← Book details Karshen Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 20

Sashe 7

Karshen Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rarrashin su tayi ta dubara ta nuna musu Suma watarana dasu zataje sun tafi cike da farinciki
Da jindadin irin hasashen da tayo musu na zama manyan mata"
_allah kamana maganin shaidanun cikin mu_

___________________
Karfe bakwai da mintina akai janazar mubeena aka Kai ta makwancinta
Har lokacin kuwa humayda Bata da labari ya daije gidan su ya faɗa wa iyayenta cewa mubeena ta rasu, so ko da suka zo Basu ganta ba sai sukai tunanin ko ita acan zata zauna. bayan andawo ne wasu cikin su suka Yankee shawarar zuwa sui mata gaisuwa kafin su wuce, Kuma a bar mata kanwarta haseena ta zauna mata

********************
Ko da taje makarantar su Saleh a firgice tayiwa malam bayani hankalinshi ya tashi shima matuqa kafin ya lallabata yace ta koma shi zai fita Nemo Saleh itakuma taje ta Nemo baban mubeena da mubeenar kafin zuwa safia aga abinda hali yayi

Gida ta dawo domin jikinta ba kwari wani zazzabi ya sauko mata Mai matuqar zafi ga wata irin faduwar gaba ciwon Kai ga wani Abu da takeji Mai Kama da kewa kewa na zagaye ta no u want a Sai Tsira suke sun cika ba a tsotse ba
Shiru shiru dai Bata rufe gidan ba har wajen asuba ta na Nan kwance zuciyar ta ta mata nauyi
Sallah aka Kira a Kan kunnen ta Dan haka ta tashi taje ta dauro alwala _abinda ta manta rabonta da tayi kenan sallar asuba akan lokacin ta sai dai in gari yawaye Rana tafito sannan_

Sallamar da taji anayi ne ya katse mata tunanin ina ta dosan da takeyi, Dan har wayewar garin Nan dai ba a ga Saleh ba mayafin ta ne a gefen ta bayan ta koma gidan malamin su Salehn yace har yanzun shiru sai da ya tambaaye ta Wai ina ma yarinyar tukun ina Kuma mahaifin yarinyar? Cikin karfin Hali "tace yatafi da ita asibiti tun a jiyan"
Duk da kuwa in za a Dora mata wuqa a wuya bazatace ga inda suke ba,
Duk ta zure ta rame kwana guda kacal
Haka ta dawo gidan ta zauna tana jiran tsammani

A firgice ta ɗago Kai jin sallama da murya sak ta maman ta da kishiyar ta sai qannen ta biyu da kallo ta bisu tana share hawaye sun tausaya mata qwarai ganin yanda ta rame ko da yake ai dole rashin da?

bayan sun zauna mamance ta mata sannu gabanta na ta faduwa kenan baban mubeena yakirasu ya faɗa musu sakacin da tayi? Ya fada musu rashin kular ta yayi sanadin *fyade* wa y"ar ta?
Tunanin ta ne yakatse bayan mamar tata tace kiyi hakuri humayda duk Kan mai Rai ai mamaci ne addu'ah Zaki mata Bata da haqqin kowa a kanta sai naki ki daina kuka" ido ta zura wa mahaifiyar tata bugun zuciyar ta ya qaru wane irin baqaqen kalmomi mama ke aiko mata dasu haka" ?
Murmushi tasaki bayan wani tunani da yazo mata kenan baban mubeena Bai sanar dasu komai ba to Amma wacece ta rasu ? Karfin Hali tayi ganin su duka sun zuba mata ido suna kallon ta tace "Mama wace CE ta rasu Kuma? Kuma ni haqqin mene nawa akanta da zan yafe mata?"

Kallon kallo aka fara tsakanin iyayen da yaran
Meke faruwa ne to?

******************
Bayan magrib abba ya biya gidan su ya tafo da azeema uwar karaɗi ita ta matsa akai ta yanzun kuma taji umman ta tadawo tace ta fasa zaman ita a Maidota gidansu inda ba acin tuwo
Tafe suke Kan hanya tana bashi lbri zuwa can tace "hmm abba ban baka labari ba"
Murmushi yayi yace "ta samu kenan azeen Abba?" itama murmushi tasaki tace "sosai kuwa Abba jiya fa ne akai wani baqo gidan granny bayan ya tafi nike cewa granny waye wancan hmm abba sai da tayi daria tace Wai sabon angon tane shine zasu aura wa aunty tahseenah tund... ai Bata qarasa ba taji Kan ta ya daki dashboard din motar Dan wani wawan burki abban yaja jin wani sabon zance
__________

Kuka take riris shi kanshi daddy kukan yake sun tasa ilham a gaba, bayan tagama basu
Labarin yanda Irfan ya mata fyade da yanda suke wasanni acikin bathroom in suna wanka da yanda suke leqen iyayen in suna halin auratayya, kunya takaici nadama tare da danasani suka taru suka rufesu yau wace irin rana CE? Dan su yawa yarsu fyade bayan yagama ganin sirrin kwanciyar su sannan ya gudu ashe duk tsawan shekarun nan a tsirara sukeaa idanun yaran? Ashe suna tufka ne kuma suna warware ta da kansu? Yanzun me gari ya waya?
Wata wawiaqr ajiyar zuciya sukaji ansaki mai tattare da huci mai tsananin zafi su duka suka yi saurin kallon inda ilham take
Tace "Mommy, Daddy" Duk kai suka dago' suna kallon ta sannan ta juya Kai tace
"Kunyi kuskure Kun tafka babban kuskure wanda gyaranshi zai mana wahala ya Irfan ya cuceni amma bani yayiwa ba tabbas kanshi yayiwa sannan na dauki alqawarin muddin ina raye a duniya wallahi wallahi sai naga bayanshi"
Ta fashe da wani irin kuka Mai cin Rai taci gaba da cewa "duk da qarancin shekaruna na ji zafin abinda yamun Wanda uwata mahaifiya ta itace silar komi tare da taimakon mahaifina Ina fatan zaku kau da Kai ga duk abunda zakuga Yana faruwa
Domin wlh tallahi sai na dasa wa Irfan baqinciki a rayuwa duk da bansan a Ina yake ba amma tabbas zan nemeshi zan nemeshi ko a Ina yake a fadin duniyar Nan".........

