Sashe 12
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin tsuma ya ce "Tuba nake oga, suɓutar baki ce, ban san waye ya fito da ni ba, kawai cewa aka yi na tafi"
Ya É—an yi shiru sannan ya ce "Kuma ka tabattar da ka gaya musu sunana, cewar ni ne me kayan?"
"Wallahi na faÉ—a musu"
Ya jinjina kai ya ce "Shikenan"
Ya ɗaga rigarsa ya zaro wata sharɓeɓiyar wuƙa, ya danƙa masa ya ce "Maza ka fasa cikin gari, unguwarmu, su walid sun tafi yaran Madaki zaku farwa babu sani babu sabo, idan an yi ram da wani daga cikin ku, ku ambaci sunana, ku ce ni ne jagoran aika-aikar, amma ku kiyaye ƙa'idar aikina"
Ɗan mama ya risuna ya ce "Umarninka ne abun biyayya a gare ni, an gama za ayi yadda ka ce" ya soke wuƙar ya juya, ya tafi da sauri yana haɗa hanya..
Cikin ƙaramin gidan ya shiga, ya nufi ɗakin kwanansa, ya kunna fitilar wayarsa, ya kunna ƙwan solar, haske ya gauraye ɗakin.
Ya saka mukulli ya rufe ɗakin, sannan ya zauna yayi shiru tsawon mintuna, daga bisani kuma ya ɗaukko wiwi ya naɗa ta, ya kunna ya fara zuƙa.
Madadin ya ji ƙunci, da zafin da zuciyarsa ke yi masa, yana raguwa, sai ma wani irin baƙin ciki da matsananciyar damuwa da suka kawo masa ziyara.
Wani abu mai tsananin ɗaci yake ƙoƙarin haɗiyewa, amma abu ya gagara.
Ya ɗaga wiwin yana kallonta cike da baƙin ciki da takaici, yayi watsi da ita yana sauke numfashi.
Kamar mahaukaci ya zabura ya buÉ—e wata akwati, ya É—aukko kwalaben allura, ya farfasa ya haÉ—a, ya yi wa kansa, ya nemi wuri ya kwanta.
Bai fi mintuna goma ba, kansa ya fara barazanar tsagewa, ya fara kakari yana rirriƙe kansa.
Duk yadda ya kai ga ƙara yawan doses ɗin abun da yake sha, ba sa ɗaukarsa, su mantar da shi damuwarsa, sai dai su wahalar da shi, shi a yanzu babban fatansa ya samu abun da zai yi amfani da shi, da zai goge masa komai na ƙwaƙwalwarsa ya yi bacci mai nisan gaske.
***
Nabila ce tsaye a kitchen tana ta ciye-ciye, tana yi wa magajiya surutu.
Baba magajiya ta ce "Dan Allah Arfa ki yi mini shiru na ji radiyona, wai ni ya aka yi, ki ka tashi da sassafen nan ma"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Baba magajiya kin gane mai muryar nan kuwa?"
Baba magajiya ta yi dariya ta ce "Sumayya ce mana"
"Ashe za ki gane ta"
"Ka ji Æ´a, yau na sanku da ke da ita, da zan kasa gane muryarta"
"Ai in gaya miki baba magajiya, wata mata ce ta takura wa aminiyata, a wurin aiki, da iskanci kala-kala ga sumayya da son aiki, amma matar nan tayi ta taÉ—iyeta, ni kuwa na ce ta daina saurara mata wallahi,shi ne ma fa ake ba ta karanta rahotanni wasu lokutan, da experience É—in ta da komai, wata sokuwa ta cuceta, ta hana ta cigaba"
Baba magajiya ta ce "Ohh Arfa, ai mahaƙurci mawadaci, yawan faɗa ba shi da amfani"
Nabila ta ce "A'a fa baba magajiya, ni ma ba faɗa ne da ni ba, wulaƙanci ne ba na so, duk wanda ya wulaƙanta ni, sai mun yi fito na fito da shi".
