Sashe 18
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko sumayya ma ba ta gaya wa ba, tayi shiru da bakinta, sai dai faÉ—uwar da tayi, duk ta goge gwiwa.
Haka kurum tausayi, da tunanin makomar rayuwar matasan da ta gani, a harkar daba da shaye-shayen nan, ya dami zuciyarta ta rasa abun da yake yi mata daɗi, tana matuƙar son sanin me suke ji a cikin kayan shaye-shaye? Tabbas da ita wata ce, sai ta taimakawa rayuwar su, ko a mutum goma, idan biyu suka shiryu ai an rage.
Kamar wadda ta sha kayan maye, haka yau tayi bacci da wuri, gudun da tayi jikinta duk ciwo yake yi mata, ga numfashi sai wahala yake ba ta.
A wani ɗaki ta ganta, mai duhu sai haske kaɗan a ciki, ga karnuka duk a cikin ɗakin, sai haushi suke yi mata, an ɗaure su da sarƙa.
Ihu take yi tana neman agaji, amma babu wanda ya san tana yi.
Can sai ga wani mutum ya shigo, dogo sosai, mai cikar halitta, ba ta ganin fuskarsa saboda duhu, ya shigo ɗakin bai ce mata uffan ba, ya danƙo hannunta ya biyo tsakanin karnukan ya fito da ita daga ɗakin, ya ciro wuƙa zai caka mata a ciki.
Wani uban ihu ta saki, tana kiran sunan Allah, da na Abba da Nasir.
Tana buÉ—e ido, ta ga Abba a kanta, da Nasir, da su walida har da Anty da baba magajiya, ana ta tofa mata addu'a.
Kallonsu take yi É—aya bayan É—aya, ta ce "Abba ya na ganku a nan? Meyafaru?"
Nasir ya ce "Sannu"
Abba ya ce "Arfa ba kya addu'a ko?"
Ta girgiza kai ta ce "Ina yi Abba"
"A'a ba kya yi, da kina addu'a babu yadda za ayi, ki kwanta kina yi mana ihu da safiyar nan, shiyasa nake hanaki wannan shegen fentin da bulbula turare a jikinki, dole sheÉ—anu su yi ayari, su yi ta binki"
Nasir ya ce "Dan Abba ka yi haƙuri, haryanzu a tsorace take ma, a bari ta dawo hayyacinta gaba ɗaya, sannu Arfat, ki ɗauro alwala ki zo ki ɗauki Alqur'ani ki karanta".
Abba ya miƙe ya ce "Aishikenan, zan yi waya da Barrister, su baki day off, ki samu ki huta"
Nabila ta yi shiru tana rarraba ido, ta san lafiyarta ƙalau, tsabar tsorata ne da tayi.
Tayi shiru ba ta faÉ—i abun da ya faru ba, suka din ga yi mata sannu.
***
YALOKO ƘARAMAR HUKUMAR UNGOGGO
Matashiyar yarinya ce, wadda dudu shekarunta ba su fi goma sha huɗu ba, take ta iza wuta a cikin murhu, gefe ga garin tuwo a cikin ƙwarya.
Yaro ne ya yi sallama, ta É—aga kai ta amsa masa.
Ya kalleta ya ce "Ramma ki zo ana sallama"
Ta É—an waro manyan idanunta ta ce "In ji wa? Ko Habu ne?"
"A'a, wani ne da mota"
Ta miƙe tsaye ta ce "To mota kuma, ina zuwa?"
Daga tsakar gidan ta É—an É—aga murya ta ce "Mama, wai ana nemana a waje, bari na duba waye, ruwan ya kusa tafasa"
Daga cikin É—aki matar ta amsa mata da "To ramma, hanzarta ki dawo, ina son zan fita ne"
Ramma ta amsa da "to" ta É—auki hijjabinta ta saka ta fice waje.
Mintuna goma sha biyu ta dawo, jiki a sanyaye.
Mamanta ta kalleta ta ce "Menene?"