Comment
Share
#repost
08038541511
[1/13, 11:46 AM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA*
_Kalubalenku iyaye_

*NA*
*Zahrabuhkar*

*Exquisite Writers FORUM*

*13*

A firgice suke kallonta Anya kuwa wannan ilham ce? Ilham dai tasu yarinya yar shekaru Tara itace ke furta wadan Nan maganganu?
Innalillahy wa Inna ilayhirraji un tabbas sunga illar sakaci
Momy ce tai qarfin Hali zuciyarta tai duhu wani irin tukukin maseefa Ke Taso mata cike da bana'i Kai tsaye tace
"Sageer"
Kaga rayuwa ko? Kaga yanda Al"amura suka juye Mana lokaci daya ko ? Dan ka ya tarwatsa mun yarinya sannan ya jefe man ita da baqin asiri wallahi wannan ba y"ata ilham bace ilham batai girman da xata iya furta wadannan kalmomin ba bayan abinda ya mata sai Kuma ya haukata mun ita? wallahi bazai yuwu ba naga sakamakon soyayya naso shi domin Allah da zuciya d"aya Ashe burin shi ni ya kassara min rayuwa'? "
Tashi tai ta dawo inda ilham din take ta dafata tace "wannan ba yaqinki bane Ke kadaice wannan yaqine da zamuyi shi da dukkan karfin mu da kudin mu da jikinmu da muggan takubba wallahi tallahi na Miki alqawarin muddin ina raye a duniyar Nan wlh tallahi sai na kawo Miki Irfan a wulaqance sai kin taka gawar shi bayan na mishi hukunci Mai tsanani tabbas wannan alwashi ne"
Juyowa tayi ta kalli daddyn tace"Ina fatan zaka kauda ganin ka ka kiyaye jinka da duk abinda zaka ga Yana faruwa domin wlh bazan yi kawaici ba "
Wani mugun kallo ya wurga mata yace "tabbas yanzun na tabbatar da cewa qwaqwalwar mata gajeren tunani take kin manta? Kin manta in tuna Miki?
Ke a yanzun laifin Irfan kike gani?
Kin manta abubuwan da Kika dinga yiwa mahaifiyar shi har tabar duniya?
Na zuba Miki idone domin yaran mu Amma wallahi a wannan yqkin babu hannu na aciki kibarni in tunkari bala"in da ke tunkaroni na Tabbata wannan tarihi ne ya maimaita kanshi"shima ya karashe cike da numfarfashin maseefa

Tabarmar kunya ta fara nadewa da hauka tana wasu maganganu shaf su duka sun manta cewa akwai ilham a gurin'
"Au haka zakace ? Me na mata Banda taimakon da na mata ? Oh to me kqkeson cewa? Ka tona min asiri wlh kayi kad"an daga Kai harshi sai in wulaqanta ku Kuma in zauna lapiya abinda ya faru inace ba Wanda yasani daga ni sai Kai sai abbana to ta ya ya Irfan yasan wayeshi?
Ohh to kenan Kai ka zaunar dashi kq fada mishi shine kuka hadu kuka yanke shawarar yi ma y'ata *fyade* to anyi walqiya ta haska na Kuma ganku Amma wlh ku jira yi waiwaye n.. saukar wasu tagwayen maruka da taji yasa sauran maganar maqale wa"yace kee Fatima ki farka in mafarki ma kike to ki farka bazan dauki wanann iskan cin ba Amma idan kikai wasa Irfan baisan Waye shi ba Amma wlh a wannan taqin tsaf zan bayyana wa duniya Waye Irfan mecece alaqata dashi wacce ke kanki ba kisani ba ba ke ba duk wani ahalin ki sai ya jijjiga so Ina so ki tanaji ma"ajin tashin hankali zuwa lokacin da gaskia zata bayyana Dan tana gaff"
Ya Kuma watsa mata wani kallon ya bangajeta ya fice"
Wata juya CE ke neman kadata tai sauri ta dafe bango"
Wasu sabbin maganganu taji sageer na fad"a me yake nufi ?
_nace bishi ki tambayeshi Kya tambaye ni Nima insha maruka_?

🤔🤔🤔

_kar kuce komai ku adana tambayo yinku_

""" Suman ta uku tana komawa da ansa mata ruwa ta dawo sai Kuma ta koma a na qarshen ne dai akasamu ba ta koma ba
Kukan ma ya kasa fita ta rasa a wanne muhalli zata ajje wannan baqin labarin y"ar ta kwaya daya jall yau ta zama gawa.? Kenan ganin bankwana ta mata lokacin da ta ganta kwance cikin jini? Wace iriyar sakayya Saleh ya mata haka ?
Shikenan ta rasa kwan da ta wahala kafin ta gani? Innalillahy wa Inna ilayhirraji un hasbunallahu wani imal wakeel tabbas kuka ma rahama meyasa baban humayda zai mata wannan hukuncin? Y"ar ta ta mutu ba a Gaya mata ba sannan har akai Jana izar ta Bata da labari me kenan?
_nace tambayi kanki_
Chapter 7 · 0% Book details