← Book details Karshen Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 20

Sashe 13

Karshen Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdul dai hankali ya kwanta Jin cewa tahseenah da ranta sai leqen ta yake ta tagar dakin da aka kwantar da ita azeema ma ansha kuka angaji har anyi bacci
Shima abban idanun shi duk sun kod'e
Waya ya d"aga ya kira haj yahanazu ya sanar da ita cewa y"an fashi sun hauro musu har sun wa tahseenah fyad'e
Cikin tashin hankali take Amsa wayar bayan Gama wayar ta sallami dadiron nata ta had'o kayan ta nufi Tasha ta hawo mota
Bayan saukar su napep ta tare ta Kai ta asibityn
A asibityn taso tada hankali sai an kai report wajen Yan sanda an nemo barayin
Abban ne yayi ta lallashin ta Yana nuna mata illar Kai report din kamar tonawa kansu asiri ne Dan ba lallai akama barayin ba ko an samesu sun batawa yarsu suna ba kowa ne zai aure ta ba banda tsangwamar da zata sha agun mutane
Da lallabi dai yasamu yace taje gida Tai wanka Tai musu girki sai ta dawo shima sai ya tafi
Keyn motar ya bata suka tafi ita da azeema Dan Abdul Bai bi ta ba
Idanun ta sunyi luhu luhu "
_oh jama"a kuji fa wani rainin sense" wanzami bai San jarfa itafa da auren ta take bin yara qanana Tana bata musu tarbiya da kudi tana koya musu zina amma yau biyan bashi ya biyo ta kan y'ar cikin ta hankalin ta ya tashi hmm🤔🤔waifa Dan ma Bata San gaskiar lamarin ba knn_

Comment
Share
08038541511
[1/23, 8:59 AM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA*
_kalubalenku Iyaye_

*na*
*Zahrabukar*

*exquisite WRITTERS forum*

*masu himma tuni sun fara subscription kui maza ku hanzarta fa kar ayi baku Tafiyar Mai tsawo ce Akwai rikita rikita da bankade bankade cin amana daukar fansa Mai zafi yaudara zamba cikin aminci kawata matso kusa da yan kudinki kalilan ki kwashi garabasar wannan daddad'an labarin*

Normal group #300
VIP #500
special #600
_duk tsarin da kike bukatarku zaki samu Akwai banbanci yawan posting a kowacce rana akan kowanne tsari_
ki biya yan sulallan ki ta wannan account number din *6035968908 keystone bank umma yusif* Sai ki Turomin shaidar biya akan wannan number din 08038541511. Sai insaki paid group

*21*

Cikin fusata baban ya Isa inda take ya fizge wayar ya buga ta da kasa sannan ya fizgota ya falla Mata maruka gefe da gefe ya wurgar da ta qasa zai taka Mata ciki kenan mamar Tai sauri ta tare shi tana kuka tana cewa "kashe ta Kuma zakai ? Haka ake gyara?"
Cikin tsananin zafin Rai shima da bakincikin halin da umaima ta tsiro dashi yace "har abada ban haifi d'n da zai mun kallon banza ya watsar ba wlh duk iskan cin da takejin zata zo dashi daidai nake da ita ada nashigo ne domin in tabbatar da cewa shin hauka ne kamar yanda ke kike tunani ko Kuma iska ne ya takata to wannan ba hauka bane tsabar ba kuma ruwan aljanu tsabar wulakanci ne da tsagwaron iskanci ne wanda ba zan dauka ba agidan Nan "
Cikin huci da d'aga murya yakai qarshen maganar
Mutuniyar taku kuwa ko gezau dan maman ta na tare dukan da baban yayi niyyar yimata ta tashi ta kakkabe wandon ta ta koma jikin bango ta jingina duk wannan fad'an da yake bata ma San yanayi ba Dan ita tama shilla duniyar tunani,

To Amma dai ai bata haka yakamata ace an bi ta ba kafa San umayma lafiya lafiya Rana tsaka bazata billo da wannan sabon halin ba"
Wani mugun kallo da yawatsa mata yasata ta ajje maganar tai diff Tana rarraba idanunta ya kalleta shima Yana kuma matse girman idanun shi sannan yace "to sannu kaza uwar son ya"ya wallahi kinji me na fad'a ko bazan yi kaffara ba karya take
Idan zata ajje duk wani salon iskanci gefe to ta ajje in ba haka ba itace da wahala ke ko haukan take kamar yanda kike tunani ko to wallahi qaryar hauka yaci uwar Shi daidai nake da kowane irin shed'ani"
Ya buga rigar shi ya bangaje aunty amarya dake tsaye tana raba ido ya fice,
Tsaki sukaji taja tace "sai kuyi ai in cigiyar kazar makwafta alkayri ne Kuma wlh tallahi Babu Wanda ya Isa ya takura min ehe a buga a saki bata maganin d'an iska
Dama kindaina wannan kukan mama Dan ni wannan d'an bugun da yamin ko a kwalar rigata
Ya maida wuqar shi kube
In yanemi samun ido a harkokina to wallahi nemana ma zakuyi ku rasa wannan duniya Mai fad'i?
Ehee Tom in ma za'a lallabani a barni inyi rayuwar y'anci abarni in ba haka ba. Tai Wata kwafa tana jujjuya idanu
a fusace mamar ta taso tana kuka itama ta rufe ta da duka tana cewa "in ba haka ba Kuma me? Ki karasa Mana qaramar marar kunya wallahi kinyi kadan bakin cikin ki ya kasheni kafin ki doran hawan jini ko ki dora wa mahaifin ki gwanda na kashe ki kowa ma ya huta" maganganu take saki cikin fitar hayyaci da tsananin tashin hankali
Ganin umaymar bata motsa ba bare Tai kokarin kwatar kai yasa aunty amarya janye ta ta tura ta waje tace "in rai yabaci hankali kar ya gushe ki dawo hayyacin ki Yar ki ce kada ki mata mugun baki
Kuma kin san illar hakan"

