← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 32

Sashe 4

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sumayya ta yi tsaki ta ce "Haushin kaina nake ji, da na karanci aikin jarida Arfa"

Cikin mamaki ta ce "Amma meyasa, na ga shi ne zaɓinki?"

"Wallahi duk ya fita daga kaina, hira aka yi da honorable Indabo, wai an yi borehole a ƙananan Hukumomin da yake wakilta, an raba kayan makaranta ga ɗalibai. An kai bencina makarantun firamare da na islamiyyu. Last week aka ce na je na tattauna da al'umman local government ɗin, na je ni ban ga ayyukan da aka yi ba, na tattauna da mutanen ƙananan hukumomin, sun ce ba ayi musu ba. Na kai recording ɗin, aka saka, wai lawisa ba ta tantance shirin ba, ba ta sani ba aka saka, kin ga cin mutuncin da aka yi mini, wai zan lalata musu business wai sai na je na samo mutanen da zan yi hira da su, su ce eh an yi ayyukan su yi godiya alhalin ba ayi ba. Na zama maƙaryaciya kenan me zan ce wa Allah? Wai har da idan ban yi wasa ba, sai honorable ya saka an ɗaure ni"

Nabila ta ce "Ikon Allah, ashe duk kanwar ja ce sumy, yo nima hakan take ai, wani tasonon Alhaji ne ya zo yayi kirim a kan kujera kamar damin doya, ya biya uban kuÉ—i wai za a kare shi, ya cuci talakawa ko kunya bai ji ba, kuma director ya sakani a team É—in lauyoyin, ni dai ba zan yi ba wallahi, sai dai ya yi ta gaya wa Abban. Haka kurum a cuci mutane ka je ka cewa Allah me?"

"Wallahi Nabila, ba ki ji zuciyata ba, yanzu sai dai na je na tara maƙwabta na yi hirar ƙarya da su, a zo a sake sakawa, kuma wai sai na rubuta takardar ban haƙuri, ki ji fa"

Nabila ta ce "Tirƙashi, wai ya ɗaure ki, to ya ɗaure ki shi ma ya hau da ɗaurin Allah " Haka suka cigaba da tattaunawa, har suka isa in da sumayya za ta sauka.

***

Cikin tsananin tashin hankali, yake magana, kallo ɗaya zaka yi masa ka san hankalinsa a matuƙar tashe yake.

Ya daki teburi ya ce "Kwamishina, dole fa ku nemo yaron nan, dole ku mayar da hankali a nemo shi a duk in da yake a ƙasar nan"

Mutumin da yake zaune cikin kakin ƴan sanda ya ce "Honorable, ka kwantar da hankalinka, aikinmu baya buƙatar garaje da gaggawa, sai mun bi a sannu"

"Haba Cp, wane irin bi a sannu? Rayuwata na cikin hatsari, yayi iƙirarin kashe ni, dole fa a nemo yaron nan, ko be kashe ni ba, idan ya buɗe bakinsa yayi wata magana a kaina kashina fa ya riga ya gama bushewa, na san fa waye yaron nan ciki da bai"

Cp ya gyara zamansa ya ce "Amma honorable, wace irin yadda ko alaƙa ce tsakanin ka da yaron nan, da har ya sanka haka, zamansa a gari yake barazana a gareka"

Tsaki mutumin yayi ya ce "Kai har ka tambayi alaƙar da ke tsakanin ɗan siyasa, da tantirin ɗan daba, ɗan iska? Ku nemo shi dillalin wiwi ne, da hard drugs. Da kun ganshi ma kawai a harbe shi, kuma a tuhumi controllern gidan yari, a kan dalilin sakinsa, bayan ko shari'a ba ayi masa ba tsawon lokaci"

Ɗan sandan ya jinjina kai ya ce "Shi controller ya ce court order ya karɓa"

"Ni dai ka yi mini wannan taimakon a nemo shi da gaggawa, dan yana cikin garin nan, tun da ga ayyukan ta'addanci yana ta yi yadda ya ga dama".

