← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 32

Sashe 23

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayi wani irin ihu, ya jinjina kai ya ce "Madaki nake, gumbar dutse, na san ko bamu yi gaba da gaba da kai ba, ka san labarina, ina son wannan ya zama gargaɗina da kai na farko na ƙarshe, babu kai babu shiga harkata da yarana, idan ba haka ba" Nasir ya tsare shi da ido, ban da lalacewa ace ɗan ta'adda ne zai shigo har office yana yi wa jami'in tsaro kashedi, saboda wasu masu faɗa a ji sun tsaya masa.

Yayi murmushi mai ciwo ya ce sergent Iliya, ka fito da yaran nan gaba É—ayansu"

Ya amsa masa da "Ok sir"

Nasir ya zagaya, ya kama gefen rigar madaki, suka fita waje, ya kalle shi ya ce "Wanene Aminu? Ina zan same shi?"

Madaki ya ce "Wane Aminun?"

"Viper, na san ka san shi, tun da an ce abokin rigimarka ne"

Madaki ya buɗe wawaken bakinsa, da wiwi duk ta dafar da haƙoran, laɓaɓansa sun zama manya, sun yi baƙi saboda taba, ya kwashe da dariya ya ce "Tabbas! Na san shi, ɗan zaki ne, da na yi sake ya girma yake neman gagarar kundila, dan da na kashe shi tun a wancan shekarun da haka ba ta faru ba. Nima neman sa nake yi ruwa a jallo, ko a raye ko a mace, dan haka idan ka same shi, ka sadani da shi.
Sai dai ka bi a hankali wurin neman sa, jami'anku su suka masa sunan Viper, kumurci ne mai hatsari da idan ya sareka zai kashe ka"

A dai-dai lokacin matasan suka fito harabar station É—in suna ihu, suna sarawa madaki, wasu daga cikinsu kuma da ba yaran madaki bane ba suka fice.

Nasir ba ya tunanin tun da ya fara aiki, ya taɓa cin karo da abun da ya ɓata masa rai kamar wannan, sai ya ji gaba ɗaya aikin ya fita daga kansa.

Haka ya ja tawagar matasan suka bar harabar station É—in suna iface-iface.

Duk yadda Nabila ta so ta samu damar guduwa, daga wurin aiki yau, ta kasa samun dama, dan haka ba ta tashi ba sai ƙarfe uku, a lokacin ba ta da wani kuzarin kirki, babu abun da take buƙata wanda ya wuce ta tafi gida.

Ba ta fi mintuna ashirin da shiga gida ba, Nasir ya dawo.

Bayan sallar la'asar ya kirata a waya, ya ce ta fito yana son ganinta.

Ba ta É—auki lokaci ba, ta fita harabar gidan, wajen parking space akwai fararen kujeru.

A can ta tarar da shi, sai dai yanayinsa ya tabbatar mata akwai damuwa "DSP, yana ga kamar ranka a ɓace ne?" Tayi maganar tana zama.

"Damuwa kam akwaita, gagaruma kuwa arfa"

Ta girgiza kai ta ce "Subhanallah, meyafaru yayana?"

Nasir ya ce "An saki yaran nan fa, da muka kama shekaranjiya"

Ta waro ido ta ce "Saboda me?"

Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce "Saboda yaran ƴan siyasa ne, ina zuwa office aka kira ni daga sama, wai suma umarni aka yi musu, kar in sake kama yaran, aikin neman Aminu aka saka ni ba wannan ba, na daɗe ba ayi mini abun da ya ɓata mini rai irin wannan ba, kamar ni wai ni ɗan daba ya kalleni a cikin kakina, yake yi mini kashedi a office could you imagine. Sai an yi magana ace ba ma taɓuka komai, an janye jami'an tsaron da aka ajiye a unguwar ma"

Nabila ta daki tebur tana huci, zuciyarta har wani tafasa take yi ta ce. "Shikenan, da wanda suka kashe, da kwanciyar hankalin mutanen unguwar, duk ba matsalar su ba ce ba? Personal interest É—in su ne kawai a gabansu?"

"Gashi kuwa kina gani, yanzu idan na matsa zasu iya raba ni da state É—in nan ma gaba É—aya, ni kuma bana son barin garin nan saboda, i don't want to miss you dear"

Kamar za ta yi kuka ta ce "Wallahi Yaya gaba ɗaya aiki ya fita daga kaina, anya ba haƙura zan yi na kama kasuwanci ba, kai babu daɗi, sumayya ma haka, nima dan jan wuya ce, idan aka addaba mini ajiye aikin zan yi, gaba ɗaya ayyukanmu na taimako ne, amma ɓata gari sun yi kane-kane a ciki. Yanzu menene abun yi?"

Nasir ya ce "Abun yi kawai na mayar da hankali, na yi musu abun da suka ce, shi kansa wanda suke son a kama É—in, ina zargin wani abu ne akansa, ko tsakaninsa da wani ya sanya suke son in kama shi, ban da baka ya za ayi ace É—an daba ya gagara kamuwa, alhalin yana cikin garin nan"

Ta ce "To ka ce ba zaka yi ba mana, idan sun matsu su manyan su kama shi mana"

Yayi dariya cikin takaici ya ce "Ba zai yiwu ba arfa"

Ta kwantar da murya ta ce "Ka kwantar da hankalinka yaya, komai lokaci ne, sai dai duk ranar da Allah ya sa muka kai wani matsayi, mu yi iya yinmu, wurin ganin ana tsage gaskiya duk ɗacinta, lokaci ne ka yi haƙuri"

Yayi murmushi ya ce "Idan ban yi haƙuri ba, ya zan yi, dolena ai, na san lokaci ne

Ta ce "Yauwwa, in sha Allah, da ni da kai da sumy, zamu yi nasara a rayuwar aiki, and zan yi duk iya yi na, na ga ka kama aminu"

Nasir yayi murmushi ya ce "How? Na yi amfani da techniques É—ina, na kama masu laifi, amma na kasa samunsa, akwai alamun shi ma yana da masu tsaya masa"

"Mu ma Allah ya tsaya mana, zamu yi yaƙi da duk wani mai kawo cikas ga aiki da adalci"

Dariya ta bawa Nasir ya ce "Ka ga ƴan ƙasa nagari" suka yi dariya gaba ɗaya.