"Mama daga Kano ne, wai Anty mai jidda ce gidan da nake aiki, ta yi waya wai azo a É—auke ni a mayar da ni, a satin nan za su dawo"
Matar tayi sak ta ce "Da wuri haka, ba cewa aka yi sai bayan wata guda zaki koma ba?"
Ramma ta ja ta tsaya ta ce "Jikina duk yayi sanyi, wai yanzu-yanzu zamu tafi"
"To shikenan ai babu wani abu, ki yi haƙuri kin ji ramma, ni kaina ba a son raina ki ke barin gabana ba, da Allah ya sa mun tara kuɗin kayan gado, shikenan sai ki dawo ki yi auren ki. Maza mu je na tayaki haɗa kayan"
Cikin abun da bai fi mintuna arba'in ba, suka haÉ—a kayan, suka yi sallama ramma ta bi direba zuwa gidan aikinta da yake Kano.
Yana zaune ya zuba musu ido, suna haɗa masa tea, Walid ya zuba ƙwayoyi a cikin kofin, sannan ya zuba shayin.
"Ƙara wannan ba zasu ɗauke ni ba"
Walid ya ce "Amma boss, kai fa ka ke hanamu sha a baya, tayi yawa wallahi".
"Ka ƙara mini na ce" yayi maganar a hasale.
Ya ƙara masa ƙwayoyin yana kallonsa, saboda ƙwayar da suke yi wa laƙabi da raina kama, a baya sam baya shan irinta, saboda yadda take bugarwa, wasu lokutan rabi suke ɓallawa su sha, amma ya ce a saka masa kusan biyar yanzu.
Ya ɗauki kofin ya kai bakinsa zai fara sha, Walid ya ce "Yau fa madaki za su je ɗaukar fansa cikin unguwa, daga majiya mai ƙarfi na ji zancen, daga jiya zuwa yau ya ce idan ɗan arearmu ya shiga ta su, a aika shi kawai"
Ya cigaba da girgiza kofin ba tare da ya yi magana ba, ya sake yinƙunrin kai kofin bakinsa, walid ya sake cewa "Wata ta je nemanka a arear, aka kaita dabar madaki, Allah ne ya yi da kwananta a gaba, da kasheta za su yi"
Duk da cikinsa yayi wata ƙara, jin an ce mace ta na nemansa. Wace mai tsautsayin ce wannan? Me take nema a wurina?, amma ya maze ya ɗago jajayen idanunsa ya kalli walid ya ce "Ni kuma?"
Walid ya ce "Ba zan yi maka ƙarya ba, da gaske nake"
Wani dogon tsaki ya ja, ya dungurar da kofin shayin, ya tashi ya ce "Ku ɗebo yaran nan na cikin unguwa, da na can wajen gari, ku sake dira a dabar madaki, ina son ɓarnar da za ku yi ta fi waccan, kar ku basu damar cutar da kowa. Ko kun gaya wa jami'an tsaro ƙudurinsu, babu abun da za su yi musu, ku far musu kawai, ka shirya komai, a bawa yaran na shan sigari" bai jira amsar walid ba ya fice.
Walid ya yi ajiyar zuciya, ɗan mama ya kalle shi ya ce "Da gaske ka ke wata ta je nemansa, ko kuma ka faɗa ne, dan ka hana shi shan ƙwayar nan?"
Walid ya ce "Duka, kai da ya sha abun nan, zai iya mutuwa fa"
Ɗan mama ya ce "Ai rigimar da yake yi kwanan nan, ta ƙara yawa, sai an ƙara saka masa ido sosai, kashe kansa yake son yi wallahi, wasu lokutan bana son muke watsewa mu bar shi shikaɗai a gidan nan".
Walid ya girgiza kai ya ce "Ba zai kashe kansa ba".
"Ya aka yi ka san hakan?"
"Yana da abun da yake son cimma, kawai kayan ne gaba ɗaya ba sa ɗaukarsa gaba ɗaya yanzu, ka san yana cikin matsananciyar damuwa, duk kayan cajin nan kansa ba ya ɗauka kamar aljani, amma ina bincikawa, an yi mini alƙawarin wata zazzafar ƙwaya, daga kudu suke kawota.
