← Book details Karshen Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 20

Sashe 8

Karshen Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna Nan zaune suna Bata Baki sukaji sallama
Basheer ne baban mubeena fuskar Nan a tamke idanun shi sunyi jazur ganin surukanshi yasa ya duqa suka Kuma gaisawa suka Kuma Mai gaisuwa kafin suce to mu bari muje Allah ya qara hakuri ita Kuma Allah ya jikanta yasa masu ceto ne" amsawa yake Sama Sama hankalin shi na wurin humayda da ta zura mishi ido ganin zasu fita ne yasa yace mata
"Zaman me kike? Me kike jirah? Ki tashi ki bisu Ina fatan dai Baki manta alqawarin da na Miki ba to Allah ya kawo lokaci Babu ma mubeenar a duniyar Kinga ba sauran wani bango a tsakanin mu Ina fata Zaki mance Dani a tarihin rayuwarki ki Kuma manta dacewa kin taba haihuwa
Wawiya jakar uwa sakarya wlh Baki cancanci zama uwa ba ina tausaya wa Wanda zai Kuma kwasarki yakai gidan shi da sunan matar aure sannan a KARSHEN watannan Ina Miki albishir da cewa zakiji zancen aure na da *FAnnah*"
Bai kula da cewa ta Kuma yin suman wucin gadi ba sai da yaga ta bingire.....

*_afwan dears kuyi hkri Dan Allah suna muke wlh naso yafi haka Amma inshallah idan na dawo da wuri qilan in qara muku uzuri! Uzuri!! Uzuri!!! Dai nasan ba yawa kuyi hkri Dan Allah_*

comment
Share
#repost
08038541511
[1/14, 12:30 PM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA*
_Kalubalenku iyaye_

*NA*
*Zahrabukar*

*Exquisite WRITTERS FORUM*

_To masu cewa Dan Allah indinga banbance musu kar in musu tashi na kamaka Gashi na muku yanda zaku gane_

*BOOK 1is free*
*BOOK 2 is paid*
*sai dai Kuyi hkr Har yanzun ban fidda tsarin biyan kudin ba nasan soyayyah ce tasa kuke ta dokin ku siya nagode kwarai idan nagama wasu shirye shirye zakuga bayani Dafatan kun fahimta*

*14*

_______Fita yayi da sauri ya cimmusu yace "mama Kun fito humayda Kuma kamar Tana da bukatarku a kusa da ita "
Kallon shi sukai har suna had"a Baki wajen "cewa kamar ya? "

Sosa qeya yayi yace "itace tace na mata magana da ku inkun je zakuji"
Ba musu suka juya suka koma gidan

Salati suka saki sanda suka ganta kwance Babu mai musu bayani Dan Bashir Bai ma biyo su ba daga can ya qara gaba zuwa gidan su
Wasu ruwan suka Kuma sa mata wannan Karan ma ta Dade kafin ta farfado sai dai abinda ta farka dashi ya firgita su
Cikin fitar hayyaci take furta wasu maganganu "Meyasa zakamun haka Bashir? Dama baka da imani in rasa y'ata guda sannan kace ka sakeni? Wlh qarya ne qarya kake wlh"
Ta rushe da wani irin kuka Mai Daci da Makakilo duk da kallo suka bita jin wani batu Kuma ana zancen mutuwa ga wani sabon zance

""" Har suka iso gida Bai Kuma tankawa ba shi kadai yasan irin xafin da zuciyar shi ke mishi
Itakam uwar karad'i tun da taji ta bige goshi bata Kuma magana ba
Har suka karaso gidan bayan Mai gadi ya bude musu ta shigo ya na daidaita wa motar Zama yaji ficewar Azeema
Da gudu ta fice a motar ya Dade a zaune Yana tufka da warwara kafin daga karshe ya Sami mafita wani kafirin murmushi yasaki kafin yace *_naku wasa ne in kunsan wata ai Baku San wata ba" ya dai tawace so muzuba mugani_*

Cikin farin ciki yashiga gidan harda y'ar waqarshi a Baki
Ya Sami tarba Mai kyau agun umma ya mata ya gajiar biki tana ta bashi labari har ya shirya suka fito

A falo suka iske Azeema tana kallo da gudu taje ta rungumeta "tace momy we miss u alot gidan so lonely da bakya Nan"murmushi tayi tace "ba wani Nan bayan kin gudu gidan Granny kin barmin daughter ita kadai?"

Murmushi ta kuma yi tace "hmm momy akwai fa labari dazun Ina baiwa Abba labarin ban qarasa ba naji goshi na ya bada dumm
Ban qarasa ba tsananin zafi Kuma Abba ko ya min sannu"
Dariya take tace "ai maganin Parrott kenan gobe ma Kya qara"
Kyabe fuska tayi tace "na ma fasa fad"a Miki tunda bazaki min sannu ba"
Dariya sukaji a bayansu tare suka juya tahseenah ce take musu dariya tace "yau ga umma da autar ta mun gansu a Rana nidai ni da abbana ba ajin kanmu ko Abba?"ta maida tambayr ta gun Abba shima fuska a washe yace "sosai ma Waze ji Kan uba da y"arsa?"

