← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 32

Sashe 32

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Nabila ta kaɗa kai ta ce "Kusan watana guda zuwa na biyu ma,  kawai ina fafutukar yaya zan ganshi, na san dama zaki ƙaryata ni, ban gaya miki ba ma balle ki hana ni ko ki yi mini masifa. Amma cikin ikon Allah, viper ya bar mini shaidar da zai tabattar da  ya ganni"

Cikin rashin fahimta, sumayya ta ce "Kamar yaya?"

Nabila ta É—aga rigarta, sai ga plasta a gefen cikinta, ta saka hannu ta cire plastan, sai ga rauni a wurin.

Sumayya ta waro ido, tare da rufe baki, ta ce "Na shiga uku, Nabila kin haukace ne? Wai dama da gaske ki ke?"

Ta saki rigar ta ce "Ai kafin yayi mini haka, rannan karnuka sun kusa yin watanda ta. Sunayya gayen nan ya wuce duk yadda nake tunani, ashe faɗar sunansa ne a baki kawai mai sauƙi, wallahi idanunsa sun kusa sakani fitsari a wando, sumayya yaya zan kwatanta miki yadda yake ne ki gane abun da na gani? Kwarjininsa ya wuce duk yadda zan kwatanta miki, wallahi da ya shaƙe ni, na ɗauka mutuwa na yi"

"Har shaƙe ki yayi, kin ga Nabila ki rufa mana asiri, amma yaya aka yi ki ka samu in da yake?"

"Na gaya miki kusan watanni biyu kenan ina nemansa, na san idan na gaya miki, hana ni zaki yi, duk ba wannan ne ya dame ni ba, yayi alwashin idan ya sake ganin fuskata, sai ya kashe ni, kuma mummunar kasada na kuma tafkawa Sumayya".

"Ta me kuma?!

"Wayarsa na sato, kan na taho!".

Alhamdilillah, duka duka a nan mu ka kawo ƙarshen free pages, mu kasance a cikin paid pages, domin jin ainihin gundarin labarin *ƘARFE A WUTA*.

₦500 ne kacal ta wannan account ɗin, masu so ta private special group 1k zasu saka a wannan account ɗin.
0009450228
Aisha Adam jaiz bank

Ayshercool.
08081012143
Chapter 32 · 0% Book details