada cikin na uku

Amma ku tsit to wallahi kodai a Haifa mun jika ko Kuma ka karo aure ka auro wacce zata haifa min Yan jikoki tunda ita wannan ta gaza Sai dai taci ta kasayar sai uwar kiba take mulka wa abinta to asake shiri wallahi Dan mu kaf dangin mu Babu juya"

Zai fara magana ta katse shi ta Mike tace "bana son wata magana kaji me nace"salan Kuma kaje ka kai karata wurin ubanka ranka ya baci wallahi ni kaga tafia ta"

Ta shuri takalmn ta tayi waje da sauri ya bita Yana Bata hakuri ko juyowa batayi ba,

Ta fice

Da sauri yadawo cikin gidan ya iske humayda tana Nan yanda take a durqushen har Yanzun Kuma kuka take

Lallashin ta yahau Yi sannan ya samu ya Sanja Kaya ya fita masallaci inda dagacan zai wuce gidansu

*******×*****************

Maganar auren fateema da sageer har tayi nisa Dan har ansa biki wata biyu kwanaki nata tahowa ana ta shirye shirye Amma umayma Bata da labarin kawarta zatai aure Bata Kuma da sanin cewa saurayin da ya Fara sanin ta y'a mace zaiyi aure zai auri qawar ta Kuma aminiyar ta harkokin ta kawai take
Dan yanzun cikin jikin ta ma taje anzubar dashi bisa ga shawarar wata sabuwar qawarta da tayi wai ita *Zeenah*
A Dan tarensu ta Ida dulmiyar da umayma Dan ita ta Bata daki a gidan ta yanzun ma har fita ake da ita qasashen waje Dan wannan qawar ta Kuma hada ta da manyan alhazai shagalin su kawaii suke Sha
*toh jama'a GA zeenah ta antayo cikin rayuwar umaima ita Kuma komeye tata kaddarar?*

A gidan su umayma kuwa baban ta paralyzed ya Kama shi maman ta Kuma tana kwance a asibity hawan jini da ciwon zuciya Dan su na da labarin komai dangane da yanda rayuwar umayma ta koma

Sai daga baya sukai nadamar korar ta Amma har Yanzun zuciyar su basajin zasu iya cigaba da zama da ita
.
Zasu dai cigaba da mata addu'ah Allah ya shirya ta ya daidaita Al amarin ta

Biki yana ta gaba towa Dan yanzun haka sauran baifi 2weeks ba shirye shirye sun Kan kama har an kawo lefe
Kaya kam sunyi ba laifi Dan sageer yasaki bakin aljihu Ana ta barin Kudi

Ga pre wedding pics" ana tasa ki a duk wata kafar sada zumunta amarya da ango sun sha kyau har sun gaji

*********************
Kwance. Take tai daidaya akan gado chatting take hankali kwance

A d"an lokaci Kuma tana duba Instagram ta
Wasu had'addin pic tagani ana ta like ana comment akai har ta wuce dan ita bata ma lura da ko su wane ne ba jikin pic's din" har ta wuce taga wani comment da ya shigo Yanzun wani nacewa..........
_yanzun wasan zai canja salo fa kawaye yanzun Zaa fara dabar salon namu zai juya alaka zuwa daukar fansa_

__________________
anan ta kwana cikin ruwan a some daga ita Har abinda Ke bayanta sanyin asuba ne yadake ta yasa a hankali ta Dan daga idanunta da suka Yi mata nauyi Abu dama ga Mai lalurar rashin lafiyar idanu Kara daga idon tai taji kamar andora mata wani Abu Mai nauyi aciki jikinta ko ina yai mata wani irin nauyi yunkurawa tayi tare da kiran sunan ALLAH ya tashi zaune kokarin bude idanunta take Ana ta tunanin Rufe suke Dan dubu take gani dind'im Babu alamar haske sai dai bata sani ba tariga ta bude idanun duhun da ya ziyarci ganinta wani sabon shaci ne ya bude acikin littafin kaddarar ta!

_hmm wai me kuke cine na Baka na zuba? ku Adana tarin tambayoyin ku duk amsoshinku zasu Fito Tafiyar Mai tsayi ce banfara sai da na shirya kudai ku kokarta kui maza kuzo kui payment kar wannna lagwadar dadin ta wuce ku_

Comment
Share
08038541511
[1/26, 9:09 AM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA*
_kalubalenku Iyaye_

*na*
*Zahrabukar*

*exquisite WRITTERS forum*

*masu himma tuni sun fara subscription kui maza ku hanzarta fa kar ayi baku Tafiyar Mai tsawo ce Akwai rikita rikita da bankade bankade cin amana daukar fansa Mai zafi yaudara zamba cikin aminci kawata matso kusa da yan kudinki kalilan ki kwashi garabasar wannan daddad'an labarin*

Normal group #300
VIP #500
special #600
_duk tsarin da kike bukatarku zaki samu Akwai banbanci yawan posting a kowacce rana akan kowanne tsari_
ki biya yan sulallan ki ta wannan account number din *6035968908 keystone bank umma yusif* Sai ki Turomin shaidar biya akan wannan number din 08038541511. Sai insaki paid group

*24*

_*Kai DUNIYA ka Gama tsula tsiyar ka da y"ayan mutane amma ka koma gefe ka darzo dalleliyar mata a kaf garin Nan waye baisan sageer ba? Amma jiba hadaddiyar da ya aura gaskia zai more kudin shi*_