CP ya ce "In sha Allah, ka kwantar da hankalinka za ayi duk mai yiwuwa, zan nemi zaƙaƙurai daga cikin mutanenmu, da suke dealing da criminal cases, very soon zai zo hannu, DSP Nasir na san zai yi abun da ya dace in sha Allah"

"Yauwwa to shikenan, ko dai sanarwa za ku yi, ace duk in da aka gano shi a kamo shi, an sake shi ba bisa ƙa'ida ba"

Da sauri ya ce "No ai ba haka aikin tsaro yake ba, ai wannan abun kunya ne ga hukumominmu, yanzu sanin in da yake shi ne babban target É—inmu, dan yaron yana da wayo sosai, na bibiyi record É—in sa, sai an yi taka tsantsan sosai wurin kama shi, sai an yi amfani da dabarun aiki, hatsabibi ne sosai"

"To ayi ƙoƙarin hakan dan Allah".

***
Gudu-gudu sauri-sauri ta ƙarasa gida, saboda azababben fitsarin da ya cika mata mararta, tana zuwa ɗaki ta watsar da komai a kan gadonta, ta shiga banɗaki.
Sai da ta gama fitsarin, ta ji iska na shigarta, tayi wanka ta fito, ta tattare kayan da ta watsar, ta samu riga ta shan iska ta saka, ta shafa turare ta fita.

Kitchen ta shiga dan zuba abinci, ta ci karo da fate-faten wake a cikin food flask ɗin ta. A ƙule ta ja uban tsaki, ta fito babban falo kamar ta fashe da kuka, ta hau ƙwalawa mai aikinsu kira.

"Baba magajiya!"

Daga can wani sashen ta amsa da "Na'am, Arfa gani nan"

"Na ga faten wake yau?"

"Eh, umarnin Hajiya babba ne, ita ta ce ayi faten wake".

Cikin É—aga murya arfa ta ce "Amma dai an san ba na ci ko? Kin dafa mini wani abun ne?"

Magajiya ta ce "Wallahi har na É—aukko doya na fara frayewa, na É—an dafa miki, na soya miki miya, aka kuma sakani aiki".

Nabila cikin kwakwazo take masifa "Saboda tsabar an tsane ni, so ake na mutu a huta, in je aiki in dawo a kasa ajiye mini abinci, sai a dafa abun da ba na so"

"Ke Nabila meye haka ne, hajiya ce ta bayar da umarnin hakan, ki shiga kitchen ki dafa wani abun mana" Nabila ta kalli Yaya Sauda ta ce "In je in dawo yanzu, sannan in shiga kitchen in hau girki, bari in je in sha faten waken, duk abun da ya same ni, ku kuka kasheni, ai kun san likita ya hana ni cin wake"

"To ki je ki ci ɗin mana, idan kin mutun sai ne? Banda gulma amma ai ki na cin ƙosai da shinkafa da wake, ko duk su ba waken bane ba"

Kamar Æ´ar goye, Nabila ta din ga zirarar da hawaye ta na bala'i.

"Kar Allah ya sa ki ci abun da aka dafa, kya mutu da yunwa agola Æ´ar wahala".

Cikin tsananin fusata Nabila ta ce "Tun da dai ba shegiya ba ce ni da ubana, ai da sauƙi"

Cikin son kunna Nabila, Sauda ta ce "Meye marabarki da mara uban?"

Baba magajiya da ke tsaye ta ce "A'a Sauda, dan Allah kar ayi haka, ke fa babbace"

Sauda ta ɗaga mata hannu tare da cewa "Babu ruwanki, ki wuce ki ƙarasawa mama aikinta. Ke kuma ki tsaya ki cigaba da hauka, banda samun wuri ina na taɓa ganin agola da miƙe ƙafa".

