← Book details Karshen Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 20

Sashe 20

Karshen Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Jama'a fa kowa yaji kudi ya rikice

A nishad'ance muka dawo muka iske shi yagaji da suman ya farfado

Baccin wahala ya dauke shi ai da sauri ta koma ta bude fridge ta dauko ruwa masu mugun sanyi Dan har sun fara dutsi ma ta zazzage mishi akan qunar Nan ta joystick dinshi aikam yafasa ihu Yana dirje dirje ya murje ciwo babu digon imani ko tausayi ta kuma barbad"a mishi gishiri akai
Ina gefe ina kallon drama ina dariya sai zillo yake Yana tsalle shi ba biri ba
Hhhhhh Kuma shi ba kwado ba

_(wayyo cikina kai gaskiya wannan currency anyi muguwa ko kunyarda da irin wannan hukuncin ga masu farke mana yara qananu da manya? Wannan hukuncin idan ana musu irin shi gobe ko ance ga yarinya zoka mata fyad"e kuna ganin zaiyi? Ku ajje min ra"ayoyin ku nikam dai🤭🤭barin Yi shiru sai najiku_)

Haka ta koma ta dafa shinkafa half done ba gishiri ba Maggi ba mai sai uban barkono mai masifar fad"a shima salaf yake Babu komai aciki ta zuba yajin Akan shinkafar tazo ta kwance mishi hannu wa tace yaci hannu baka yafara diba hhhhh ai dasauri ya zubar ya furzo na bakin shi masifa ta ishe shi fadi yake ruwa ruwa

Wlh umayma ga ruwan ta hanashi tazo gabanshi ta na tsiya yar dasu yana ta tarba hannu Yana binta ido a rufe amma ta hanashi" da kukan shi yake neman ta fad'a mishi shikam me ya Mata Dan girman Allah tayi hakuri

Bai bani ko digin tausayi ba

Balle in tausaya mishi

Haka dai mukaita ajiyar shi ba laifi Yanzun tana bashi abinci sau daya a Rana
Ruwa Kofi biyu zakuma yayi alwala yayi sallah Kuma har akadau tsawan wata hudu baisan Dani a gidan ba masu cigiya kuwa har lokacin ana ta fama
Kunar Nan ta Joy stick dinshi ta chabe da ruwa sabida rashin magani da kulawa duk ta zagwanye

Cikina yana ta girma Dan har yashiga wata na bakwai

Private hospital nake zuwa awo da nikaf inje indawo

Currency kuwa ta Sami sabbin costomers" harka ta bude" karanta take ci Babu babbaka
Dan duk rintsi bata kawo ka gidan sabida tsaro bata Kuma" kwana a waje duk dare sai ta dawo

Ta boyeni tana bani kulawa dani da d'an cikina muna ta siyayyar kayan haihuwa

Bansan gun wane boka taje ba ya kafe mata kaka malan Dan yasha attempt din guduwa amma da ya fita da kanshi ya ke dawowa

Ya rame ya tsane
Sai uwar qasumba ta wahala ga qunar Nan da tazo warkewa sai ta kuma talbeta" joystick din ta zama yar qarama dama wajen gana mishi azaba
Da yawan fitar ya mata yawa wasu marasa imanin ta dauko aikam suna bashi gwale gwale
Suka yanke mishi qafar shi

Ashe yana da diebitis aikwa kafa taita ciwo

Babu Wanda ya damu ko ya kula sai da ta fara ruwa harda tsutsotsi sannan mukaje aka kaishi asibity a boye itama asibityn ta wani dadiron currency' CE so bamu da matsalar sirri suka duba karshe dai da ciwo yayi tsanani sai dai yanke kafar akai

Sannan ciki na yashigo wata tara so lokacin Ina gida

Can tabiya kudi akai mishi komai aka tattaro shi aka maido likitan yake zuwa' gida yake duba mishi

Ganin azabar tayi yawa yasa nace mata abarshi haka tacemun saura aiki daya dana haihu zan bayyana gareshi kuma dole ya amsa dan yakaiwa hajiya ta rike ta samu dan dakan kuka

Haka kuwa wata ranar alhamis na tashi da naquda" ba jira dama mun shirya komai sai asibity

Ban dadeba cikin ikon Allah na haihu na haifa yata qatuwa jajur da ita

Abin mamakin kuma sakk kaka malan Dan har wata yar Bula kamar hudin kunne ke gefen kunnen Kaka malan to jaririyar nan ma tana da ita

Bayan na huta anshirya baby nima na kimtsa

Currency ta dauko mu sai gida ina ta kallon fuskar babyn kyakkyawa da"ita har a raina naji matuqar qaunar ta to amma fa bikin magaji baya hana na magajiya

Son da nake mata bazai hanani qarasa nufina ba wallahi"

Yau fuskana babu nikab Kai tsaye muna shiga dakin kaka malan muka tun kara ga baby a hannu na"...........✍🏼

*Alhamdulillah masoya masoyan littafinan Nan alkawari ya cika yau dai na gama free page tafiyar yanzun za a fara ta akwai dunkulallun abubuwa dayawa masu bukatar warwara meye makomar zeenah umayma da Kuma currency? Jaririyar fa? Ina fateema Ina sageer? Ina Kuma ilham da Irfan humayda fa? Tahseena da dadiron babanta ummanta Abdul alh wada beery duk suna ina? Wacece badiyya? Wacece ake duka cikin ruwan sama?wacece bintu zeenah?hmmm Taya?: Taya Uba ke haihuwar d'a baisan da shi ba matanshi da kowa nashi baisan da wannan yaron ba? Wai kuma sai yayar yaron ta rikeshi tsawon lokaci da wata siga ta daban bata San kanenta bane wacece ke haihuwa a primary skull lubna and other friends suna ina Saleh almajiri fa? ?*
_duka wadannan amsoshin na cikin littafin Karshen Duniya book 2 dama wasu agaba karki bari karku bari ayi Baku domin tafiyar ta dabance tsarin ma na daban ne ki siya ki karnta cikin salama karki jira na SATA yar uwa Allah ya isa bata da knkanta_

Comments
Shared
Chapter 20 · 0% Book details