Sageer ? Sageer take ta mai maitawa sageer dai nata Wanda ta sani? Shine zaiyi aure Bata da labari? Ta kalli pic's din yafi a qirga
Amma ta kasa Gane wacece amaryar
_sakamakon kwalliyar da aka mata yasa ta canja_

Amma ta dad'e tana zooming fuskar zuciyar nata mata wani irin zafi ta ma kasa tunanin komai sai dai Tai zooming fuskar ango Tai na amarya ga hawaye masu zafi da suka wanke mata fuska wani irin yanayi take jin kanta a ciki

A haka zeena ta shigo ta iske ta
Ta dad"e tsaye a kanta bata ma San ta shigo ba tafi tayi amma bata motsa ba fizge wayar tayi sannan ta d"ago da sauri tana share hawayen fuskar ta"

Da kallo zeena ta bita cikin manaki tace "kuka?
Me yayi zafi haka da har zaisa ki zauna kina zubda hawayen ki masu matuqar tsada?"

Bata tanka mata ba sai ma qaruwar wasu hawayen da ke zubo mata a fuska

Wacece ita? Meke faruwa da ita? Wani yanayi take ji yana shigar ta mai wuyar fassara

Da sauri ta tashi ta rike zeena tace
"Baiwar Allah wacece ni ? Kema wacece? Ina ne Nan?"
Da kallon banza zeena ta bita tace "ke bansan iskanci ya zan zo in iske kina kallon waya kina kuka Yanzun Kuma ki tashi kina mun wasu silly question?"

"Ni? Ni ke kuka? Hannun ta ta sa ta shafo fuskar ta taji akwai lema kenan da gaske kukan take? To amma wai shin wacece ma ita a taqaice wannan dake gabanta kuma wacece ita ma?

_addu"ar iyaye Bata fad"uwa kasa banza musamman uwa mahaifiya duk da halin da umayma ta saka su gata a kwance a asibity Amma kullum addu'arta Allah ya shirya Mata y"ar ta ya daidaita Mata tunanin ta da Al"amuran ta_

Wani fitinannen ciwon kai ya taso mata Mai tsanani ga wani jiri da taji duniyar na juya Mata
Zeena dai na tsaye sake da Baki tana kallon ikon Allah ganin idanun umaymar na rufewa tana niyyar faduwa yasa Tai sauri" ta taro ta ta kwantar da ita Kan gado

Tana cewa "wai lapiyarki kuwa? Nifa bangane Me ke faruwa ba kike ta wasu abubuwa haka kamar Mai almatsutsai"?

Umayma Bata ma San tanayi ba Dan ji take ana Mata wani gudun dawakai akai cikin ikon Allah ta Kama addu'ah duk wacce tazo bakin ta haka dai ta shafe kusan mintuna Sha biyar tana jin azaba kafin zuwa can Allah ya sa taji ciwon Kan kamar an tsige Mata shi sai Kuma mara ta dauka ita ma
Zeena dai sai ta samu wuri ta zauna tana kallon abinda ke faruwa da umayma Dan ita wani tunanin ta Kira likita ko ta taimaka Mata duk Bai zo Mata ba
Gani ma take kamar rainin hankali ne umayma ke neman Yi Mata
Amma dai bari ta sa ido

Azabar marar ma tafi ta ciwon Kan da har kusan fad'owa tayi daga kan gadon da sauri zeenar tasa Mata kafa ta tare ta
Tana girgiza ta tana cewa "ke Wai bazaki min magana ba?"

Wata irin damkawa da marar ta Mata yasa ta hantsile zeenar ta kife kasa bull taji wani Abu ya bullu ta qasan ta
Sai wata irin zufa taci gaba da feso Mata
Lema taji a kasan inda take kwance ta mirgina ta matsa"😳😳😳 wallahi ni kaina kusan zura wa nayi da gudu wasu irin ruwane green Shar kamar damsa kuka sun jike Mata jiki sai k'udaje sukayo buuu ga wasu qananun tsutsotsi da suka dinga fitowa daga ruwan da sun fito sai su dinqule wuri daya su cure sai su had'e kqnsu sai kiga sun koma wani irin kwaro
Hmm sai da na waiga naga Ashe zeena ita har ta Kai bakin kofa saboda tsabar firgici Dan itama taga abinda yafaru a yanzun din
Umayma dai na Nan sheme Bata San meke faruwa ba wani irin Nishi take Mai ban tausayi tana ambaton sunan Allah da ya kawo Mata daukin wannan azabar da takeji
Cikin ikon Allah kamar da kiftawar ido sai gata a zaune"

Idanun ta sunyi jazur sai kerma jikin ta keyi da kallo tabi gurin da ta take zaune tabi wa"innan ruwan da suke ta komawa" tsutsotsi daga tsutsotsi zuwa qwqri da kallo.sai ta Mike bako tsoron ganin su a ranta ta nufi toilet ta fidda kayan jikin ta tabi jikinta da kallo ganan ruwan Nan a jikinta har sun bushe wanka tayi yafi aqirga ta darje jikinta zuciyar ta nata Mata barazanar tarwatse wa alwala dauro ta fito Dan Babu lokacin tunani a Yanzun bari ta Gama da abinda ke gabanta"
Chapter 15 · 0% Book details