"Ai gara ni, agolar ce, kuma iya wuya ni ƴar gari ce, ba baƙuwar haure ba, jikar yarabawa. Kuma ni ba dan albarkacin ubana ba, wallahi da na daɗe da barin gidan nan, gara na je na kama gida na yi zaman kaina, iyaka ace ina zaman kaina, ba ɗan iskan da zai takura mini"

Sauda ta tsaya ta ce "To ki je ki kama ki yi zaman kan naki mana, ke dama banda Abba a tsaye yake a kanki, ai Æ´ar zaman kantan za ayi, kuma Æ´ar gagara".

Nabila ta buɗe baki za ta yi magana, suka ji gyaran muryar Abba, daga saman bene. Tuni idon Nabila yayi jawur, saboda kuka da ɓacin rai.

Ya ce "Magajiya" cikin sauri ta ce "Na'am ranka ya daÉ—e"

"A gabanki kina tsaye yaran nan suke faÉ—a? Ki ka kasa tsawatar musu?"

Ta risuna ta ce "Tuba nake ayi mini afuwa".

Sauda ta ce "Wallahi Ab...." Ya dakatar da ita ya ce "Ban tambaye ki ba, kukan me ki ke yi ke kuma?" Yayi maganar yana kallon Nabila.

"Faten wake aka yi, ba a dafa mini komai ba, kuma yunwa nake ji"

Ya ce "Wannan abun kawai shi ne abun kuka kuma? Ke a rayuwarki ba zaki taɓa girma ba kenan?" Tayi shiru tana sheshsheƙar kuka, kukan da yake jin sa har zuciyarsa.

"Magajiya, ko aikin wa ki ke yi, ki ajiye ki sama mata abun da za ta ci, ba biyanki nake dan a farantawa wani a ɓatawa wani ba, duk ƴaƴana nawa ne, babu banbanci a tsakaninsu"

Ta risuna ta ce "In sha Allah Alhaji, za a kiyaye"

"Ke kuma, ki cigaba da faɗa da yayyenki, zaki ga yadda zan yi da ke. Kuma na gode da furunciki Arfa, zaki yi zaman kanki ko? Tun ina raye ki ke wannan iƙrarin, ranar da na mutu ban san me zaki aikata ba, kin kyauta" bai tsaya jiran me za ta ce ba, ya wuce ya koma ɗakinsa.

Sauda ta yi wa Nabila gwalo, Nabila ta ce "Ai ke yakamata na yi wa gwalo, ni na yi nasara, tun da an ce a ajiye aikin babarki ayi nawa, banza ƙatuwar kwabo" Nabila ta wuce ɗakin su, tana tunanin ko dan wannan tijarar, ya isa tayi fatan tayi aure ta bar gidan nan.

***
Ɗan siririn matashi ne dogo, wankan tarwaɗa, sanye da kakin ƴan sanda, da ɗan hanzari yake bin wata doguwar baranda, wadda ta sa da shi da wata ƙofa.

Ya buɗe ya shiga da sallama, ya sarawa wanda ya tarar a cikin ofishin, wanda da gani babu tambaya, ka san babba ne sosai a cikin rundunar jami'an tsaro, duba da yanayin ranks ɗin da ke maƙale a kafaɗar uniform ɗin sa, da kuma haɗuwa da tsaruwar office ɗin na sa.

Ya ƙame tare da sarawa mai office ɗin, ya yi masa alama da ya zauna.

Ya zauna tare da sake gaida wanda ya tarar a office É—in, da uniform É—in sa ke É—auke da sunan ACP Solomon wada.

ACP wada ya kalli matashin ya yi murmushi ya ce "CSP Nasir Yusuf"

Nasir ya waro ido ya ce "Wane ni Yallaɓai, Dsp ɗin dai"

"Au Csp É—in ne ba ka so? Ba abun mamaki ba ne ba, ka ji gobe kai ne Cp na garin nan, kai koma IG gaba É—aya"

Nasir yayi murmushi yana sunkuyar da kai.
Chapter 4 · 0% Book details