Yanzu dai wannan aikin da ya ce , maza-maza ka kira kwangila a waya, ya haɗa mana yara, a basu kayan caji, zamu fasa ƙofa, ai Madaki shi da ɗaukar wata fansa a kanmu, sai dai a lahira idan ana yi. Sai mun ga abun da ya turewa buzu naɗi.
Ɗan mama ya miƙe ya ce "Ok, bari na hanzarta na fara haɗo su ta arear wajen garin nan".
Walid ya ce "Nima fitar zan yi, wurin liti zani, zan shiga karɓar balance". Suka fice gaba ɗaya.
Bayan tafiyar su Aminu ya koma cikin ɗakin, ya fara duba in da walid yake ajiye ƙwayoyi, amma ya dudduba bai gansu ba, ya zazzage ko ina, amma babu.
Wani irin takaici ya tokare masa ƙirji, ya ja dogon tsaki, ya ɗaga gefen katifarsa, allurar sa saura kwalba biyu kawai, kuma ya san ba ɗaukarsa za ta yi ba.
Haka ya zuƙe ta ya yi wa kansa, sai dai kamar kullum, yau ma ƙirjinsa ne ya fara da zafi, kansa yana juya masa.
Wuƙar da take gefensa yake ta kallo, zuciyarsa na raya masa abubuwa daban-daban.
Tun da Ramma ta suka isa cikin kano, gidan da take aikatau, kayanta kawai ta sauke a É—akinta, ta hau aikace-aikace.
Duk da akwai wata mai aikin, wadda ta girmewa ramma, sosai da sosai, amma matar gidan ita ta yarjewa ta shiga sashenta, har uwar ɗaka da na maigidan ta gyara mata, a cewarta ramma ta fi nutsuwa, kuma ba ta taɓa ƴar aikin da ba ta yi mata sata ba, sai ita.
Matar gidan da Æ´aÆ´anta gaba É—aya sun tafi dubai hutu, shiyasa ta sallame ta, ta ce ta je gida ta huta, za su yi wata biyu kafin su dawo, kuma kwatsam yanzu sati biyu wai dawowa za su yi.
Tana falon matar gidan, tana ta uban aiki, ɗan kwanakin da aka yi ba a taɓa wurin ba, duk ya yi ƙura.
Ƙofar falon aka shigo, ta tashi da sauri, tana kallon mai shigowar, dan ba ta yi tsammanin ganin kowa a sashen ba, dai-dai wannan lokacin.
***
Nabila kuwa kusan kwanaki uku curr, ta kasa nutsuwa da kwanciyar hankali, da ta kwanta bacci, sai mafarkin karnuka, tayi ta ihu.
Haka Anty da baba magajiya za su danneta, su yi ta shafa mata man gelo da miski, ta ja bakinta, ta yi shiru, ba ta gaya musu abun da ta aikata ba.
Yau kuwa gajiya ta yi da zaman gidan, dan baka cikin hijjabi ta shirya, ta ɗauki ƴar ƙaramar wayarta, ta fito falo.
Umma ta kalleta ta ce "Ke da baki da lafiya, ina zaki je kuma?"
Nabila ta ce "Wurin aiki, akwai buƙatar in je zan kai wani bayani ne mai muhimmanci"
"Amma kin gaya masa, kar ya dawo ya tarar kin fita, ya yi ta faÉ—a"
"Umma ba daÉ—ewa zan yi ba"
Saudat ta ce "Mhmm, a ma faÉ—i gaskiya, ko yawon banza za aje".
Nabila har za ta yi shiru, ta ga idan tayi shiru, za ta cutu, dan haka ta ce "Idan fitsari banza ne, kaza ma tayi, idan yawon ma zan tafi, mai lasisi ne akwai riba, ke ki yi mana"
Umma ta kalli Sauda ta ce "Sauda dan Allah ki din ga jan girmanki, Nabila fa ba sa'arki ba ce ba".
"Na saka da ke ne?"