Baba magajiya ta ce "A dai din ga haƙuri, tun da.... ba ta gama magana ba, Nabila ta yi wani irin tsalle ta ɗauki radiyon, tayi waje da gudu.
Sashin mama ta faÉ—a, dan ta san tun da Nasir yana gari, lallai zai shiga sashen ta ya karya kafin ya fita.
Aikuwa a sashen ta tarar da shi, yana karyawa, su na hira da mama, da kuma sauda.
Ƙaro volume ɗin radiyon tayi, ta na yi masa nuni da ya saurara.
Rahoto ne a kan rikicin faɗan daba, da ya gudana a cikin ɗaya daga manyan unguwannin kano, wanda tun goma na dare ake rikicin, har ƙarfe sha biyu ana rigimar, ƴan sandan sun yi nasarar cafke wasu daga cikin matasan, in da ɗaya daga wanda aka kama, ya ce Aminu Viper ne ya aka su
Sai da suka kammala ji, Nabila cikin rawar jiki ta ce "Yaya Nasir, ba wannan ne wanda ka ke nema ba?"
Ya jinjina mata kai ya ce "Shi ne"
"Ka yi sauri ka tashi, ka je division É—in da aka tsare Æ´an daban, a baka su ka zurafafa bincike, gidan radiyon su sumayya ne, sai na biya can na sake samo rahoto".
"Ke!" Mama ta daka mata tsawa, har sai da ta É—an razana.
"Tashi ki bani wuri, yaya ina magana da shi, ba sallama ba gaisuwa babu neman izini, kawai ki zauna ki na surutun banza" Nabila ta yi shiru ba ta ce komai ba.
Sauda ta ce "Dama mama yaushe za ta gaishe ki, tana abu kamar mahaukaciya"
Ta kalle su, ta kalli Nasir da yake wurin, ta haÉ—iye wani abu ta tashi, za ta fita.
Nasir ya riƙo hannun ta ya tashi ya tsaya, ya ce "Sorry barrister, na gode sosai da wannan gudunmawa, zan je division ɗin, ki samo mini bayani a wurin sumayyan".
Ya kalli mama ya ce "Haba mama, kin san tana gaishe ki, tsananin zumuÉ—in ta kawo mini labari ne fa ya sa ta manta, thank you Arfa ki shirya ki tafi aiki kar ki makara"
A ƙule mama ta ce "Wai kai har abada ba zaka yi hankali ba, dan ubanka ya zauna yana cewa in ja maka kunne, a kan shishshigin da ka ke yi mata, amma ina magana kana dizagani a gabanta" Nabila ta yi gaba ta fice a fusace, dan idan ta cigaba da tsayuwa, za ta iya aikata abun da zai hana kowa wuni cikin farin ciki.
Ya ce "Ni É—in kuma mama?"
"Kai É—in fa, ko ka shiga hankalinka, ko kuma duk abun da ya biyo baya kai ka so".
Sam sai ya ji maganar kamar maman ce, ta shirya kayarta dan ta saba, dan haka ya yi musu sallama ya fice.
A gurguje ta tsaya ta gaisa da Abba, ta fice cikin zumuÉ—i, gidan radiyon su sumayya ta fara tsayawa.
Sumayya ta yi mamakin ganinta, ta ce "Hajiya lafiya ki ka zo mana wurin aiki da sassafe? Talla ki ka kawo ko cigaya?"
"Ƙaniyarki na kawo" Nabila ta ba ta amsa.
Sumayya ta ce "Ai na san ke ungulu ce, ba kya jewar banza, ya aka yi uwar makara"
Nabila ta ce "Yau da safe kan na fito, na ji baba magajiya na jin program ɗin ku na labaran ƙarfe shida, bayan kin karanto naki, na ji wani rahoto na faɗan ƴan daba, jiya a kano"
Sumayya ta ce "Eh meyafaru?"
"Kin je wurin ne?"