******************
Batare da ta tankawa aunty amarya ba tafice tanufi dakin ta da gudu
Ta wuce umaymar dake zaune falo tana jijjiga jiki

**********************
Idanun ta sunyi jazur sanda suka isa gidan dan ba qarya fa tana cikin tashin hankali
Ba qaramin buri ta daura akan tahseenah
Ba Allah kad"ai yasan burin da taci akan
Yanmatancin tahseenah har zuwa auren ta Amma yanzun wani qaton banza ya rushe mata budget Kuma yaci bulus
Zata aurar da budurwa matsayin bazawara

Haka dai ta surutai azeema na kallon ta wankan ma bata samu tayi ba abincin kawaii ta girka mai sauki ta dauki abinda tasan zasu buqata a asibityn ta rufe gidan dama bata shigo da motar ciki ba a waje ta barta
Da wani irin gudu take tafia da ta tuna yanda ta hangi tahseenah a kwance kamar gawa sai taji kamar kafin sukai za a kirata ace mata ta mutu haka dama iyayen da akayiwa
Yaransu *fyade* sukeji? Lallai Ashe Akwai masu kakkarfar zuciya acikin mutane Tabdin
Wallahi da ace Yanzun zatai ido hudu da shegen da ya farke Mata y'a wlh itace ajalin shi
_nace anya kuwa?🤔_

*********************

Cikin kwana biyu soyayya ta yi nisa tsakanin basheer da humayda ruwan love kawai suke zubarwa
Basheer d"an katsina ne karatu yakaishi adamawa tun yana d'an shekara tara aka kaishi almajiran ci cikin ikon Allah da fadi tashin rayuwa a makarantar ba a bara za a kai yaro da abincin shi har na shekara to idan yaro yakai shekara Sha biyar to alokacin za a yayeshi daga kawo abunci sai ya tafi ya fara kananun Sana'o'i Dan ya ruke kanshi a haka shima yai tashi rayuwar har Allah yasa ya mallaki hankalin shi lokaci zuwa lokaci yana ziyar tar iyayen shi dake katsina yaje musu da abin alheri daga cikin irin fad'i tashin da yake na neman na Kai
A hankali har yasiyi fili a katsinar Yana ginawa a hankali iyayen na taimaka mishi

A haka suka had'u da humayda da sunyi soyayya mai tsafta ita Yar adamawa ce inda karatun ta da kaf din rayuwar ta anan ta yita bata da yawan qawaye qawarta daya *fannah* tun kuruciya a tare suka tashi qawancen su na muddin Rai kowa baya boyewa kowa damuwa ko farinciki son Gaskia ne a tsakanin su babu hassada kyashi bare bakin ciki ba tare da bata lokaci ba iyaye suka shiga maganar
Duk wani shiri na hidimar bikin *fannah* ce a gaba haka dai akai biki lpy aka watse akayo da amarya garin katsina _ta dikko dakin kara kunya garemu ba dai tsoro ba_

Amarya ta tare a gidan ta suna rayuwar su cikin aminci da kyautatawa juna

*******************
Durkushe take bakin kofar dakinta ruwa ne Ake tsugagawa kamar da bakin kwarya Amma dakin a Rufe yake duk bayan lokaci sai tasa hannu ta bubbuga Dafatan Wanda Ke ciki ya bude mata duk ruwan nan batai yunkurin kare kanta daga zubar ruwan ba tadai lullube goyonta Sai jijjiga yarinyar dake ta tsala ihu take ga wani irin sanyi tayi kuka tayi kuka tayi rokon da magiyar Amma duk a banza Wata irin tsawa da akai yasa yarinyar bayanta ta daddage ta kwallah wani irin ihu ta firgice a gigice take Haka ta dage da Dan sauran karfin da yaragen mata ta cigaba da dukan kofar a fusace nacikin dakin ya bude dakin Wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke Tana niyyar kutsa Kai cikin dakin ya fizgo ta ya dage ya fallah mata Mari bata damu ba tai kasa da kafafunta zata Fara rokonshi yayi kwallo da ita tsakar gidan bai dsmu da ruwan da yafara jikashi ba ko kukan da yarinyar ta tsala jin ta gwaru da kasa ya zaro belt din wandon shi yaci Gaba da dukanta yadake ta yahado da yar idanunshi sun Rufe zuciyarshi ta dugunzuma dukanta kawai yake tun Tana Jan Jiki Tana girgiza Kai Har tai lakwas kukan yarinyar ma ya dauke diff sannan ya saurara ya buga tsaki yabar su nan sheme cikin ruwan Babu Mai kwakkwaran motsi
👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼

comment
share
08038541511
[1/24, 9:25 AM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA*
_kalubalenku Iyaye_

*na*
*Zahrabukar*

*exquisite WRITTERS forum*

*masu himma tuni sun fara subscription kui maza ku hanzarta fa kar ayi baku Tafiyar Mai tsawo ce Akwai rikita rikita da bankade bankade cin amana daukar fansa Mai zafi yaudara zamba cikin aminci kawata matso kusa da yan kudinki kalilan ki kwashi garabasar wannan daddad'an labarin*

Normal group #300
VIP #500
special #600
_duk tsarin da kike bukatarku zaki samu Akwai banbanci yawan posting a kowacce rana akan kowanne tsari_
ki biya yan sulallan ki ta wannan account number din *6035968908 keystone bank umma yusif* Sai ki Turomin shaidar biya akan wannan number din 08038541511. Sai insaki paid group

*22*
Chapter 13 · 0% Book details