***
Sanye yake da gajeren wando, da riga armless baƙa, joint ne mai kyau sosai da sosai, yanayin matasan da suke shiga suna fita, zai tabattar da na masu hannu da shuni ne.

Ya ɗora ƙafarsa a kan kujera, yana ta shan shisha, kusa da shi wasu matasan ne, suma suna ta nasu shaye-shayen.

Sai matashi É—aya da yake kujerar da take facing É—in sa, yana shan sigari, ya kalli Abdul ya ce "Kai Abdul, wai wannan lumshe idon da ka ke yi, lafiya kuwa?"

Ya sauke ƙafafuwan sa, ya tashi ya gyara zamansa ya yi wani murmushi ya ce "Ba lafiya ba" yayi maganar yana murmushi.

"Ba lafiya ba kuma ka ke dariya?"

Ya girgiza kai cike da shauƙi ya ce "Na rasa ya zan yi ne, tun ranar da na samu wata cika, under 18, na sarara na kasa mantawa da ita, duk matan da nake harkata da su, na kasa samun abun da nake so, kamar yadda na samu a wurinta. Ashe duk wahalar banza nake yi da nake biyewa manyan yaran nan"

Saif ya ce "To ka koma mata mana"

Abdul ya ce "I rape her" yayi maganar yana sake sakin hayaƙi a iska.

"Rape kuma? How?"

Abdul ya ce "I don't know, i was drunk, bai gama sakina ba kuma, na je gidan aunt maijidda, na tarar da yarinyar ashe ba ta gari ita da mijinta, duk yadda nake da ƙyanƙyami, nake son manyan mata, amma na kwaɗaitu da yarinyar nan, tun a ranar farko da na fara ganinta.
I don't know why, but i still need her, na kasa samun yadda nake so, ita É—in dai nake son sake kasancewa da ita.
Warin da jikinta yake yi, make me more crazy on her, she was the first under 18 virgin i mate, i don't think...

Saif ya katse shi ta hanyar cewa "Anya kana hayyacinka kuwa? Ko ka sha wani abun ne bai sake ka ba, ka ke yi mana surutun banza, ka yi raping É—in under 18 old girl, kana vewa warin jikinta make you more crazy are you well?"

Abdul ya gyara zamansa ya ce "Saif da gaske nake, i rape her, dad is even working on it, mamanta wai har sun shiga media sun kai ƙara. I don't care what so ever, i still need her, at any cost".

"Abdul, ka ce dad ɗinka yana ƙoƙarin a rufe case ɗin, amma kana wannan zancen, ka san idan magana ta shiga media sai a hankali, da kai da dad ɗin abokan hamayya za su saka ku gaba".

"Abu nawa na yi babu wanda ya fashe? I don't care, you will help me in nemo yarinyar nan, na ji dad ya ce naja ta shiga case É—in, kuma ba wata ba ce ba, she's just maid da gani ka san yar talakawa ce"

Cikin tsoro, Saif ya waro ido ya ce "Wannan barrister? Aikuwa ka kaÉ—e Abdul, an ya zaka sha wannan karon?"

Abdul ya kwashe da dariya, har sai da ya janyo hankalin wasu kansu ya ce "You don't get sense, malam zaka taimake ni na sake nemo yarinyar nan, itakaɗai ce maganin ƙishirwata" yayi maganar yana cigaba da ƙyaƙyata dariya.

***
Abun da Nasir ya gaya wa Nabila, ya ƙara azalzalar ta, akan son samun Viper, ta tabbatar da kama Viper zai iya zama silar cigabansa da ɗaukakar da take nema.
Sai dai ta kawar da tunanin daga zuciyarta, a lokacin da ta nutsa, tana kallon hotunan Barrister Naja'atu a social media. Ayyukanta na jin ƙai, da makamantansu.
Babu wani information da zai gaya mata haƙiƙanin wacece Naja'atu Bunkure, amma ta barwa zuciyarta lallai akwai wani abu a ƙasa a kan ta, kuma zata tono shi.

Ranar talata da safe tana shirin fita aiki, sumayya ta kirata ta ce su haÉ—u, a in da suke saba haÉ—uwa, su tafi tare.

Tun da Nabila ta ji haka, ta san akwai wani abu a ƙasa, dan haka ta amsa mata da to.

***
Walid ne yake ta yi wa Al'amin lissafi, da bayanin ayyukan da ya saka ayi masa, amma sam hankalinsa baya kan abun da walid É—in yake faÉ—a.

"Viper" walid ya kira shi.

Maimakon ya amsa sai ya ce "Haryanzu babu wani labari a kan masu zuwa gidan malam lawan?"

Walid ya numfasa ya ce "Babu"

Ya ce "Yaran nan gaba É—aya aka sake su, tare da yaran madaki ko?"

"Eh, É—azu duk suka fita, an sake su duka".
Chapter 23 · 0% Book details