Dariya sukai gaba daya sannan umma tace "muje anshirya dinning "
A nutse suke cin abincin har suka Gama sannan umma tace "Wai nikam Ina Abdul tunda na tafi bami waya ba nadawo Kuma banganshi ba?"
Azeema tace "wlh umma yah Abdul Bai zama gida tun Randa ki ka tafi banqara ganinshi ba" tahseenah ce tace to "kanwa uwar gami
Umma qarya take ko jia yazo ya dauki kaya yace min abokin shi ke asibity to shi ke jinyar shi Kuma a asibityn ya nemi wayar shi Bai ganta" ba"
Ajiyar zuciya ta sauke tace "to alhmdlillahi tunda lapiya wane abokin nashi?"
Abba yace "muheeb yake kowa kinsan sunfi shaquwa ai"

Haka sukai ta fira cikin nishad'i
Kafin lokacin kwanciya yayi kowa ya nufi makwancin shi

_________ Jin qarar horn yasa ta dawo hankalinta kenan sageer fita yayi to yanzun da ya fice ya barta da ilham ita ba likita ba ya zatai da ita ?.
Yarinya ko zama ya gagareta da ta zo miqewa sai fitsari ya zubo ta rasa ina zata saka RAYUWAR ta abin takaicin ma wa zata Kira in ta Kira tace me ? Dan mijin ta yayiwa y"ar ta *fyade* ya gudu sannan shima mijin ya juya musu baya"
Girgiza Kai tayi ta share hawayen da suka zubo mata
Tafara safa da MARWA ta rasa me ke mata Dadi a duniya wane bango zata jingina taji Dadi dama shaquwa tsakanin y"an uwa yanasa cutarwa? Dama soyayya ta Kan zamo makamin cuta?
To ko dai haqqin umayma ne zai Fara bibiyar ta tun a yanzun ?
Cike da tashin hankali kwalwar ta ta juya ta fara tunanin baya "

*_waiwaye_*

Alh sani na Abba shine mahaifin ta mahaifiyar ta " haj habiba Yan uwa ne auren zuminci sukai itace ya ta uku agurin iyayen ta " yah hafeez yah Nadeem sai ita fateema sai qannen ta haris da zubaida" sun taso cikin so da kulawa gata Kam sun sameshi iyayensu sun fi bama ilimin Boko muhimmanci shiyasa basui zurfi a ilimin addini ba
Mahaifiyar ta Bata da kishiya Amma haka ta taso da tsananin kishi"
Kishinta har akan Yan uwanta nunashi take ko wani Abu aka Basu ko kala a ka canja to sai tayi kishin an Bata kala mara kyau haka zatai ta Jin zafin Yan uwanta har sai an hada kayan wuri daya ta zabi abinda takeso sannan a zauna lpy haka aka Saba mata da wannan Hali har girmanta

Sageer salees Dan kano shine sunan shi da na qarshe a gidan su su hudu ne a gidan su yayyenshi mata ne shine kqdai namiji yataso cikin gata da kula shima Bai samu zurfin ilimin addini ba" ya dai samu na boko Dan yanzun haka ma da bokon yake ci"
A sangarce ya taso Dan ba kwaba ba kyara " aqalla ba a kasara ba yayiwa yan mata" shida ciki wasu sun San gidansu wasu Kuma Basu sani ba ma"abocin yaudara ne ya iya tsara mace shiyasa Bai shan wahala yake Jan raayin su su fada tarkon shi"
Koda kin kai qara gidan su to iyayen sa basa masa fad"a sai ma sui muku barazanar zasu sa akulle ku yawanci suna barin cikin su Haifa sai su Kai titi su Yar wasu kuma su jefa masai wasu Kuma zubar da cikin ma sukai wasu ta sanadiyyar haka iyayen su suka koresu suka fada duniya

_watarana_
Yana tafe a mota Yana shan kida har ya qaraso wani park parking yayi yafito ma"abocin ado ne Dan haka a yau din ma cikin adon yake" Yana tafia Yana basarwa har ya gota inda suke zaune yadawo da baya da yake ya iya basarwa sai ya nuna kamar ba Dan su yadawo ba hasalima sai ya dauki dutsi Yana da Dan jefashi Sama Yana cabewa cikin Sa a kuwa" ya cilla wani sai akan screen din wayar ta""" a tsorace ta dag'o taga meye ya fad'o idon ta ya sauka cikin na shi...........

_to fans Allah yakawo mu mu waiwaya zamu tsunduma Muji shin menene tushe mafari? Gamu dai ku biyo ni zan warware muku duka abinda yashige muku duhu_

Comment
Share
#repost
08038541511
[1/15, 2:23 PM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA*
_Kalubalenku iyaye_

*NA*
*Zahrabukar*

*Exquisite WRITTERS FORUM*

*15*

________Kurawa juna ido sukai na tsawon sakanni daga bisani shi yafara kauda na shi idon ,
Itama janyewa tayi cike da kunya
Murmushi yayi yace "sorry pretty Ina fata dai ban Miki b'anna ba?"
Itama murmushi tayi tace "ah ah baka min banna ba ko kamin ma na yafe"
Zama yayi akusa da ita yace "to ngd da gani dai wnn gimbiyar akwai saukin Kai "
Dukar da kanta tayi batace komi ba" fateema dake gefenta ta tsura mishi ido
Bai ma San tanayi ba hankalin shi na gun umayma fira suke kamar wadan da suka Saba umayma ce ta gabatar mishi da qawarta fateema kallo daya ya mata ya Kau da Kai bayan yace "sannu fa" cikin rawar murya tace "Ina wuni"
"Lafiya"kadai yace ya kauda idon shi
Haka sukai ta fira cikin salon iya tsara mace a Dan zamansu har yasan sunan ta anguwar su hada no din wayar ta ya karba
Da suka tashi tafia ma shi ya daukesu a motar shi suka bita shop yamusu siyayya sannan ya Kai kowacce gidan su yayi mamakin ganin gidan su umayma Bai Kai gidan su fateema tsaruwa ba Bai wani damu ba
Ya mata sallama ya tafi,
Chapter 8 · 0% Book details