Sumayya ta zaro ido ta ce "In je in yi me?"
"Na ji an ce wai yaran Aminu Viper ne"
Sumayya ta ce "Eh to, ni ma haka na ji"
"Dan Allah ki tashi mu je asibiti, an ce an kama wasu, wasu kuma da aka yi musu miyagun raunuka suna asibitin koyarwa na cikin gari"
Sumayya ta ce "To wai ke duk menene haÉ—inki da hakan?"
Kamar Nabila za ta yi kuka ta ce "Sumy ban gaya miki ba? Yaya Nasir ne incharge É—in bincike a kan mutumin nan, kusan kullum sai an faÉ—i mugun aikinsa, ya tabattar mini da in dai na gano masa in da yake, ko na taimakasa ya gano zan yi suna sosai"
Cikin matsanancin takaici Sumayya ta ce "Tashi ki tafi ko na ɗura miki ashar, ƴar wahala, shi yaya Nasir ɗin ne ya gaya miki haka? Ƴar sanda ce ke? Su ma ya suka ƙarke da su balle ke ki na mace, wallahi ba zan kai kaina ga halaka ba"
"Sumy ki gane, this can all help our career ki zo mu je mana"
"Wallahi ba zan shiga shirgin ƴan daba su kashe ni ba, idan kin yi sunan uban me zai ƙara miki, za a binneki da shaharar ne idan kin mutu?"
Cikin ƙoƙarin son fahimtar da sumayya ta ce "Ba za a binne ni da shahara ba, amma atleast zan samu chances da zan iya fuskantar Naja bunkure"
Wata uwar ashar sumayya ta yi wa Nabila, ta tashi ta ce "Mahaukaciya, ai sai ki yi, ke da bunkuren Æ´an wahala"
Nabila ta tashi a fusace, ta É—auki jakarta ba tare da ta sake cewa sumayya komai ba, ta tashi.
Sumayya ta girgiza kai ta ce "Arfa Allah ya taro ki ya shirye ki, ya yaye miki baƙin taurin kai"
"Tun da kin ce ba zaki je ba, kar ki sake yi mini magana, kuma na gode"
"Eh ba zani ba, haka kurum a kashe ni a banza, mutanen da ba tsoron Allah ne da su ba, mutanen da suke shan ƙwaya tana gaya musu gaibu, su ɓantarani biyu a banza ba da ni ba"
Nabila ta yi mata shiru ta fice.
Nabila ba ta yi tunanin komai ba, ta garzaya asibitin koyarwa, na cikin gari.
Ba ta wani sha wahala ba, saboda tana zuwa, ta tarar jami'an tsaro sun kewaye sashen emergency, ba wanda yake shiga ko ya fita.
Zagaye harabar wurin ta fara yi,tana neman hanyar shiga, da son tabattar da abun da yake faruwa a wurin, ta samu wata cleaner, ko meyafaru a in da Æ´an sandan suke.
Nan ta sanar mata da cewa, yaran da aka illata a wurin faÉ—an daba a daren jiya, aka kawo an hana kowa shiga ko fita.
Nabila ta yi mata godiya, ta yi mata alheri, ta nufi wurin da aka hana shigar da fita..
Ta ƙarasa ta samu ɗaya daga cikin jami'an tsaro suka gaisa, sannan ta nemi shiga, suka ce ba za ta shiga ba.
ID card ta nuna musu, amma É—aya daga cikin su ya ce "Madam nan ba prison bane, kuma ba police station ba ne ba, nan Asibiti ne, ki bari idan aka kai su can, sai ki je ki yi aikin ki".
Ta kwantar da murya ta ce "Dan Allah yallaɓai, ku bar ni na shiga, Ma'aikaciya ce nima"
"Get out from here" yayi mata tsawa.
Aikuwa ta hasala ta ce "A beg, don't shout at me, aikinka ka ke yi, nima nawa nake son yi, a kan me za ka yi mini tsawa?" Hankalin mutane ya fara dawowa wurin.